Daga Umar Faruk, Birnin-kebbi
Daminar bana dai za a iya cewa ta zo da baraza ga mutanen Jihar Kebbi, domin a cikin watan mayu da ya gabata mutanen jihar na yankunan wasu kananan hukumomi da dama sun yi hasarar gidajen su da ma wasu dukiyoyin su.
Abin ya fi muni ga mutanen Karamar Hukumar Maiyama wadanda sun fuskanci barazanar barnar ruwa har gidaje da dukiyoyin miliyoyin Nairori suka salwanta a yankin, har ya kai ga shigowar hukumar ba da agajin gaggawa ta tarayya domin tallafa wa wadanda abin ya shafa.
Har ila yau, a cikin makon da ya gabata mutanen Kananan Hukumomin Aliero, Kalgo da Birnin-Kebbi bala’in ambaliyar ruwa ya lashe gidajensu da dukiyoyi na miliyoyin Nairori.
A yayin da Gwamnan jihar Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya samu labarin irin laba’in da ya aukawa mutanen jihar sa, inda barnar ruwan ya zama sanadiyyar mutuwar Abubakar Bawa Kwakware dan shekara talatin a duniya kan wani babban ice da ya far masa a cikin gidansa da ke Kwakware a Karamar Hukumar Kalgo, ya kai ziyarar gaggawa ga yankunan da abin ya shafa don jajanta musu ga irin abin ya da same su.
Har ila yau, Gwamna Bagudu ya ziyarci garuruwan Aliero, Kwakware, Kuka-Nayelwa Karamar Hukumar Kalgo da kuma garin Makera a cikin Karamar Hukumar Birnin- Kebbi domin gane wa kansa irin barnar ruwan da aka samu a yankunan.
Haka zalika Gwamnan ya jajanta wa mutanen da abin ya shafa, ya kuma roki Allah da ya saka musu da wata hanya mafi alhairi, ya kuma jawo hankalin su da su dauki wannan matsalar barnar ruwan wata kaddara ce wadda Allah ya kawo musu, don haka su bar ma Allah lamarin sa.
Bugu da kari, Gwamnan Bagudu ya umurci hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Kebbi da ta tantace mutanen da bala’in ambaliyar ruwan sama ya aukawa dukiyoyin su, domin ba su agajin gaggawa.
Daga nan ya kara ba mutanen hakuri da kuma basu tabbacin Gwamnatin sa na taimaka musu. Daga nan ya kai ziyara ga Sarkin Aliero da kuma ubannin kasar kuka-Nayelwa, Makera, Kwakawre da Sandare da sauran yankunan don jajanta musu.
Da suke jawabin godiya ga Gwamnan Jihar Kebbin, Sarkin Aliero da kuma Ubankasar Makera, sun gode wa Gwamnan Bagudu ga irin ziyarar tausayawa da ya kai a yankunansu da kuma irin gudunmuwar da ya bayar ga mutanen su da barnar ruwa ta shafa.
Ma’aikatan Gwamnati da suka tarbi Gwamnan jihar a yayin da ya kai ziyarar kananan hukumomin da barna ruwan ta shafa sun hada da Danmajalisa mai wakiltar Kalgo a majalisar dokoki ta jihar, Ahmad Kuka, Sakataren karamar hukumar mulki ta Birnin- Kebbi, Alhaji Sani Muhammad Mashaya da kuma Alhaji Abu Sale Aliero da sauran su.