Ra’ayoyi Kan Maganar Obasanjo Ta: Karuwar Yawan ‘Yan Nijeriya Na Tayar Masa Da Hankali

Olusegun-Obasanjo

Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa hauhawar adadin al’ummar Nijeriya na matukar tayar masa da hankali musamman ma, in ya yi la’akari da halin da kasar take ciki, a cewarsa, nan gaba ciyar da al’ummar zai zama abu ne wanda zai kasance mai wahala ga mahukunta.

“Duk lokacin da na tuna da yawan al’ummar da muke da ita a kasar nan, sai na kasa rintsawa, ta wacce hanya za mu ciyar da su? Kwanakin baya alkaluman hasashe suka bayyana yadda nahiyar Afirka za ta fada cikin matsalar karancin abinci, ya za mu yi? In ji Obasanjo.

Obasanjo ya ci gaba da cewa; rashin  aikin yi da matasan Afirka suke fama da shi, ya fi na kusan dukkan sassan duniya, dole ne kasashen Afirka su samar da wata hanyar da za su magance wannan matsalar tun kafin shi al’amarin ya addabi kowa. Dole ne hukumomin Afirka su mai da hankali kan ilmantar da ‘yan baya, saboda kowa ya san yadda ilimi ya ke taimakawa kasa wajen magance matsalolinta irinsu rashin aikin yi, talauci da ma uwa-uba rashin tsaro.

A kan haka ne muka leka shafin sada zumuntarmu na Facebook domin jin ra’ayoyin da mazumuntanmu suka bayyana kan wannan magana ta Obasanjo. Ga su kamar haka:

 

Assalamu alaikum ni a ra’ayina kan wannan batu shi ne,

Wato duk zuciyar da babu Allah a cikinta kuma ba ta yi imani da shi ba, za ka samu ta kan yi tunanin cewar ita ce take tsara wa kanta rayuwa, ita ce kuma ke samar da arziki ba Allah bane.

Wasalam

Sako daga Bashir Musa Faruruwa:

 

Assalamu alaikum ni a ra’ayina kan wannan batu shi ne,

Allah sarki! Idan tsufa ya fara gardama komai tsoho yana iya fada. Ji don Allah kamar su suke ciyar damu.

Sako daga Umar Faruk

 

Assalamu alaikum ni a ra’ayina kan wannan batu shi ne,

Wannan magana ai bama dadin ji, yandu ma ai an iso inda kake hangen gashi gidauniya ma wadda zaka yi amfani da ita wajen  taimakawa baka da ita, balle mu gane da gaske kake yi, cewar shi yawan al’umma yana tada maka hankali.

Daga Sualiman Muhammed Tukur

 

Assalamu alaikum

Obasanjo kada ka manta duk abin da Allah ya

halitta abincinsa yana hannunsa, duk yawanmu ba mu kai yawan mutanen kasar Indiya ba,

amma kuma har Indiya ciyar da Nijeriya take,

Duk wani arziki yana cikin yawan al’umma

Allah ya ba mu yawan al’umma, da kasar noma

matsalar ita ce ba ma amfani da damar da Allah ya bamu

Daga Ghali Muktar Na’Abba

 

Assalamu alaikum. Yanzu duk yawan kashe al’ummar da ake yi ai ko wannan ai ya isa masu ganin an yi yawa, su daina yin maganar hakan. Alhamdulillahi dadin abin dai kowa ma zai mutu kuma kowa zai tarad da sakamakon abin da ya aikata a lissafe.

Daga Grey Nasir

 

 

Barkanku da aiki. Ubangiji Allah shi ne yake ciyar damu tun muna cikin mahaifiya, haka nan ma shi ne zai cigaba da ciyar da mu. Dukkan dan’Adam cinsa, shansa, da arzikinsa yana wajen Allah wanda ya hallicce mu.

Daga Saeed Ibrahim Daud

 

 

Tun da aka kirkiri Njeriya ai babu wata gwamnati data taba ciyar da kowa, dama tun ma kafin a kai ga haihuwar mutum Allah ya dade da yi ma sa tanadin  a rayuwarsa.

Daga Rabilu Hamza Muhammed

 

 

A gaya masa shi kansa kafin Allah ya halicce shi sai daya tanadar mai abincin da yake ci, wanda kuma ba zai kare ba har sai lokacin da yayi bankwana da rayuwar duniya.

Daga Lawan Hamisu Danhassan

 

Tun da aka kirkiri Najeriya ai babu wata gwamnatai da zata ce ta ciyar da mutanen kasar, domin kuwa ai Allah ne yake ciyar da kowa  da kuma biya masa bukatunsa.

Daga Umar El Faruk Alkalin Facebook

 

 

Shi dama na shi tunanin ke nan domin bai san yadda Allah madaukakin Sarki yake kulawa da duk wata halitta tasa, bama kamar mutum, wanda ya fifita fiye da duk wata halitta .

Daga Yahooza Kaseem Bakori Katsina

 

 

 

 

Da yake mu an ja mana kunne da mu yi wa shugabanni biyayya da kuma girmama na gaba, shi ya sa zan yi shiru, amma dai ni abin da na sani babu wata gwamnati da take ciyar da al’ummarta abinci, su ne suke ta dawainiya ta hanyoyi daban su nemi yadda za su tafiyar da rayuwar.

Muhibbullah Nasir Haarun

 

Salamu alaikum, ni dai ra’ayina kan wannan magana ta tsohon shugaban kasa Obasanjo ya yi shi ne, ya kamata shi ya ja girmansa domin har yanzu akwai masu yi masa kallon dattijo, ko da yake ni ba na yi masa wannan kallon. Amma dai idan tsoho bai ji kunyar hawa jaki ba, to jaki ba zai ji kunyar kada tsoho ba, ya kamata ya rike ragowar girmansa, abin da ya saya ya a je idan zai iya ya cinye.

Habulele Muhammad

 

Salamu alaikum Edita ga tra’ayina kan furucin Obasanjo

To dama yaya ba za ka ji tsoro ba ka sace musu dukiya ka bar su cikin talauci da shiga halin kakanakayi, mun sani da kai da masu tunani irin naka duk suna cikin wannan fargabar. Sannan ba za ka taba samun kwanciyar hankali ba tun da baka nemi zaman lafiya ba, ka saci kudin jama’a ka boye ka rasa yadda za ka yi, dole ne ka zama cikin razani.

Exit mobile version