RAHOTO: Burinmu Majalisa Ta Yi Dokar Tilasta Gwajin Kanjamau Kafin Aure — Dakta Bashir

Daga Mustapha Ibrahim Tela Kano

Babban Daraktan Hukumar Yaki da Yaduwar Cutar Kanjamau ta Jihar Kano, Dakta Usman Bashir ya ce yanzu haka suna da burin gabatar da kudiri ga Majalisar Dokokin Kano domin ta yi dokar da za ta tilasta wa saurayi da budurwa da sauran baligai yin gwajin cutar kanjamau kafin su yi aure.

A cewarsa, yin hakan ne zai tabbatar da ingancin lafiyar ma’auratan tare da dakile yaduwar cutar a tsakanin al’ummar Jihar Kano.

Dakta bashir ya bayyana haka ne a yayin bikin ranar yaki da cutar da kuma kokarin da ake na nemo rigakafin cutar da kuma kokarikn kawar da ita a doran kasa. Ya ce an kai shekara ashirin ana wannan kokari na nemo wannan rigakafin cutar kanjamau a duniya amma har yanzu ba a samu ba, sai dai duk da haka ana ta iya kokari kuma da alamun za a samu nasara. A cewarsa, yanzu haka akwai mutum dubu biyar da ake aikin gwaji da binciken rigakafin a kansu a Afrika ta Kudu.

Dakta Bashir ya kuma yanzu haka kokarin da wannan hukuma take yi da goyon bayan Gwamnan Abdullahi Umar Ganduje, akwai asibitoci 194 na Gwamnatin Kano da ake gabatar da gwaje-gwaje ga duk wanda yaje yana bukata, a wani bangare na kokarin da ake yi na kawar da wannan cuta da kuma dakile yaduwar ta a tsakanin al’umma.

Haka kuma ya ce in dai aka gwada mutum aka ga yana da ita, ana bashi magani to ba shakka baya iya yada ta, don haka ya shawarci dukkan masu wannan larura da su tabbatar suna aiki da dokoki da ka’idojin da aka sa musu na shan magani.

Dangane da adadin mutanen da suka kamu a jihar kuwa, ya ce “adadin masu dauke da wannan cuta a Najeriya su ne kashi uku cikin dari yayin da Kano take da adadin kashi biyu cikin dari na yawan al’ummarta, wato mutum 280,000, kasancewar jihar tana da adadin mutane sama da miliyan goma”.

Ya kuma ce wannan hukuma na iya kokari na ganin ta wayar da kan mutane ta kafofin yada labarai ta yadda za a kauce wa kamuwa da cutar ta kanjamau.

 

Exit mobile version