Ra’ayin Masana Kan Makomar Nijeriya Da Tulin Basussukan Da Ake Bin Ta

Nijeriyar Jiya

Daga Khalid Idris Doya Abuja,

kasar Nijeriya mai dimbin albarkatun kasa na fama da dimbin basukan da suka mata katutu da hakan ke kara jefa ‘yan kasar cikin damuwa da tunanin hanyoyin da kasar za ta bi wajen biyan wadannan basukan da suke jibge.

Kodayake hukumomin kasar sun nuna cewa, suna ciwo basukan ne domin gudanar da ayyukan raya kasa da bunkasa cigaban al’umma, sai dai kuma ‘yan kasar na korafin cewa ayyukan da suke tsammanin gani daga basukan da ake ciyo musu bai kai yadda suke tsammani ba.

Zuwa ranar 30 ga watan June na 2021, basukan da ake bin Nijeriya sun kai dala biliyan 33.468 kamar yadda ofishin kula da basuka na kasar ya fitar.

Kuma duk da hakan Nijeriya tana hankoron sake ciyo wani sabon bashin da ya kai naira tiriliyan 6 domin dafa wa naira tiriliyan 16 da take tsammanin kashewa a shekara mai zuwa.

Bisa basukan waje da ake bin Nijeriya a halin yanzu, kowani dan kasar zai amayar da bashin da ya ci da ya kai dala 157 ko naira 64,684.

Yawan al’ummar Nijeriya zuwa ranar Asabar, 9 ga watan Oktoban 2021, bisa dogara da bayanin majalisar dinkin duniya da ta fitar, ya nuna cewa 212,599,044, tare da kasafta basukan da ake bin kasar da ya nuna cewa kowani dan kasar kama daga babba ko matsakaici, mace ko namiji ana binsa ko ita bashin dala 157 ko naira 64,684 a kan kowani dan kasar.

Basukan da ake bin Nijeriya ya na karuwa sosai a ‘yan lokutan nan, ta yadda basukan suka karu da dala miliyan 120.84 a tsakanin watan Janairu zuwa June na wannan shekarar da muke ciki.

A wani rahoton da Bankin Duniya ya fitar, ya bayyana cewar, Nijeriya tana cikin kasashe guda 10 da suka fi yawan karban basuka a fadin duniya. Domin Nijeriya ta kasance kasa ta 5 a zurfin ciwo basuka domin gudanar da ayyuka.

Bayan Nijeriya sauran kasashen sun hada da Indiya ce kasar da ta fi cin bashi, Bangladesh ta mara mata baya, sai kuma Pakistan ta zo ta uku, bietnam ta 4, Habasha Kenya, Tanzania, Ghana da kuma kasar Uganda.

Wani masani kan harkokin tattalin arziki, Dakta Tayo Bello, ya nuna damuwarsa matuka bisa yawan bashin da ake bin Nijeriya duk kuwa da cewa ayyukan zahiri da za a iya nunawa a ce ga su an yi da kudaden da aka ciyo basu bayyana ga jama’an kasar, ya nuna hakan a matsayin babban abun damuwa ga kasar da al’ummarta.

Dakta Bello na cewa: “Babban matsalar ma shine kudaden da Nijeriya ke fita waje domin ciyo bashinsu bai yi daidai da kudaden shiga da ake samu ba balle a yi tunanin biya a gabar da ya kamata, sannan uwa-uba kuma shi ne, ba a ganin ayyukan da ake yi da kudaden a zahirance da za a su iya tabbatar maka da cewa bashin kasa da aka ciwo ga aikin da aka yi da shi da ‘yan kasar za su gamsu. Gaskiya ana kara dulmiya lamarin cikin dulmiya ne kawai.”

Ya kuma yi zargin cewa, wasu tsirarun mutane na sace kudaden da aka ciwo bashin su da zimmar gudanar da ayyukan raya kasar ba tare da tunanin basukan na yawa ko wani hali kasar za ta shiga a nan gaba ba.

“karin matsala kan basukan waje shi ne za a biya su ne da dala kuma da karin riba ga wadanda suka bada. To, da za a kashe kudaden da aka ciwo wajen gudanar da ayyukan da za su iya dawo da kudaden to ba matsala da hakan, amma babban matsala ne a ciwo bashi a biya albashi da shi,” ya fadi.

