Daga Muhammad Awwal Umar. Minna
A daidai lokacin da ake yaba wa Gwamnatin Neja kan cikarta shekaru biyu bisa mulki, mutanen Mazabar Egwa-Gwada sun koka kan rashin samun wadataccen wutar lantarki tare da karancin dakunan karatu a makaranntun sakandare mata da yara.
Kansila mai wakiltar yankin kuma shugaban Majalisar Kansilolin Karamar Hukumar Shiroro, Hon. Jibrin Ladan Gwada ya yi kiran a lokacin da yake zantawa da manema labaru a dandalin ‘yan jarida ta kasa da ke Minna.
Hon. Baba Awai ya ce ‘lallai maigirma Gwamna ya yi kokari gaya domin aikin ruwan sha da aka yi watsi da shi sama da shekaru goma sha, zuwan Gwamnatin Alhaji Abubakar Sani Bello ya mayar da hankali a kan shi wanda yanzu muna anfana da shi”.
“Maganar makarantar sakandare kuwa, in ban da Allah ya sa muna da makarantun sakandare masu zaman kansu saboda yawan dalibai da karatun ya gagari al’ummarmu, dan haka ina kira ga maigirma gwamna a cikin makarantun sakandaren da yake son karawa yankin mazabar Gwada ya sa mu a ciki”. Kamar yadda ya bayyana.