Ra’ayin Bai Daya Na Xi Jinping Da Mahaifinsa

“A nemi taimako daga wajen Zhongxun.” Wannan jimla ce da jami’ai da jama’ar yankunan dake arewa maso yammacin kasar Sin su kan fada, hakan ake iya ganin muhimmancin matsayin Xi Zhongxun a cikin zuciyar jama’ar wurin.
Marigayi Xi Zhongxun, mahaifin shugaban kasar Sin a yanzu Xi Jinping, ya dade yana shugabantar ayyukan da suka shafi jam’iyya, siyasa da soja a yankunan dake arewa maso yammacin kasar Sin, tun bayan kafuwar sabuwar kasar.
Xi Zhongxun, wanda ake kiransa “shugaba ne da ya fito daga jama’a” ya kan gayawa iyalinsa cewa, ‘Ni dan manoma ne.” Ya yi ta tsayawa kan amfani da kowace irin dama don mu’amala da jama’a. A idanun manoma, shi ne dan uwa mai kauna, a idanun ma’aikata, shi ne abokansu dake mayar da tsaronsu a gaban kome, a idanun jami’an kananan hukumomi, shi ne sakataren dake mayar da hankali kan moriyar jama’a. Xi Zhongxun ya taba gayawa Xi Jinping cewa, “kowane irin shugaba za ka zama, kada ka manta da bada hidima ga jama’a, ya kamata ka maida hankali kan fararen hula, da kuma yin mu’amala da su.”

Xi Jinping bai taba mantawa da maganar mahaifinsa ba. Yana gudanar da ayyuka ne bisa tushen maida hankali kan moriyar jama’a. Ya yi bincike a dukkan yankuna mafiya fama da talauci a nan kasar Sin, ya dauki niyyar kawar da talauci dake shafar mutane miliyan 40 kafin karshen shekarar 2020, da samar da hidima ga jama’arsa wajen samun ilmi mafi kyau, da ayyukan yi mai karko, da kudin shiga mafi yawa, da muhallin zaman rayuwa mafi kyau da dai sauransu.
Bayan babban taron wakilai karo na 18 na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, Xi Jinping ya zabi lardin Guangdong da aka soma gudanar da manufar yin kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare a matsayin zango na farko wajen yin bincike, da nufin “waiwayen yunkurin yin kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare, da kuma ci gaba da inganta manufar”. A watan Oktoban shekarar 2018 kuma, ya kara yin bincike a Guangdong, inda ya sanarwa duniya cewa, “Kasar Sin ba za ta dakatar da yin kwaskwarima a ciki gida da bude kofa ga kasashen ketare ba”. Daga baya kuma, ya dauki jerin manyan matakai, don ciyar da manufar gaba, wanda ba a taba ganin irinsu ba a da.
‘Ya’yan Xi Zhongxun sun taba cewa, “mahaifinmu ya tsaya kan abubuwan gaskiya, bai taba boye komai ba, musamman ma a batutuwan dake shafar moriyar jama’a bai taba janye jiki ba.” Xi Jinping ya gudanar da ayyuka a karkashin tasirin da mahaifinsa ke kawo masa. Ya jaddada cewa, idan ana fatan fahimtar hakikanin yanayi, dole ne a yi bincike sosai a tsakanin jama’a, ya ce, “dole ne sakatarorin kwamitin jam’iyya na gundumomi su yi bincike a dukkan kauyuka, sakatarorin kwamitin birane su yi bincike kan dukkan garuruwa, sakatarorin kwamitin larduna su yi bincike kan dukkan gundumomi da birane.”

Tun bayan babban taron wakilai karo na 18 na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, Xi Jinping ya kai ziyara a kusan dukkan kasar, ciki har da al’ummomi, kauyuka, kamfanoni, makarantu, rundunonin soja, don fahimtar yanayin da jama’a ke ciki, da kuma ra’ayoyinsu.
Bayan haka, Xi Jinping na da niyyar neman ci gaba ta hanyar kiyaye muhalli a karkashin tasirin da mahaifinsa ya kawo masa. A yanzu haka, kasar Sin na neman bunkasuwa a fannin kiyaye muhallin halittu, ana ta samun kyautatuwar muhalli a kasar.

Exit mobile version