Daga Muhammad Maitela, Damaturu
Jam’iyyar APC mai mulki a Jihar Yobe, ta sanar da dakatar da sabon Daraktan Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Alhaji Mustapha Yunusa Maihaja daga jam’iyyar baki daya.
Matakin wanda shugabanin jam’iyyar suka bayyana, ya zo bisa kan zargin rashin biyayya da uwar jam’iyyar ke yi masa.
Alhaji Abubakar Bakabe ya bayyana cewa “bisa dokar sashe na 21’D’ da kuma a karamin sashe B cikin baka, na kundin dokokin jam’iyyar APC ya baiwa wannan kwamitin gudanarwa damar daukar mataki ga kowanne dan jam’iyyar wanda ya nuna halin rashin biyayya. Bisa ga wannan, Maihaja ya ci mutuncin wadannan dokoki na APC ta inda ya garzaya kotu tare da yin karar zababben Gwamnan da ya lashe zaben 2015, Alhaji Ibrahim Gaidam kuma ba tare da saurare ko kallon kan shugabanin jam’iyyar da gashi ba; ya yi gaban kan sa.
“Duk da matsayin Alhaji Maihaja na dan takarar kujerar Gwamna a APC, ya garzaya kotu tare da kalubalantar dan takarar da jam’iyya ta tsayar a zaben 2015 wanda ya gudana, yana mai zargin cewa ya sha rantsuwa sau biyu – ta farko bayan rasuwar marigayi Mamman Ali, sannan ga na zaben 2011. Duk da wadannan zarge-zarge nashi biyun, ya sha kasa a kotun daukaka kara da ta koli”. Ta bakin Bakabe.
“Har iala yau, jam’iyya ta gano cewa Maihaja ya yiwa dokokin APC karan -tsaye, Idan an duba sashe na ‘A’ mai karamin sakin – layi na 10. Sashen da ya yiwa kowanne dan jam’iyya kan-da-garkin garzayawa kotu da nufin kalubalantar jam’iyya ko jami’an ta dangane da kowanne abu ta hanyar daukar matakin kashin kai wajen sabawa kudin ba”. Ya nanata
Abubakar Bakabe ya sake bayyana cewa wannan mataki wanda babban Daraktan NEMA ya dauka ya sa jam’iyyar ta dare gida biyu sannan ya jawo rarrabuwar kai da rashin hadin kai, da rashin ganin kima a cikin jam’iyyar APC a Jihar Yobe.
A sa’ilin nan ne sakataren jam’iyyar APC a Jihar Yobe, Alhaji Abubakar Bakabe ya bayyana cewa “bisa ga wadannan dalilai, jam’iyya ta dakatar da Mustapha Yunusa Maihaja shi sai Illa Masha Allah, tare da bashi shawarar cewa hawainiyar sa ta kiyayi ramar jam’iyyar APC dangane da alakanta kansa da ita wajen bayyana kansa dan jam’iyyar, cikin lamurran sa na yau da kullum”. In ji sanarwar.
Duk kokarin jin ta bakin Alhaji Mustapha Yunusa Maihaja dangane da wannan lamari ya ci tura domin wakilinmu ya buga wayar sa a lokuta daban-daban tana kara amma ba a dauka ba, sannan ya aika sakon kar – ta-kwana shi ma dai shiru har zuwa lokacin hada wannan rahoton.