Bankwana Da Ban Masanin Kano 1929-2017

A makon da ya gabata aka kaddamar da littafi mai dauke da bayanan tarihi da kuma gwagwarmayar da Alhaji Maitama Sule (Dan Masanin Kano) ya yi yana raye, saboda haka muka sake yin waiwaye domin duba irin fadi-tashin da wannan bawan Allah ya yi tsawon shekaru 88.

Tun bayan rasuwar Mai Martaba Sarki, Alhaji Dakta Ado Abdullahi Bayero, Jihar Kano ba kara tsintar kanta cikin yanayi na dimuwa da damuwa sakamakon rashin jigo a tafiyar ci gaban harkoki yau da kullum ba wannan makon, inda aka yi wayi gari da babban rashin Alhaji Yusuf Mai Maitama Sule (Dan Masanin Kano), wanda ya yi bankwana da duniya a ranar Litinin, 3 ga watan Yuli, 2017.

Hakika wannan babban rashin ya samar da gibi a sha’anin addini, zamantakewa, siyasa da kuma mu’amala a Nijeriya, kasancewar Dan Masani mutum mai burin ganin ci gaban al’umma ta kowace fuska, shi ya sa lokacin da yake raye yake bada gudunmawa iya karfinsa don tabbatar da ganin kasar nan ta samu ci gaban mai dorewa.

Mutane da dama sun shaidi Dan Masani ba shi da kabilanci; a addinance ko a siyansance, duk bangaren da kake yana baka gudunmawa iyakacin iyawarsa. Kullum burinsa al’umma ta yi ilmi domin ta fa’idantu da sha’anin bambancin da ake da shi tsakanin al’umma.

Za mu dan waiwaya baya kadan domin kawo tarihinsa a takaice:

An haifi Alhaji Yusuf Maitama Sule a shekarar 1 ga watan Oktoban 1929, a unguwar Yola, cikin kwaryar birnin Kano. Maitama shi ne na uku a jerin ‘ya’yan gidansu; Rabi ana mata lakabi da (Yaya ta Zagi), Maimuna kuma ana kiran ta (Yaya ta Bichi). An sa masa suna Yusuf, saboda sunan Mahaifin Madakin Kano Mahmudu, shi Madaki yana kiran shi Abbana.

Sunan Maitama kuwa an sa masa shi ne saboda Galadiman Kano Yusuf, dalilin an yi amfani da makamai sosai lokacin yakin basasar Kano; akan yi wa duk wani mai suna Yusuf lakabin Maitama a wancan lokacin.

Madakin Kano ya yi wa Mahaifin Maitama, Abba Sule Danmuri, mai kula da dukkan al’amuransa na gida da kula da Dawakai. Marigayi Yusuf Maitama yana dan shekaru hudu mahaifiyarsa Hauwa ta rasu. Ita Allah ya yi ta ne mace mai ban dariya, mai raha, ba ta fushi, shi ya sa duk bukin da ya tashi ita ake kira ta yi ta magana a gidan biki, halinta da iya maganarta Maitama ya gado.

Madakin Kano ya saka Maitama a makarantar Elamentari ta Shahuci a cikin watan Janairu 1937. Kafin a kai su makarantar boko, suna yin karatun Kur’ani a gida. A ka’ida shekaru hudu ya kamata a yi a Elamentari, amma saboda hazakar da ya nuna shekaru biyu kawai, ya yi aka ba shi damar daukar jarabawar zuwa makarantar gaba. A wannan lokacin ne Maitama ya fuskanci kalubalen da bai taba fuskanta ba a rayuwarsa.

A wannan gabar ne Madaki Mahmudu, mai daukar dawainiyarsa a rayuwa ya rasu cikin shekarar 1939. Aka bar kujerar Madaki, tsawon shekaru biyu ba a nada kowa ba, har sai a shekarar 1941. Baki dayan dawainiyyar Maitama ta koma kan Mahaifinsa Abba Sule, wanda a wancan lokacin kuma ba shi da karfin da zai iya daukarta. Sai da ta kai Abba Sule, ya sayar da duk wani abunda ya mallaka har da suturunsa na sawa don ya dauki dawainiyar ‘ya’yansa. A lokuta da yawa haka suke kwana da yunwa. Ranar da suka samu dan abin daren gasashehen rogo ne za su ci su kwanta. A karshe Maitama ya shiga makarantar Middle, a wannan datsen an kai matsayin da Maitama ko suturar da zai sa ba shi da ita, kayan makaranta kawai sune kayan sa wansa.

A shekarar 1943 Maitama ya shiga kwalejin Kaduna, yana dan shekaru 13, ya kammala karatunsa na kwaleji cikin shekarar 1948, ya kuma kama aikin Malanta, a makarantar Middle ta Kano. Ya tsaya takarar dan majalisa tare da tsohon Malaminsa a makaranta, Malam Aminu Kano, wannan zabe ya gudane a Central Office a shekarar 1954. Lokacin da aka fadi sakamakon zaben cewa Maitama ne ya lashe, nan take Malam Aminu Kano, ya yi masa mubaya’a da nuna cikakken goyon bayansa

Lokacin da aka fara Jamhuriyya ta farko, ya zama ministan tama da karafa. Bayan faduwar janhuriya ta farko, ya dawo gida Kano, inda ya rike mukamin kwamishina mai kula da kananan hukumomi a gwamnatin Audu Bako. Ya rike mukamin shugaban hukumar sauraren koke-koken, jama’a ta kasa a gwamnatin Murtala. Ya tsaya takarar shugaban kasa a jam’iyyar NPN, amma Shagari ya kada shi a zaben fidda gwani. Ya taba zama wakilin Nijeriya na dindindin a majalisar dinkin Duniya. Kafin daga bisani ya dawo domin ci gaba da bada shawarwari kan harkokin da suka shafi ci gaban siyasa da zamantakewar Nijeriya.

Ya rasu ya bar ‘ya’ya: Bashir Maitama Sule, Umma Maitama Sule, Ahmed Maitama Sule, Abdulkadir Maitama Sule, Zainab Maitama Sule, Umamatu Maitama Sule sai kuma jikoki da dama.

Muna fatan Allah ya yi masa Rahama, ya sa Aljannah makoma, Amin.

.

Exit mobile version