Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Ra’ayoyinku Kan Wanne Bangare Ya Dace Ya Karbi Mulkin Kasar Nan A 2023

by
4 months ago
in TASKIRA
4 min read
Ra'ayi
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

A wannan makon mun nemi jin ra’ayin al’umma a kan, ko wanne bangare ne na Nijeriya ya dace ya karbi ragamar mulkin kasar nan a shekarar 2023.

Hassan Y. Balarabe Ra’ayi na shi ne. indai adalcin dimokaradiyya za a bi to tsarin karba-karba shi ne daidai,wato a ba yankin Kudanci suma su dana Zee Waziri Ya kamata a ba ‘yan kudu dama suma su fito, ko Allah zai sa mu samu cigaba a kasar nan ta hannunsu.

Shamsi Umar Bakanike Dambatta Ni dai a nawa ra’ayin yakamata shugaban kasa ya fito daga kudanchin kasar nan, duba da yadda wanda yake mulkin a halin yanzu shekararsa takwas [8] a kan karagar mulkin.

Labarai Masu Nasaba

Alfanu Da Matsalolin Tiktok Ga Rayuwar Matasa

Kwalliyar Sallar Da Ta Fi Birge Matasa A Wannan Shekarar

Muhd Basheer Sa’ad So so ne amma san kai yafi, Idan mun duba zamu ga cewar babu wani dan kudu da yake zuwa ya yi wa dan arewa aiki haka nan ba tare da yana rike da wata kujera mai girma, amma dan arewa kuwa yana zuwa kudu ya yi aiki ba tare da yana rike da wata kujera ba, sannan kuma mafi yawancin ‘yan arewa basu da kishin yankin su, amma duk da haka ina bkatar dan arewa ya karbi ragamar mulki a shekarar 2023.

Hon. Hafeez KiiDo Ra’ayi na bashi da wani karfi, saboda ra’ayi na ba zai yi daidai da dalilin ba. Mun gwada ‘yan Arewan babu uwar da suka yi mana. Muka sake gwadawa, daga karshe mun gwada wanda muka fi samun nutsuwa dashi ya ci amanarmu. Wannan ya sa na keso a gwada mana dan kudu a karo na uku. Yawanci ana amfani da sunan arewa ne kuma a cutar da ‘yan arewan.

Faisal Haruna Alhunkawee Idan za a bi tsarin karba-karbba kamar yadda aka faro a gwamnatin baya, Obasanjo 1999-2007, Yar’adua 2007 – 2010, Jonathan 2009 – 2015, idan aka lissafa Obasanjo ya yi shekara takwas yana mulki, Yar’adua ya yi biyu (2) saboda rashin lafiya, sannan Jonathan ya yi biyar (6), idan aka hada lissafi kudancin Nijeriya daga 1999 zuwa 2015 sun mulki Nijeriya na tsawon kimanin shekara goma sha hudu (14) wanda yanzu Arewacin Nijeriya bisa Jagorancin Shugaba Buhari sun samu mulkin shekara takwas wanda idan aka hada dana ‘Yar’aduwa za su koma goma. A mahangata yanzu lokaci ne da ‘yan kudu za su yi wa Arewa uzuri su kara shekaru hudu (4) nan gaba kafin su amshi mulki a hannun Arewa.

Engr Kawu Yankoli Yakamata a ba wa ‘yan kudu su dana

Sadiya Garba Kudu don a zauna lafiya

Sadeek Rufa’i Danguguwa Ba kowanne lokaci ne son zuciya ke yin nasara a kan abin da yake zai zamo maslaha ba a tsakanin al’ummah. Don haka a ra’ayina, ina ganin yakamata ace Shugaban kasar Nijeriya na gaba ya fito daga Kudancin Nijeriya. Ba don komai ba sai don a samu daidaito a tsakanin “yan kasa. Bana ganin aibun fitowar Shugaban daga kudu domin dai cigaba ake bukata daga koma ina ne, samuwar Shugaban daga yankin kudu na iya samar wa da yankin Arewa cigaban da ba zato, Kamar yadda ya faru a gwamnati mai ci a yanzu. Inda ayyukanta suka fi shahara a yakin kudun, bayan kuma Shugaban ya fito daga yankin Arewa ne.

Mustapha Yakub Abdussalam Duk wanda Allah ya bawa indai mai tausayin al’umma ne bamu da matsala, fatan mu Allah ya bamu shugaba mai tausayi da adalci a tsakanin al’ummar Nijeriya. Mu kuma Allah ya bamu ikon gyara halayenmu.

Musa G Usman Damaturu Ba ruwanmu da wani kudu koh arewa, kawai adali mu keso.

Hassan Y. Balarabe Ra’ayi na shi ne indai adalcin dimokaradiyya za a bi to tsarin karba-karba shi ne daidai.

Kabiru Ado Muhd Arewa mana, tun da dai shugaban kasar yanzu kudu yafi maida hankali.

Adamu Yunusa Ibrahim Da irin wannan shekara 8 da dan Arewa ya yi a mulki, ai gara dan Kudu ya shekara dubu, matukar za mu samu saukin rayuwa. Idan kuma muka ga akasin haka, mu zage mu yi masa daukar albarka.

Ayat Uba Adamu Nikam a ra’ayina yanzu ko Ojuku ne ya dawo in har akwai alheri a mulkinsa, zan zabe shi.

Adamu Yunusa Ibrahim A ra’ayina yakamata shugaban kasa na gaba ya fito daga yankin kudu. Dalilina shi ne, Nijeriya kasa ce mai yawan kabilu da masu addinai mabambanta. Duk da cewa kundin tsarin mulki bai yi hasashen inda yakamata shugaba ya fito ba, amma tsarin karba-karba shi ne zai fi zama alheri ga kasar. Hakan zai sa sauran kabilu ba za su ji an mayar da su saniyar ware ba. Sannan da irin wannan shekara 8 da dan Arewa ya yi a mulki, ai gara dan Kudu ya shekara dubu, matukar za mu samu saukin rayuwa. Matukar za mu samu zaman lafiya. Idan kuma muka ga akasin haka.

Lawan Muhammad Allah ya zaba mana mafi alkhayri ko daga wane yanki ya fito.

Sani Bello Kano Ra’ayina shi ne bazan sake cewa sai wani ba kawai Allah ya zaba mana mafi alhairi don na daina zabe fakat.

Maryam Nuhu Turau In dai za a yi adalci a kudu yakamata ya fito, amma yanzu tunda muna neman zabin Allah ne mun barwa Allah duk inda ya fi alkhairi Allah ya kawo ma mu na gari.

Mahdee Bashir Duk inda ya fito idan mai kaunar kasar ne, muna maraba da shi Jamila Aminu Ko ma ina ne Allah ya zaba mana mai hankali da tausayi.

Abubakar Ghali Gaskiya a arewa tunda sun fimu yawan shugabanni tun farkon dimokradiyya zuwa yanzu.

Abdul Aliyu Saleh Nagari kawai muke fata mai kaunar talakawa Abdallah M Yau To, Allah ya kawo na gari, amma dan Arewa.

Yahaya Aliyu Sani Gaskiya bamu da wani cikakken zabi, mu dai Allah ya zaba nama mafi allaheri Baban Khairat Koma wanene indai mai adalchi da rikon amana ne, muna maraba da shi

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Tsakanin Maza Da Mata Wa Suka Fi Tafka Rashin Adalci A Zaman Aure?

Next Post

Mene Ne Hukuncin Shan Maganin Tauri A Musulunci?

Labarai Masu Nasaba

Alfanu Da Matsalolin Tiktok Ga Rayuwar Matasa

Alfanu Da Matsalolin Tiktok Ga Rayuwar Matasa

by Rabi’at Sidi B.
5 days ago
0

...

Kwalliyar Sallar Da Ta Fi Birge Matasa A Wannan Shekarar

Kwalliyar Sallar Da Ta Fi Birge Matasa A Wannan Shekarar

by Rabi’at Sidi B.
2 weeks ago
0

...

Sallah

Tsokaci Game Da Sabon Salon Da Za A Ci Bikin Sallah Da Shi Bana

by Rabi’at Sidi B.
3 weeks ago
0

...

Tsokaci A Kan Yadda Matasa Ke Raya Al’adar Tashe A Zamanin Nan

Tsokaci A Kan Yadda Matasa Ke Raya Al’adar Tashe A Zamanin Nan

by Rabi’at Sidi B.
4 weeks ago
0

...

Next Post
Hukuncin

Mene Ne Hukuncin Shan Maganin Tauri A Musulunci?

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: