Daga Muhammad Awwal Umar, Minna
An bayyana sana’ar nika da surhe a matsayin sana’ar da ta samo asali a rayuwar dan Adam, shugaban kungiyar masu sana’ar nika da surhe ta jihar Neja, Alhaji Muhammadu Jibo Kuta ne ya bayyana hakan a lokacin rangadin kafafen yada labarai a Minna fadar Gwamnatin Neja.
Jibo Kuta ya ci gaba da cewar “ganin yadda rashin aikin yi ya zama ruwan dare yanzu haka kungiyarsu ta kuduri aniyar mai da hankali a manyan ayyuka guda uku, koyar da matasa sana’ar nika, ba da dama ga wadanda suka manyanta kuma suke muradin sana’ar ta hangar dora shi a hangar da zai iya cin moriyar sana’ar, na uku kuma yanzu haka kungiyar ta bada dama ga wanda ke da kudi kuma yana son sanya hannun jari a kungiyar ta yadda kungiyar ce za ta dauki nauyi kula da jarin ta yadda mai dukiyar zai Iya cin moriyar ribarsa da dukiyarsa ke janyowa a karshen kowani wata.
“Yanzu haka idan ka cire wadanda ba su yi karatun ba, da wadanda karatunsu bai yi nisa ba a kowani shekara ana samun matasa dubu saba’in da biyar ne ke kammala karatun jami’a wanda dubu sha biyar ne ke iya samun aiki a hannun Gwamnati da wasu kamfanoni, wannan matsalar na rashin aiki ga matasa ya fi matsalar Boko Haram illa a cikin al’umma. Rashin aiki babban matsala ne a rayuwar matasa da al’ummarmu da cigaban tattalin arzikin kasa”.
Da yake karin haske ga wakilinmu, shugaban kungiyar a Neja ta tsakiya, Malam Usman Yakubu ya ce a yankinsu babban matsalar da suke fuskanta bai wuce matsalar wutan lantarki ba, duk da cewar kusan kashi saba’in da biyar na wutan lantarki daga yankinsu ake tatsarsa. “Zamani yazo da kusan komai ya ta’allaka ne a kan wutan lantarki, dan haka muna kira ga Gwamnatin jiha da kamfanonin da ke Samar da wuta a jihar nan da su inganta shi”.
Shugaban ya ce wannan sana’ar ta samarwa jama’a da dama rufin asiri, “kungiyar mu tana shiga dan walwale matsalolin da suka shafi wutan lantarki ba Wanda bai fi karfinmu ba kuma ita kanta Gwamnati na karuwa da mu wajen kudin shiga”.
Da yake bayani a madadin kafafen yada labarai, babban darakta a kamfanin buga jaridun Newsline Newspapers da Tauraruwa, Malam Ndama Abubakar, ya ce kungiyar duk da cewar jarirya ce ta zo da manufofi nagartattu da kafafen yada labarai za su yayata shi, musamman rayuwar mutumin da ya bar aiki abu ne mai kyau ya samarwa kansa madogara.