RAHAMA Ta Horar Da Mata Dubu 18 A Arewa-maso-Gabas

Wata kungiya mai zaman kanta da ke fadi tashin taimakawa hadi da ci gaban mata, mai suna ‘Rahama Women Debelopment Programme’ ta samu nasarar horar da mata sama da dubu goma sha takwas (18) a jahohi hudu da suke cikin Arewa-maso-Gabas, kana kungiyar ta kuma samar wa matan rance mai saukin biya domin taimaka wa rayuwarsu.

Shugaban majalisar Daraktoci na kungiyar ta Rahama, Malam Muhammad Inuwa Bello shine ya shaida hakan a lokacin da ke jagorantar kaddamar da sabbin mambobin majalisar amintattu na kungiyar ta Rahama a jihar Bauchi.

Ya shaida cewar matan da suka samu cin gajiyar bashi mai saukin biyan sun kuma samu horon yadda za su tafiyar da sana’ar hanu domin bunkata musu jarinsu tun a lokacin da suke matakin tatata.

“Mun horar da mata sama da dubu 15 a jihar Bauchi, da karamar hukumar Alkaleri, Tafawa Balewa, Katagum, Darazo, Zaki, Dass, Misau da kuma karamar hukumar Bogoro da suke jihar Bauchi. Mun kuma fadada sauran dubu ukun ga matan da suke makwaftan jihar ta Adamawa, Gombe da Jihar Filato sama da shekaru shida da suka gaba,” in ji Inuwa Bello.

Kamar yadda yake shaidawa, ya ce wadanda suka samu rancen kungiyar ta Rahama sun samu horo ne kan hanyoyin sana’ar saye da saida kayyakin masarufi, yadda za su sarrafa taliyar sufageti, sabulai, kala-kalar abinci daban-daban domin sarrafawa hadi da saidawa ga masu bukata, ya shaida cewar da wasu kayyaki daban-daban ma da masu cin gajiyar shirin suka koya wanda zai taimaka musu gaya kan sana’o’insu.

Da take jawabinta, Babban Daraktan kungiyar Rahama, Misis Miriam Iliya ta shaida cewar a bangaren sha’anin lafiya kawai, kungiyar nata tana da jami’an sa-kai na kiwon lafiya su 480 suka horar hadi da bazasu a cikin al’ummomin Alkaleri, Kirfi da karamar hukumar Itas/Gadau domin taimaka wa jama’a kan sha’anin lafiya da kuma rage yawaitar mace-macen yara da mata masu juna biyu.

“A karkashin tallafin shirin USAID/TShip Project, jami’an sa kai kan sha’anin lafiya ‘CBHBS’ mun horar da su yadda za su kula da mata masu juna biyu da kuma taimaka musu kan yadda za su kare kansu daga matsalolin da suke akwai, koyar da su kan yadda za su shawo kan kamuwa da cutar maleriya ga yara ko mata masu ciki, da kuma yadda za su iya kula da marasa lafiya,” in ji Misis Iliya

Kan cutar kanjamau kuwa, Miriam Iliya ta shaida cewar sun biya ya dalibai 104 kudin karatu a cikin shekara guda domin samar da wadanda za su yi aiki don rage yaduwar cutar. Da sauran jami’an da suka samar kan cutar.

Da yake tasa jawabin, sabun shugaban majalisar amintattu na kungiyar ta Rahama, Mista Abdon Dala Gin wanda tsohon shugaban ma’aikatan jihar Bauchi ne, ya nuna gamsuwarsa kan irin nasarorin da kungiyar Rahama ta samu cimmawa da kuma muhimman aiyukan da ta sanya  kanta domin taimaka wa rayuwar mata da yara.

Mista Abdon Gin ya jinjina wa Rahama a bisa agajin da take samar wa jama’a, yana mai shan alwashin cewar majalisar amintattu da aka kadddamar za su yi kokarin daukaka darajar kungiyar a jihar Bauchi da ma fadin kasar nan.

 

Exit mobile version