Ra’ayin A Kan Mamayen Da ‘Yan Awaren Amazon Suka Wa Kauyen Manga A Jihar Taraba

Taraba

Maudu’inmu na wannan makon na filin Ra’ayi Riga, ana dara ga dare ya yi. A yayin da Nijeriya ke kokarin shawo kan matsalar tsaron cikin gida da ta shafi Boko Haram da sace-sacen mutane ana garkuwa da su, sai kuma ga wani sabon kalubale na tsaro, inda ‘yan awaren Ambazoniya na kasar Kamaru suka far wa kauyen Manga a Jihar Taraba. A ganinku me wannan harin yake nufi? Kuma ta yaya ya kamata gwamnati ta bullo wa lamarin? Sai mun ji daga gare ku…

 

Ahmad Yusuf

Innalillahi waa Inna ilaihi raju’un, tabbas wannan wani sabon al’amari ne bayan wanda ake ciki. Kuma Yana da kyau gwamanati tasan ta yadda za ta bullo wa wannan al-amari tun kafin ya yi nisa. Domin kuwa ba fata ake ba,Hakan zai iya zama mafari na wata sabuwar annoba. Ubangiji Allah Ya kara zaunar mana da kasar mu lafiya. Aameen.

 

 

Muhd Basheer Sa’ad

Allahumma ajirni fi masibati wa’aklifini kairan minha! Astagfurullah!

Allah mun tuba!

Ya kamata gwamnati ta kara jajircewa wajen kulawa da al’ummar da take shugabanta.

Kuma muma yakamata mu dage da addu’a saboda wallahi wannan hali da kasar me ke ciki babu abunda take bukata face addu’a.

Allah ya kiyaye mu ya bawa shugabannin mu ikon kulawa da al’umma

 

 

 

Maryam Rabo

Allah mun tuba ka yafe mana ka kawo mana karshen wannan musiba

A gani na kawai mafita shine mu gyara halayen mu mu kuma komawa Allaah

 

 

 

Hassern Mustapha

Wannan ba karamar matsala bace ace ba’a gama da wadannan matsalolin da suke faruwa a cikin gidaba wasu sabbin “Yan ta’adda su sake bullowa daga wata kasa. Maganar gaskiya gwamnati tanada sakaci Akan hakan kuma jami’an tsaro basa aikinsu yadda ya kamata. Idan har zai zamana kasa kamar Nijeriya duk wanda yaga dama zai shigo kuma ta inda yaga dama to tabbas duk wanda yake Nijeriya yana cikin matsala idan har gwamnati da jami’an tsaro za su yi abinda ya dace tabbas babu yadda Za’ayi hakan ya cigaba da faruwa

 

 

 

Ibrahim Hassan Baban Adila

Slm Ibrahim Hassan minister Baban Adila da Ansar Gombe, tabbas kasarmu Nijeriya ta shiga jarrabawa kala kala amma fa musani tun zamanin Obasanjo Nijeriya tana shan fama da kasar Kamaru a kan iyakar kasar mu Nijeriya da Kamaru, tabbas ya zama dole gwamnatin Nijeriya tafarka daga gyangyadin da take yi game da kare hakkin ‘yan kasa a kan tsaro. Sannan ta nuna wa duniya rashin jin dadin abinda ya faru. Wannan kalubale ne ga gwamnatin kasarmu Nijeriya.

 

 

 

 

 

Ibrahim Hassan Baban Adila

Wannan hari da aka kai yankin Taraba ya nuna mana kaf yankin Afirka babu tsaro ,kuma yana nufin hada gwamnatin Nijeriya da Kamaru rashin jituwa tsakaninsu, kuma yakamata karsar Nijeriya ta dauki matakin kare yankinta, wanda ake kira booda a turance, sannan ta kara kaimi kan matsalan tsaro na cikin gida. Shawari daga Ibrahim Hassan minister Baban Adila da Ansar Jihar Gombe.

 

 

 

Zee Waziri

Allah ya kawo mana dauki ya saukaka mana.

 

 

Exit mobile version