Mairo Muhammad Mudi" />

RAGAYA: Gwamnatin Tarayya, Yaba Kyauta Tukwici

Rubutu da na yi na mako da ya gabata kan rokon Gwamna Malam Nasiru El-rufai na Kaduna da ya bai wa mutanen Suleja sarautar Zariya don su ne ainihin ‘Yan Zazzau da Fulani suka masu kwace, ya jawo cece-kuce da dama.

Wasu sun nuna da gaske ba su san tushen Suleja daga Zariya ba ne ko kuma ba su ma san cewa, ai Abuja an kirkiro ta daga Suleja ba ne. Wasu suna da fahimta na dabam wanda ya ba in mamaki da takaici.

Ina son masu karatu su fahimci manufata ta wannan rubutu, ba don a ba mu sarautar ba ne don na san hakan zai yi wuya amma don duniya ta san tushenmu da irin gudumawa da mutanen Suleja suka bai wa Nijeriya bakidaya wanda a al’umma yau babu wata  al’umma da ta bayar, in kuma akwai a fada mani.

Hatta wadanda aka samu mai a jihohinsu an wayi gari yau, gwamnati na biyan su wani kaso kowane wata amma duk da gwamnati ta san al’ummar Suleja (Abuja) manoma ne, ta karbi filaye bila adadi, babu diyya babu kafa mata wasu masana’antu, babu kayayyakin jin dadin rayuwa, babu makarantun da yaransu za su rinka shiga don neman ilimi. Ko jami’a daya babu, hatta makarantun gaba da firamare da su ke da su, yawanci, wajen kwanan awakai ne saboda rashin gyara.

Har ila yau, yawanci ma’aikatar da masu sana’a na yau da kullum na Abuja wadanda suke ganin tsadar rayuwa ta yi musu tsanani a Abuja, a Suleja suke da zama. Amma wannan bai cancanci gwamnatin tarayya ta taimaka wajen samo da hanyoyi da ruwan sha da wasu kayayyakin more rayuwa ga wannan gari ba.

Wasu sun ce babu yadda al’umma bakidaya za ta ba da abinda Suleja ta bayar ba tare da an ba ta wani abu ba kuma a zauna shiru. Maganar da wasu ke yi cewa mu tambayi manyanmu kila su suka kwanta a kai. Amsata ita ce, sam in har gwamnatin tarayya ta yi wa Suleja wani abun a zo a gani babu yadda za a yi ya boyu da doLe har waDanda ba a haifa ba za su zo su ga wannan abu. Kai ba Suleja ba, har jihar Neja ya kamata ta amfana da wannan tukwici na gwamnatin tarayya.

Abin da ke ba ni mamaki shi ne ba mutanen kasar nan kadai ba amma har da wasu ‘Yan Suleja ba su san daga ina suka fito ba balle su san irin sadaukarwa da garinsu ya yi ga kasar Nijeriya bakidaya.

Mahukuntan kasar nan da kowa aka tabe shi zai ce Abuja ko yana alfahari da Abuja, yawancinsu ba za su iya fada maku yadda aka samo Abuja ba, yawanci gani suke kamar an baro Abuja a itace ne.

An yi amfani da irin halayen iyayenmu da kakanni kara aka yi mana wannan. Na yi wayau na ga ba a sayar da fili a garinmu. In bako ya zo sai dai a ce ya je ya debi duk inda ya yi masa ya yi gini ba tare da an karbi ko sisi a gare shi ba, amma yanzun ko dan gari wani ma bai da filin gini kuma babu hali balle ya saya saboda karancin wuri da kuma tsada.

Rokona shi ne, ya kamata gwamnatin tarayya ta yi wa wadanan mutane na Suleja, in ma zai yiwu da jihar Neja baki daya wajen ganin ta ba ta wani kaso na gyara garin don kuwa har yanzun akwai nauyin da Suleja na daukawa na babban birnin tarayya da babu wanda ke ce mata sannu balle na gode.

Tsorona shi ne kar watarana abin da ya faru da kakaninmu a Zariya ya faru da mu a nan Abuja, saboda haka ina kira da babbar murya ga gwamnatin tarayya ta yi wa mutanen Suleja adalci ta yi masu wani abun da ko da jikokin su sun daga; watarana za su san cewa, cin albasa da kakanninsu suka yi da bakinsu bai tafi a banza ba. Sannan yana da kyau manyan da aka yi wannan abun a idonsu tun kafin su yi kaura, su fadakar da na baya ainihin abun da ya faru kar a wayi gari ya kasance ba su san me ya faru ba sannan su gansu an yi waje da su kuma su kasa yin wani abu tun da ba su san abin da ya wakana ba.

Mutane nawa a cikin Suleja ma a yanzun suke da masaniyar cewa ainihin sunan garinsu, Abuja ne amma iyayensu sun kyautar da kasarsu hade da sunan don raya kasar. Abu ne mai kyau da aka yi amma illar nuna godiya ko da cewa an san an yi ita ce illar da ka hana zaman lafiya watarana in ba a yi hankali ba.

 

Ra’ayinku Ga Ragaya

 

Salamu alaikum Hajiya Mairo,

Kin yi daidai! Naji dadin rubutunki kan sarautar Zazzau.  Allah Ya kara gwarin gwiwa, Ya sa a maki Kwamishinan Yada Labarai ta jihar Neja

Goma, daga  Australia

Amsa: Na gode ranka ya dade amma a bar ni da alkalami ya fi mani.

 

 

Salam Hajiya Mairo mun gode da gudummuwar tarihin masarautar Zazzau da kika ba mu. Hajiya ki koma ma wakar marigayi Dankwairo a wakarsa mai taken

Mai Kasar Suleja Dan Musa, ya kawo kayayyakin tarihin kasar Hausa bakidaya wanda ku kadai yanzu ke da su sannan ya shaida ma Sarki cewa Daura, Abuja duk gidajen kune tun asali saboda haka ku yi hakuri wannan zaben sarkin ya wuce na malam Nasiru tun da na ga tsohon shugaban kasa ya je Zaria kuma ya fadi dangantakarsa da Sarkin Zazzau Shehu saboda haka ya yi endorsing na Turakin zazzau Aminu shehu Idris da fatan Allah Ya tabbatar mamu da alkhairin sa amin.

Daga Muhammad Bashar.

 

Gwamna Malam El-rufai ne kawai zai iya share mana hawaye ya mayar mana da Gadon kakannin mu na asali akan Saurautar Hausawa na Zazzau.

Idan aka bi tarihi kuma aka bi adalci tun daga 1800-1804.

Daga  Yusuf Yahuza, Suleja

 

Exit mobile version