Wani dan Nijeriya Mai sharhi kan lamuran yau da kullum, Alhaji Mohammed Sabi’u, ya shaida wa LEADERSHIP HAUSA cewa, “Dukkanin wani mai kishin kasar ban zai damu da yadda ake ciwo basuka a kasar nan. Gaskiyar zance ya kamata hukumomi suke nazarin matakan ciwo bashi domin lafta bashin ba cigaba bane ga kasa. Kuma idan ka duba kudaden da ake ciwo basuka a kansu talaka bai shaidawa ko na ce bai ganinsu a zahirance.

“Gwamnati Mai ci tana kokarin yaki da rashawa kamar yadda take ikirari, in haka ne, akwai bukatar ta waiwayi basukan da ta ciwo tun lokacin hawanta mulki zuwa yanzu ta duba irin ayyukan da aka yi da su da yadda aka kashe kafin fara tunanin sake lafto wasu bashin.

“Fatanmu dai shine a ke duba tattalin arziki na kasa da kudaden shiga da kuma bukatun da suke kasa kafin aiwatar da kowa.”

Mafi yawan basukan da ake ciwo basukansu daga IDA reshen babban bankin duniya. Bashin da IDA ke bin Nijeriya ya kai dala biliyan 11.62, sannan kuma tana da wani bashin dala biliyan 10.37 daga Eurobond.

Sannan kuma ana binta dala biliyan 3.5 daga International Monetary Fund da kuma wani dala biliyan 3.5 daga EdIM bank na China.

Babban bankin duniya ya ce kasashen da suka fi yawan ciyo bashin nan suna fuskantar hatsari sosai na rashin gamsuwa daga masu basu lamarin cin bashin ko amince musu. Kuma hakan na barazaka ga cigaban tattalin arzikin kasashen lura da irin yarjejeniyar da ake cimmawa a tsakani wajen badawa ko sharadin biya.

Dukkanin wannan kurar kan yawan bashin da ake bin Nijeriya ya taso ne a daidai lokacin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta ayyana neman bashin naira tiriliyan 6.26 domin cike gibin kasafin 2022.

Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Zainab Ahmad, ta bayyana cewar a kasafin 2022 din za a dauki kaso 22% cikin dari ne wajen sayo kayan tsaro, naira triliyan 3.61 wajen biyan basussukan da aka ci a baya, sannan a yi amfani da naira triliyan 4.11 wajen biyan albashin ma’aikata, su kuma ‘yan fansho an ware masu naira biliyan 579.

Lamarin ya dauki hankalin ‘yan Nijeriya ciki kuwa har da majalisar kasa, kodayake shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya bayyana cewar majalisar za ta yi bita a tsanake ga kasafin domin duba ababen da za ta rage domin rage yawan wasu kudade da za su samu shiga lalitar gwamnati wajen toshe gibin.

Shi kuma a ra’ayinsa, Sanata Abdullahi Adamu, ya nuna gamsuwarsa kan wannan ciwo bashin, yana mai cewa ba kasar nan kadai ce ke cin bashi domin gudanar da ayyuka ba. Ya buga misali da Birtaniya da ya ce yanzu haka ana bin ta bashin fam triliyan 3.

A lokacin da yake na shi nazarin, Sanata Barau Jibrin wanda yake shugabantan kwamitin kula da kasafin kudi a Majalisar Dattawa, ya yaba ne da irin ayyukan more rayuwa da za a yi da kasafin inda ya ce za a kyautata sashin tattalin arzikin Nijeriya ne saboda masu kananan sana’o’i su samu ayyukan yi.

Honarabul Abubakar Yunus, dan majalisar wakilai ne na tarayya, ya ce “Muna son wannan ya kasance ya inganta tsarin yadda ake tafiyar da ayyukan gwamnati musamman ma abin da zai kawo wa kasa dogaro da kai, da kuma inganta kalubale na wajen samun kuɗaɗen shiga.

“Abin da ya burge mu shi ne akwai wadansu abubuwa da aka yi la’akari da su wadanda gaskiya idan aka yi za su ta da wasu kura-kurai wadanda aka yi a baya. Kuma akwai kyakkaywan fatan inganta abin da ake aiwatarwa a 2021.

Exit mobile version