Rabon Mukami: Ya Dace Rika Fifita Yankinmu – Gwamna Zulum

Abinci

Daga Muhammad Maitela,

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa, Jihar Borno hadi da Arewa maso Gabas su na bukatar kula ta musamman dangane da sha’anin raba mukamai a matakin tarayya.

Gwamna Zulum ya bayyana hakan a ziyarar da ya kai a shalkwatar hukumar kula da daidato wajen raba mukamai ta Nijeriya (Federal Character Commission) a birni Abuja, inda ya bukaci hukumar ta ba Arewa maso Gabas tare da jihar kula ta musamman wajen mukamai.

A lokacin ziyarar, Gwamna Zulum ya samu tarba daga shugabar hukumar tare da sakatarenta; Dr Muheeba F. Dankaka da Mohammed Bello Tukur.

Gwamnan ya ce, wannan bukata ta zama dole ne biyo bayan yadda matsalar tsaron Boko Haram ta tagayyara yankin kana da jihar Borno a kebance, tare da nuni da cewa dubban daruruwan yan asalin jihar Borno ne wannan rikicin ya shafa, sannan kuma da matasa masu dimbin yawa wadanda sun kammala karatu babu aikin yi, duk da kokarin da gwamnatin jihar ke yi wajen samar mu su abin yi.

Zulum ya kara da cewa, “Wannan matsala ta tsaro ta jawo koma baya a jihar Borno, wanda hakan ya wajibi ga wadanda su ka cancanta a jihar samun kula ta musamman wajen samun aiki a matakin gwamnatin tarayya.”

Gwamna Babagana Zulum wanda kuma shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Arewa maso Gabas, ya bukaci hukumar ta cewa suma sauran jihohin arewa maso gabas su na bukatar kula ta daban fiye da wasu jihohi a fadin kasar nan, amma jihar Borno ita tafi sauran jihohin yankin shan wahalar matsalar tsaron, wanda ya dace ta samu kaso na musaman wajen rabon mukamai a matakin gwamnatin tarayya ga matasan ta.

A jawabin shugabar hukumar, Dr Muheeba F. Dankaka ta sha alwashin duba bukatar Gwamna Zulum tare da bayyana cewa babu wanda bai san halin da jihar Borno ta shiga ba, sannan ta kara ba shi tabbacin cewa jihar zata samu kason da ya dace na ma’aikatan.

Dr Muheeba hadi da sauran kwamishinonin hukumar daga jihohin fadin kasar nan, sun yaba da ziyarar da Gwamna Zulum ya kai a shalkwatar.

A tawagar Gwamna Zulum ta hada da shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar, Farfesa Isa Hussaini Marte, tare da wasu kwamishinoni da manyan jami’an gwamnatin jihar Borno.

A wani labarin kuwa, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya dakatar da bangar siyasa a fadin jihar tare da bai wa jami’an tsaro umarnin kama duk matashin da aka samu yana ikirarin bangar siyasa da sunan Ecomog.

Gwamna Zulum ya sanar da hakan a karshen mako a garin Biu ta jihar Borno a sa’ilin da yake kaddamar da bai wa matsakaitan yan kasuwa tallafin naira biliyan daya tare da raba motoci da Keke Napep kimanin 80 don karfafa gwiwar al’ummar jihar wajen samun dogaro da kai. Ya ce matakin dakile bangar siyasa da maula ba kai ba gindi a jihar, inda ya umurci jami’an tsaro cabke duk matashin da aka ga yana bangar siyasa a fadin jihar.

“Wanda ya hada da kwamishinan yan-sanda,Daraktan jami’an tsaron ciki, da sauran dukan jami’an tsaro, ina mai bayar da umurnin kama duk wani wanda ya yi ikirarin shi dan ECOMOG ne, wannan umurnin zai fara aiki karfe 6:00 na safiyar ranar Asabar).”

A hannu guda kuma, ya ce, “Duk wani dan siyasar da ke daukar nauyin irin wadannan yan bangar siyasa, za mu sanya kafar wando daya da shi,” in ji Zulum.

A watan Junairun 2020, gwamnatin Borno ta kashe naira miliyan 515 wajen biyan yan bangar siyasa (Ecomog) kimanin 2,862 alawus na naira 30,000 na tsawon watannin shida. Baya ga karin wasu naira miliyan 384 da jihar Borno ta kashe wajen biyan matasa masu aikin sharar gari, a 2019.

A hannu guda kuma, akokarin sake farfado da tattalin arzikin jihar Borno, a karo na biyu, Gwamna Babagana Umara Zulum, ya kaddamar da raba tallafin naira biliyan daya a matsayin bashi ga matsakaitan yan kasuwa daga kananan hukumomi uku a jihar, a garin Biu.

Gwamnatin jihar ta ware naira biliyan daya domin bai wa matsakaitan yan kasuwa kimanin 5,000 daga kananan hukumomin Biu, Gowza, Ngala, Monguno, Mobbar hadi da birnin Maiduguri.

Tallafin wanda hadin gwiwa ne tsakanin gwamnatin Borno da Bankin habaka masana’antu, sun samar da naira biliyan daya (N1bn) domin raba wa matsakaitan yan kasuwa kimanin 5000 bashin wanda ba shida ruwa.

Baya ga hakan kuma, Gwamna Zulum ya raba motocin sufuri tare da Keke Napep sama da 80 domin samar wa da matasa abin dogaro da kai a garin na Biu.

A jawabin Zulum ga wadanda su ka ci gajiyar tallafin motocin tare da kekuna masu taya uku, ya bukace su da cewa su yi amfani dasu ta hanyar da ta dace a matsayin sana’ar dogaro da kai. Sannan ya ce, “duk wanda ya yi kokari a cikin shekaru uku ya kawo rabin kudin, gwamnati za ta yafe masa sauran kaso 50 cikin dari.”

Exit mobile version