RAHOTO: Fastoci Sun Ziyarci Masallaci A Kaduna, Sun Yi Bude Baki Da Musulmai

Daga Abdullahi Usman, Kaduna

A cikin makon da ya gabata ne tawagar Malaman Addinin Kirista, karkashin jagorancin Pasto Yohanna Buru, jagoran Cocin ‘Christ Ebangelical Intercessory Followership Ministry’ da ke Unguwar Sabon Tasha Kaduna suka ziyarci wani Masallaci, inda suka yi bude baki da al’ummar musulmi don kyautata alaka tsakanin mabiya addinan guda biyu.

Wakilinmu ya shaida mana cewa a wannan ziyarar da tawagar Fastocin suka kai masallacin ’Yan Doya da ke babbar kasuwar Kaduna, mabiya addinan guda biyu sun ci abinci tare, wanda kuma dama sun saba kai irin wannan ziyara a duk shekara.

Da yake jawabi bayan kammala bude bakin, jagoran tawagar Fartocin, Fasto Yohanna Buru ya bayyana cewa sun zo masallacin ne don taya al’ummar musulmi murnar fara azumin watan Ramadan, da kuma rokon su da su nunka ibadunsu a wannan wata, musamman salloli da karatun Alkur’ani mai girma. Sannan ya roki matasan musulmin da su mayar da hankali zuwa wajen tafsirin Alkur’ani da ake yi a wannan wata don neman yardar Allah.

Ya ce, wannan ziyara tasu wata aba ce don kara kyautata hulda tsakanin Malaman Addinin musulunci da kuma na addinin kirista, don kyautata alaka da kuma yafe wa juna, da kuma aika sakon zaman lafiya da hadin kai don kawar da kiyayya da gaba da kuma yaki da rikicin addini ko na siyasa.

Fasto Buru ya ci gaba da cewa, “mu a matsayinmu na shugabannin addinin kirista, duk shekara muna zuwa gidan yari mu fidda ‘yan uwanmu musulmai don su yi azumin wannan wata a gidajensu da iyalansu da abokai kamar sauran musulmai. Sannan muna ziyarar Malamai don yin bude baki tare da su. Sannan mukan halarci tafsiri don mu karu gaba daya.”

Malamin ya ci gaba da cewa, “don haka Muna kiran al’ummar musulmai da su yi wa Nijeriya addu’a da kuma shugaban kasa. Sannan su yi addu’a don samun ci gaba mai amfani a kasar nan. Sannan su yi addu’a don marasa lafiyarmu, Allah ya ba su lafiya, sannan su yi addu’a don ci gaba da dunkulewar kasar nan.”

Ya ce, sun san muhimmancin addu’a da kuma azumi, don haka suka zo don yin roko ga al’ummar musulmai da su ci gaba da yi wa kasar nan addu’a don ci gaba da dunkulewar kasar nan waje guda ba tarwatsewa ba.

Da suke nasu jawaban, Fasto George John, da kuma Rabaran John, duk sun bayyana jin dadinsu ga wannan ziyara da suka kai Masallacin. Sannan suka yi kira ga gwamnatocin jihohi da na tarayya da su mayar da hankali wajen shirya tarukan da za su hada kan mabiya addinai daban-daban a kasar nan. Suka ce yin hakan zai taimaka sosai wajen samar da hanyoyin tattaunawa tsakanin mabiya addinan don samar da zaman lafiya a tsakaninsu.

Da ya ke mayar da jawabi, babban Limamin masallacin, Shaikh Ibrahim Kyauta ya bayyana cewa Allah ne kadai zai saka wa Malaman addinin kiristan da suka kawo masu wannan ziyara har suka yi buda baki tare da su.

Daga nan Shaikh Ibrahim ya yi kira ga jama’a da su yi koyi da halin wadannan shugabanni da suka kawo masu wannan ziyara. Ya ce, yana da kyau a rinka kai irin wannan ziyara a wurin aiki ko a wurin ibada, domin yin hakan zai kara dankon zumunci da kaunar juna.

Daga Malamin ya yi godiya ta musamman ga jagoran wannan tawaga, wanda ya ce wannan ne karo na biyar da suke zuwa suna taya su buda baki a wannan Masallaci.

Exit mobile version