RAHOTO: Biyafara: Hadin Kai Muke Bukata, Ba Rabuwa Ba —Sanata Jibril

Daga Musa Muhammad, Abuja

“A ra’ayina na dan Nijeriya, kuma daya daga cikin dattawan Arewa, ina so in fadi cewa mu in sonmu  ne mu zama mun hada kanmu ne a Nijeriya da kowane irin kabila da kowane addini, musamman addinan nan guda biyu, musulunci da kiristanci, ba mu da dama mu hana kowa ya rayu a Nijeriya, domin Nijeriya kasar mu ce. Domin wata kila su masu neman a kori Ibo su koma yankinsu, ba su yi dogon tunanin abin da zai iya biyo baya ba ne. Ni ba mai son a kori kowa daga Arewa ba ne, ni mai neman hadin kan kasar nan ne.”

Wadannan kalamai sun fito ne daga bakin wani dattijo daga cikin dattawan Arewacin kasar nan, Sarkin Fulanin Nasarawa, Sanata Walid Jibrin a lokacin da yake zantawa da manema labarai cikin makon da ya gabata a Kaduna.

Sanata Walid ya ci gaba da bayyana cewa, duk dayake masu wannan kiraye-kiraye suna yi ne bisa kafa hujja da kalamai da abubuwan da su wadancan ke yi, amma yana da kyau a yi tunanin yadda kasar nan za ta zama idan an biye masu. Ya ce, “shi ya sa yara matasa suka tashi suka yi irin wannan gori. Kowa yana da tasa manufar, da abin da yake so ma kabilarsa da kuma addininsa. Amma kullum idan za mu yi haka, to mu yi tunanin yadda kasar nan za ta zama. Kamata ya yi mu yi tunanin yadda za mu hada kanmu a kasar nan, yadda komai namu zai tafi daya, ba tare da mun samu wani cikas ba.”

Sarkin Fulanin na Nasarawa ya kuma soki su kansu ’yan kabilar ibon da suke neman wannan fandarewa, da cewa wannan ba daidai ba ne, “wannan ba daidai ba ne. Kuma idan ma za a balle, kowa na neman nasa ’yancin, amma mu nemi ’yanci din bisa ga lumana. Akwai hanyoyin da ake bi na arziki, na gaskiya na lumana idan kana so ka samu kasarka daga cikin wata kasa. Za a je a tattauna a Majalisunmu, suna da wakilansu a wurin,” ya ce.

Da ya juya game da rigingimun Fulani da ke faruwa tsakanin makiyaya da manoma da wasu kabilu a kasar nan kuwa, Sarkin Fulani kira ya yi da a duba batun sosai, “domin idan ba a duba shi ba, ina ganin zai kai mu ga irin matsalar Boko Haram, domin ba karamar magana ba ce,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa a yawancin wadannan rigingimu, magana ce akan fili, wanda abin da su manoma ke so, shi ne su cire wannan ciyawa su zubar da ita saboda su samu yanayi na nomansu mai kyau, “mu kuma Fulani muna ganin wannan ciyawa a matsayin abincin dabbobinmu, idan ka shareta ka kawo wa Fulani matsala. Wato Fulani yana bukatar ya tafiyar da shanunsa a kewaye a kasar nan a cikin ’yanci . Domin yana ganin shi ma yana da ‘’yancin ya yi kiwo a ko’ina cikin kasar nan. Kamar yadda muka koka cewa kada a kori Inyamurai a kowane yanki na Arewa, haka su ma Fulani akwai bukatar a hada kai da su domin a samu zama lafiya.”

Ya ci gaba da bayyana cewa, akwai bukatar su ma a biya masu bukatunsu na kiwo domin su samu ci gaba ta yadda za su yi kiwo a kasar nan, ba rigima suke nema ba. “Babu shakka rikicin nan abin damuwa ne a wasu jihohi, misali wadanda ke da nufin korar Fulani, da masu nufin samar da dokokin da za su takura wa Fulani, wannan ba daidai ba ne,” in ji shi.

Saboda haka sai ya ba da shawarar cewa, “abin da ya kamata a yi, shi ne a zauna domin tattauna yadda za a magance wadannan al’amura, a zauna da ’yan Majalisunmu da dattawanmu da ’yan kungiyarmu ta Fulani domin a tattauna yadda za a magance wannan matsala, da yadda za a samu zaman lafiya a tsakanin Fulani da sauran kabilun kasar nan. Abin da ke faruwa a jihar Benue da Taraba ba abu ne da zai kawo mana zaman lafiya a kasar nan ba.”

“Ka ga kamar Gwamnan jihar Taraba, ba mutum ne mai neman rigima ba, mutum ne da nake ganin yana son zaman lafiya. Don haka mai zai hana a samu Fulani da jama’ar Gwamna a zauna a tattauna wannan fitina ta yadda za a samu mafita. Misali, dubi yadda rigimar jihar Filato ta ragu matuka. Saboda haka me zai hana mu bi wannan tsari domin maido da zaman lafiya da fahimtar juna irin na  jihar Filato,” ya ce.

“Yanzu a garin Jos rigingimu sun ragu matuka, amma a jihar Taraba kuwa abin sai kara habaka yake yi. Yana da kyau a dubi matsalolin Fulani a Taraba da kuma matsalolin sauran kabilun Taraba da nufin tattaunasu domin a samu maslaha,” in ji Sarkin Fulanin.

Sanata Walid ya ci gaba da nuna takacinsa, musamman game da abubuwan da ke faruwa a jihar Yaraba, inda ya ce, “a halin yanzu abin da ke faruwa a jihar Taraba abin kunya ne a gare mu, domin  wata hanya ce da za ta iya kawo wata babbar fitina a kasar nan. Mu a matsayin mu na manyan Fulani, ba za mu yarda a shiga cikin wata rigima da za ta kawo tashin hankali a kasar nan ba. Abin da muke so shi ne zaman lafiya. Amma kuma akwai bukatar sauran kabilu su ma su fahinci Bafulatani, domin shi ma a taimake shi ya zauna lafiya a kasar nan da dabbobinsa kamar kowa.”

“Ina ganin ya kamata mu kauce wa kashe-kashe, domin yin hakan ba daidai ba ne. Kuma akwai bukatar mu canza tsalo. Ina kuma yin kira ga gwamnatin tarayya ta saka baki wajen kawo karshen wadannan rigingimu. Idan babu zaman lafiya a wannan kasa ba za a taba samun kwanciyar hankali ba. Mu muna nan muna taro muna kuma fatan su ma kabilun za su yi nasu taron domin mu zauna taburi daya a tattauna wannan matsala. Ni a yanzu yadda abin yake, yana ba ni tsoro,” in ji Dattijon.

 

Exit mobile version