Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RA'AYINMU

Yaushe Za A Daina Zubar Da Jini A Nijeriya?

by Tayo Adelaja
June 22, 2017
in RA'AYINMU
3 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Akwai matukar tashin hankali yadda kullum ake  samun yawaitar asarar rayuka da dukiyoyin jama’a babu gaira babu dalili a kasar nan, musamman baya-bayan nan rikicin da ya barke a garin Ile-Ife na Jihar Osun da Zaki Biam na Jihar Binuwai. Wadannan kashe-kashe suna neman fito da maitar wasu ‘yan Nijeriya fili kan bukatarsu ta zukar jinainan ‘yan uwansu, wanda hakan ke jefa ayar tambaya kan imaninmu da dan’adamtarmu. Lamarin har ya kai munzalin da shi kansa Shugaba Muhammadu Buhari abun ya daure masa kai, yana kokwanto anya ‘yan Nijeriya sun san darajar dan’adam kuwa.

Tsakanin ‘yan shekarun da suka gabata, babu wata rana da ta wuce ba tare da bullar rahoton an kashe wani ko wata ba, kisa wanda ya wuce hankali. Hanyoyin da wadannan mugaye ke bi wajen aikata ta’asa abin tsoro ne matuka, ba su da imani daidai da cikin cokali. Sun mayar da ‘yan uwansu tamkar dabobi, a wasu lokutan ma dabba ta fi ‘yan uwansu daraja; a wurinsu, yin gunduwa-gunduwa da gangar jikin makwabtansu ba wani abu ba ne; su kashe; su bizne, su daddatsa; su watsar kan tituna sannan kuma rika murnar irin barnar da suka yi a bayyane. Shin yaushe za a daina zubar da jinin ‘yan Nijeriya ne?

samndaads

Wadannan kashe-kashe sun dauki sabon salo tun bayan dawowar tsarin mulkin dimukradiyya sakamakon tsagerun matasa da ‘yan siyasa ke amfani da su a matsayin masu kare tawagarsu daga harin ‘yan adawa. Suna ba su mamaki da miyagun kwayoyi su yi abin da suka ga dama har zuwa lokacin zabe. Inda gizo yake sakar shi ne, bayan zabe sai a bar su da makamai a hannu ba tare da an karbe ba, su kuma tun da ba saiti ke garesu ba, kan wata biyan bukatarsu kansu, sai su zama jagororin kansu, ba kwaba balle fada. Da yawan mutane sun tafi a kan wannan shi ne jijiyar da ta yi sanadin bullar bishiyar da ta yi ganyen ta haifar da ‘ya’yan kungiyar Boko Haram, wadanda cikin kankanin lokaci suka addabi Nijeriya da duniya baki daya.

Sojoji na tsaka da fatattakar wadancan masu tayar da kayar bayan, sai kuma ga shi wasu nau’ukan makasan sun sake bulla da sunaye kala-kala; ‘Yan Bindiga ko kuma Fulani Makiyaya, inda suke neman ture wadancan su kafa nasu sansanin shan jinin jama’a. Suna kai farmaki, su kashe na kashewa su raunata na raunatawa, idan hali ya yi kuma su sace mata. Baya ga wannan, ga rikicin kabilanci da yake shirin samun gindin zama, har yanzu kuma ba a dauko hanyar dakile shi ba.

A duk wadannan artabun da ake yi, ba daidaikun mutane ne ke mutuwa ba, a’a, daruruwa ne ko a ce dubbai kuma ba yaki ake yi da wata kasa ba, balle a ce. Jami’an tsaro sun bayyana masu aikata wadannan laifuka a matsayin ‘bata-gari’ wadanda suke son tada zaune tsaye, amma babu koda mutum guda da aka kama balle a gurfanar da shi gaba kuliya.

Mun ga dacewar fito da abubuwa fili, cewar Gwamnoni Jihohi suna karbar kaso mai tsoka daga Gwamnatin Tarayya da sunan Tsaro. Akwai rundunonin ‘Yan Sanda, Jami’an Tsaro, Sansanin Soji da sauran jami’ai masu damara. Amma duk da wadannan sun gaza dakile kashe-kashen da ke ci gaba da yawaita a cikin al’umma tamkar sun mance da hakkinsu na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa bisa alkawari da suka yi.

Kafin yanzu, mafi yawacin zarge-zargen da jami’an tsaro ke yi shi ne cewar, masu kai farmakin ba ‘yan Nijeriya ba ne, suna sulalowa ta iyakokin kasa, su yi barna sannan su fice. Idan har ta tabbata haka ne baki na kawo wa ‘yan kasa hari, to lallai ana bukatar mutumin da zai jagorancin yaki da wannan rashin hankalin.

Shugaban Kasa ya yi wata ganawa ta musamman da Shugabannin Tsaro kwanakin baya don su yi masa bayanin matakan da suke dauka wajen shawo kan wadannan rikice-rikice. Fatanmu shi ne, hukumomi su yi mai yiwuwa don tabbatar da ganin an dawo da martabar ran dan’adam. Halin da ake ciki a yanzu na rashin yarda da aminci tsakanin kabilu, lallai ya dace gwamnati ta yi wani abu, domin zaman lafiya ya fi zama dan sarki!

SendShareTweetShare
Previous Post

RAHOTO: Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Rasa Rai Da Milyoyin Naira A Kebbi

Next Post

NAZARI: Farashin Hajjin 2017 Na Nijeriya: Sauki Ko Tsada?

RelatedPosts

Dambarwar Najeriya Cikin Shekaru 60: Murna Ya Kamata Mu Yi Ko Kuka?

Yayin Da Nijeriya Ta Cika Shekaru 60 Da ‘Yancin Kai…

by Muhammad
4 months ago
0

A jiya ne Nijeriya ta yi bikin cika shekaru 60...

Gwamnatin Tarayya Za Ta Kafa Cibiyar Jinkan Tsofaffi – Minista Sadiya

Kafa Hukumar Kula Da Nakassasun Nijeriya Da Dawo Da Martabarsu

by Muhammad
4 months ago
0

A ranar Litinin, 24 ga Agusta na 2020 ne, Shugaban...

Bashin NIRSAL: Anya Talaka Na Da Rabo A Ciki Kuwa?

Bashin NIRSAL: Anya Talaka Na Da Rabo A Ciki Kuwa?

by Muhammad
6 months ago
0

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta...

Next Post

NAZARI: Farashin Hajjin 2017 Na Nijeriya: Sauki Ko Tsada?

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version