Yusuf Shuaibu" />

Ragin Harajin Shigo Da Motoci Zai Fara Aiki Daga Mako Mai Zuwa

A ranar Talata ce, hukumar Kwastom ta Nijeriya ta bayyana cewa, ragin harajin shigo da matoci da taraktoci wanda ake rage kashi 10 cikin 35 zai fara aiki a mako mai zuwa. Shugaban hukumar Kwastam, Hameed Ali shi ya bayyana hakan lokacin da yake zantawaa da manema labarai a garin Abuja. Ya bayyana cewa, a yanzu haka hukumarsa tana dakon ma’aikatan kudi a kan lamarin kafin a fara gudanar da canjin. Ya bayyana cewa, an rage harajin shigowa da kayayyaki a karkashin dokokin kudade ta shekarar 2020, wannan kokarin hukumar Kwastam ce wanda ta sa aka rage kudaden harajin domin saukaka harkokin sufuri a Nijeriya.

Ya ce, “Wannan kokarinmu ne ya sa aka samu sabon ragin harajin shigo da motoci. Mutane da dama sun ta suka na, suna cewa, na yi amfani damar da nake da ita wajen tabbatar da wannan lamari. Amma kuma daga baya ‘yan Nijeriya sunyi maraba da hakan.
“A yanzu haka ya zama doka. Muna jiran ministar kudi ta bamu dokar a rubuce. A lokacin da muka samu haka, za mu bayyana fara amfani da ita cikin gaggawa tare da sanar wa jami’anmu a ko’ina a fadin Nijeriya.
“Muna fata zuwa mako mai zuwa za mu fara amfani da wannan doka,” in ji shi.
A bangaren yarjejeniyar harkokin kasuwanci na yankin Afirka kuma, Ali ya bayyana cewa, dukkan wani bangare da yake karkashin hukumar Kwastan zai bi wannan yarjejeniya. Ya kara da cewa, ayyukan suna bukatar a samu sakateriyar jarjejeniyar harkokin kasuwanci na yankunan kasashen, domin a samu shugabanci a cikin harkokin kasuwanci. Ya ce, hukumar Kwastam za ta kasance cikin wannan tawaga na harkokin kasuwanci.
Gwamnatin Tarayya ta rage harajin shigo da motoci a karshen 2020. Gwamnatin tarayya ta kawo sababbin rangawame a sabuwar dokar tattalin arzikin kasa. Kudirin kodar harkokin kudade wanda yanzu ya zama doka ya sa motoci za su rage tsada, an dawo da harajin shigo da motocin waje kashi 10 daga kashi 35 da ake biya a baya. Da wannan doka da aka kawo babu haraji kan albashin duk ma’aikatan da abin da suke karba bai wuce naira 30,000 ba, kuma an rage nauyin da ke kan kamfanoni.

Exit mobile version