Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Ra’ayin Kasar Sin Zai Taimakawa Aikin Yakar Cutar COVID-19 A Duniya

Published

on

A jiya Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taron koli na kasashen Sin da Afirka dangane da hadin gwiwarsu a kokarin yakar cutar COVID-19, taron da ya gudana ta kafar bidiyo, inda shugaban ya jaddada bukatar karfafa hadin kai tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, da tabbatar da kasancewar bangarori daban daban a duniya, da kokarin zurfafa zumunta dake tsakanin Sin da Afirka, gami da kafa al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya da ta shafi dukkan bangarorin Sin da Afirka. Ma iya cewa kalaman shugaba Xi manuniya ce ga yadda kasar Sin da kasashen Afirka suke kokarin hadin gwiwa da juna don yakar annoba, wanda ya tabbatar da alkiblar da za a bi don zurfafa hadin kai a tsakaninsu, gami da karfafa gwiwar kasashe daban daban a kokarinsu na hadin kai da juna don dakile cutar COVID-19.

Yanzu an shiga lokaci mai muhimmanci a aikin yakar cutar. Saboda a halin yanzu, kasashe da yawa sun fara maido da ayyukan masana’antu da na sana’o’i daban daban, don haka akwai fargabar yiwuwar fuskantar hadarin sake bullar annoba. A sa’i daya, wasu ‘yan siyasar kasashen yammacin duniya suna ta kokarin siyasantar da annobar, da neman alakanta cutar da wata kasa, lamarin da ya haifar da matukar illa ga kokarin kasashe na dakile cutar. To, a bisa wannan yanayi ne, kasar Sin da kasar Afirka ta Kudu, wadda take shugabancin karba-karba na kungiyar tarayyar Afirka AU, gami da Senegal, dake shugabancin dandalin hadin gwiwar kasashen Sin da na Afirka FOCAC, sun yi kira tare don gudanar da wannan taron koli, wanda ya dace da yanayin da ake ciki sosai.
A matsayinsu na aminai kuma kawaye, kasar Sin da kasashen Afirka sun kulla zumunta mai zurfi cikin shekaru fiye da 50 da suka wuce. A nasa bangare, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba gabatar da jerin matakai don karfafa huldar hadin kai tsakanin bangarorin Sin da Afirka, a yayin tarukan koli guda 2 na kasashen Afirka da kasar Sin. Sa’an nan yayin da ake fuskantar hadarin bazuwar annobar, kasar Sin da kasashen Afirka sun ci gaba da nuna wa juna goyon baya, da kokarin yakar cutar kafada da kafada, lamarin da ya kara yaukaka huldar dake tsakanin Sin da Afirka.
A yayin taron da ya gudana a wannan karo, shugaba Xi ya gabatar da jerin shawarwari, da wasu nagartattun matakai, inda ya mai da hankali kan hadin kan Sin da Afirka a fannin dakile cutar, da batun samun ci gaba mai dorewa a nahiyar Afirka, gami da yadda za a taimakawa aikin dakile cutar COVID-19 a duniya. Wadannan shawarwari da matakai sun nuna ra’ayin gwamnatin kasar Sin na ba da muhimmanci ga batutuwan da suka shafi jama’a, da tsaron lafiyarsu, da yadda ake da cikakken sahihanci da gaskiya yayin da Sin take hadin gwiwa da kasashen Afirka.
Wani abun lura shi ne, bangarorin Sin da Afirka sun cimma daidaito kan batutuwa guda 7 a yayin wannan taro, inda kasashen Afirka suka jinjinawa gwamnatin kasar Sin, kan yadda ta dauki matakai masu karfi don hana bazuwar cutar COVID-19 a duniya, da samar da bayanai a kai a kai ga hukumar lafiya ta duniya WHO, da sauran kasashe masu ruwa da tsaki, ba tare da rufa-rufa ba. Ban da haka, kasashen Afirka sun nuna goyon baya ga kasar Sin kan batutuwan da suka shafi yankin Taiwan, da na Hong Kong. A nata bangare, kasar Sin ta nuna goyon baya ga kasashen Afirka kan yadda suke kokarin neman hanyar raya kasashensu, ba tare da tsoma bakin sauran kasashe ba. Wadannan abubuwa sun nuna aminci a fannin siyasa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.
Ko da yake annobar ba ta kai karshenta ba tukuna, amma abubuwan da suka faru sun nuna cewa kasar Sin ita ce aminiya mai gaskiya da kasashen Afirka za su iya dogaro a kanta, a wannan zamanin da muke ciki da duniya ke fama da yanayin rashin tabbas matuka. Kamar yadda shugaba Xi Jinping ya fada, “ a karshe dai ‘yan Adam za su samu nasarar kawar da cutar COVID-19, kana jama’ar kasashen Afirka da ta kasar Sin su ma za su samu damar kyautata zaman rayuwarsu sosai.” (Bello Wang)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: