Connect with us

ADABI

Rabe-Raben Salo A Rubutun Kagaggen Labari

Published

on

Mukala ce ta musamman da Malam Lawan Muhammad Prp ya gabatar da ita don amfanin marubuta a taron Barka Da Sallah da kungiyar marubuta ta Tsintsya Writers Association ta shirya a ranar Litinin 18/06/2018. Kuma wannan shafi ya kawo rahoton taron a ranar Lahadi 24/06/2018. Malam Lawan dama fagensa ne bayar da darasi a kan Dabarun Rubuta Labari tun a Dandalin Marubuta dake facebook cikin shekara ta 2012. Ga dai cikakkiyar mukalar ta Malam Lawan Muhammad Prp, a sha karatu lafiya.

Da sunan Allah mai rahama mai jinkai. Tsira da aminci su tabbata ga shugaban halitta Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi wasallama.

Ma’anar Salo
Salo wata dabara ce ko hanya da marubuci ke bi wajen isar da sakonsa ga makaranta cikin hikima da gwanintar harshewajen tsara kalamai da ayyuka. Ko kuma a ce wata dabara ce da hikima wajen isar da sako ga makaranci cikin hikima da azanci da nuna gwanintar harshe.

Salon bayar da labara ya kasu kasha biyu. Labarin da tauraro yake bayarwa da kansa da kuma wanda Marubuci ke bayarwa.
Akwai kuma salo a bangare guda wanda ya kunshi kashi biyar zuwa shida, shi wannan salo ana kiran sa salon gina labari.
1. Salo mikakke
2. Salo tafiyar kura
3. Salo sassauka
4. Salo Danmagori
5. Raggon salo
6. Salo mai karsashi
Dukkanin wadannan rabe-raben salo ana iya amfani da su a rubutun zube, ya danganta da irin hikima ko dalilin da ya sa Marubucin ya zabi wannan salon.

Salon Bayar Da Labari Daga Bakin Tauraro
Kwatankwacin wannan salon yana iya kasancewa kamar haka;
“Na kammala shirina gabadaya, na dauki jakata na rike. Takalmana a hannu na nufi kofar zaure cikin sanda don gudun kada wani ya gan ni. A daidai lokacin da na bude kyauren ne na ji motsi daga dakin mahaifina sannan aka dalle min fuska da tocilan.
“Wanene nan?” aka kwatsa mini tsawa.”
Daga jin wannan labarin ka san yana fitowa ne daga bakin tauraron labarin, sabanin haka kuma shi ne salon bayar da labara daga bakin Marubuci.

Salon Bayar Da Labari Daga Bakin Marubuci
Misalin wannan salo yana iya kasancewa kamar haka;
Ya kammala shirinsa gabadaya, ya dauki jakarsa ya rike. Takalmansa a hannu ya nufi kofar azure cikin sanda don gudun kada wani ya gan shi. A daidai lokacin da ya bude kyauren ne ya ji motsi daga dakin mahaifinsa sannan aka dalle masa fuska da tocilan .
“Wane ne nan?” aka kwatsa masa tsawa.
Ba daidai ba ne a cakuda salon bayar da labari daga bakin tauraro da salon bayar da labara daga bakin Marubuci.
Salon bayar da labara daga bakin tauraro ya fi ba wa Marubuci wahala saboda dokokinsa, kuma zai yi wahala y agama ba tare da an samu kuskure ba, sannan yana da illoli da ake bukatar lura da su.
Babbar katobarar da Marubuci zai yi a irin wannan salon shi ne a ji jarumin labarin ya ce, “Daga nan sai na mutu.”
Daga cikin illolin akwai;
Ba zai yiwu tauraron labarin ya bada labarin dake zuciyar waninsa ko kuma ya fadi abin da ba ya nan aka yi, ba tare da an nuna labara aka bas hi ba.
Misali; Lokacin da nake tunanin yadda zan samu gida, shi kuma Kabiru yana tunanin Amina a cikin ransa.
Ba zai yiwu tauraro ya bada labarin rayuwarsa yana jariri zuwa (mai yiwuwa) shekaru bakwai, don ba zai yiwu ya san kansa a wadannan shekarun ba, sai dai idan za a nuna labara aka ba shi.
Babu yadda za a yi a irin wannan salon daga karshe a nuna tauraron labarin ya fadi ya mutu. Idan haka ta faru to wanene zai karasa labarin?

Salo mikakke: Salo mikakke shi ne wanda ake fara labara daga haihuwar tauraro zuwa mutuwarsa ko kuma inda labarin zai kare. Misalin litattafai masu kunshe da wannan salo akwai; Iliya Danmaikarfi (Ahmadu Ingawa), Sajida (Umma Rimaye).
Mafi yawan salo mikakke labarin yana tafiya ne kai-tsaye akan tauraron labarin da irin dabi’arsa, wato shi yake kwashe kaso casa’in da doriya na labarin.
Salo tafiyar kura: Wannan salo ne da ake fara labara daga tsakiya ko karshe sannan a koma farko sai a sake komawa karshe, wato ya saba da salo mikakke. Wato labarin zai tafi ne kamar yadda kura ke tafiya, wato bat a tafiya kai tsaye, sai ta yi ta kwana-kwana. Idan za ta je gabas sai ta fara yin kudu sannan ta dawo yamma sannan ta koma arewa, daga nan sai ta yi gabas. Salo tafiyar kura ya fi kowanne salo tasiri wajen rike mai karatu. Misalin wannan salo akwai littafin ‘Yar tsana (Ibrahim Sheme), Cinikin kifi a ruwa (Hauwa Lawan Maiturare).
Salo sassauka: Shi ne salon da aka yi amfani da sassaukar hausa a labarin, hakan ta sa makaranci ba ya shan wahalar fahimtar labarin, domin an yi amfani da saukakan kalmomi wajen gina labarin, maganganun taurari da ayyukansu. Misalin littafi mai kunshe da wannan salo akwai, Walkiya (Muhammad L. Barista), Sababi (Muhammad L. Barista).
Salo danmagori: Shi ne salon da tauraron labara zai dinga wasa kansa, walau shi yake bada labarin ko kuma labarin daga alkalamin Marubucin yake. Sai dai bai dace a ce Marubuci ya dinga wasa kansa a labarin ba, musamman idan labarin daga wurinsa yake, misali ya ce;
Ina labe ina kallon Sadik da Hanan. Bayan sun gama cin kazar amarci sai suka lulluba a bargonsu… A nan sai in ce Sadik da Hanan mu kwana lafiya.
Ko kuma kai tsaye Marubucin ya rikida ya zama tauraro na musamman a labarin.
Misali ya ce, Ina tsaye ina kallon su har suka shige mota, saura kadan su gan ni amma sai na yi hanzari na labe. Daga baya na fito dauke da biro da takarda na bi su cikin motar don kawo muku abin da ya gudana.
Misalin littafi mai kunshe da salo danmagori shi ne, Ruwan bagaja (Abubakar Imam), Gandoki (Bello Kagara).
Raggon salo: Wannan shi ne salon da a labari ake dora wa tauraro wahala ko bala’i haka siddan! Ba tare day a ji ya gani ba, kuma ba a nuna wani laifi day a aikata a rayuwarsa wanda ya jaza masa shiga wannan halin ba. Ko kuma a gina labarin da wani irin gini da mai karatu zai kasa gane kansa da gindinsa. Irin wannan salon yana saurin gundurar da makaranci ya ji duk ya tsani littafin, a karshe ma dai zai ajiye littafin ne bayan ya soma karantawa. Misalin irin wannan littafi shi ne, Ta Kowa (Sani Yusuf Mararraba), Zarishma (Sani Yusuf Mararraba) da sauransu.
Salo mai karsashi: Wannan wani salo ne dake kunshe da nishadi da tsayawa a ran mai karatu saboda yanayin bayar da labarin, musamman wajen kwatantawa, siffantawa da kamantawa. Irin wannan salon yana sanya nutsuwa da son maimaita karanta littafin da kuma rike mai karatu ya ji a ya son ajiye littafin idan ya fara karantawa. Misalin littafi mai kunshe da wannan salo akwai, NaShiga Aljanna (Maimuna Idris Sani Beli), Cuta Ta Dau Cuta (Nazir Adam Salih), Bindigar Kwali (Nazir Adam Salih) da sauransu.

Abin Lura
Yana da kyau a san cewa salo shi ne labari kuma da shi ake rike makaranci, duk labarin da ya rasa ingantaccen salo to yana zama kamar miyar da ba gishiri ne ko kuma shayin da babu sukari.

Manazarta:
Muhammad L. Barista (2013) Salo Da Matakan Nazarinsa (HAF 2013)
I.M.Indabawa , Kabiru Yusuf Fagge (anka) (2014) Dab arun Rubuta Kagaggun Labarai (2014)
Anka Graphics Fagge, 709 Gidan Lemo, Fagge D2, Kano.
Junaidu I (et al) (2007) Harshe Da Adabin Hausa A Kammale: Don Manyan Makarantun Sakandare. Spectrum Books Limited. Ibadan Spectrum House. Ring Road, PMB 5612, Ibadan, Nigeria.

An karanta wannan takarda a taron shekara na kungiyar Marubuta ta Tsintsiya Writers Association, ranar Litinin 18 ga watan Yuni, 2018. Za a iya tuntubar Lawan a 08166473270, 09077405762 ko imel: muhdlawanprp@gmail.com
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: