Daga Mustapha Ibrahim, Tela Kano
Fitaccen Malamin nan a duniya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya yi wani gagarumin taron shan ruwa tare da mabiya tafarkin Shi’a, inda aka gayyaci dandazon ‘yan jarida na cikin gida da waje a Kano, a ranar Litinin ta makon nan.
Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya yi bayanin cewa “Allah da Manzonsa shi ne babban karfinmu to sai Ahlil Baiti, don haka mu muna son Ahlil Baiti kuma ba mu da wata matsala da masoya Ahlil Baiti domin ba wani fada ko tashin hankali a tsakanin mu da yan Shi’a domin suna son mu suna girmama mu suna karrama mu suna san sharifai sosai. Kuma suna harkoki tare da mu kuma suna bin mu sallah ga shi yanzu mun ci abinci tare da su kuma suna ziyartar mu har ma shugaban su Sheikh Zakzaky mun sha yin zikiri da shi, don haka ba mu da wata matsala”.
Haka kuma malamin ya jaddada cewa mu “mu ‘Yan Tijaniyya muna tare da su tunda ba sa kafirta mu ba sa ce mana mushirikai don haka soyayyar sharifai Ahlil Baiti da son Allah ya hada mu da su. Amma ka ga da masu ce mana mushirikai ko kafirai ba ma tare da su tunda ba sa cin yankan mu ba sa bin mu sallah, sun yarda da duk salati amma ba su yarda da Saltail Fatih ba, mu kuma duk wanda ya yarda da Salatil Fatih mu mun yarda da shi babu wata matsala amma wanda ya kafirta mu ai ka ga kun rabu da shi kenan”.
Don haka Sheikh Dahiru Bauchi ya yi Nasiha ga mabiya Shi’a da su raba kansu da masu maganganu mara sa dadi masu muni. Inda kuma ya yi Nasiha gare su a kan cewa su bi hukuma a hankali ba tare da tashin hankali ba, “domin bin hakkin ka a cikin hankali da lumana Musulunci bai hana ba, domin in ba ka bi a hankali ba sai hukuma ta rike hannunka ta dake ka dashi ta ce kai ne ka doki kanka”, kamar yadda ya fada.
Har ila yau, Shaikh Dahiru Usman Bauchi ya yi kira da babban murya na cewa Gwamnati ta saki shugaban mabiya Shi’a Sheikh Ibrahim Yakubu Alzakzaky, a cewarsa “yin haka zai sa zuciyoyin miliyoyin mabiyansa su samu sanyi wanda hakan zai kawo zaman lafiya a cikin al’umma kuma in batun rashin tsaro ne ya sa ba’a sake shi ba to a sake shi a tsare lafiyar sa”.
Haka kuma a karshe ya yi kira a kan matasan Arewa da shugabannin su da matasan Kudu shugabannin su a kan abi a hankali wajen warware rikici da yake kokarin tasowa da sunan biyafara.
“Wa’adin da matasan Arewa suka ba inyamurai a bi a hankali duk da yake wanda ya fara zalunci shi ne babban azalumi domin can Kudu ake hana mutanen mu gina Masallaci da makabarta amma kuma har ma an hana Fulani shiga wasu wurare a Kudu wanda mu kuma a nan ba haka bane, amma dai kamar yadda wani ya ce a shekarun baya kasa ba a raba ta akan Tebur sai dai a bakin daga, don haka sulhu shi ne alkahairi a dukkan lamari ba tashin hankali ba, kuma kowa a masa adalci, Nijeriya kasar musulmi ne da wanda ba musulmi ba”, cewar Sheikh Dahiru Bauchi.
Da yake jawabi a nasa bangaren, Wakilin Shaikh Zakzaky, Shaikh Yakubu Yahaya Katsina, ya bayyana cewa, “wannan rana ko da kalma daya Shaikh Dahiru Usman Bauchi ya furta ta fi wa’azi na shekara goma tasiri domin haka Allah ya tsara kuma ya ba su Shehu Dauhiru Usman wannan baiwa don haka, ba a rabu ba ma tun farko balle a ce yau an hadu. A’a malaman Darikar Tasawwuf ta Sufaye su suka haife ni kuma su suka yi tarbiyar mu, don haka ba wani abu sabo a tsakanin mu da wadannan malamai. Don haka ba wani Masallaci na kashin kanmu, su muke bi sallah ko hana mu aka yi ba za mu gina masallaci ba sai dai mu koma gida mu yi sallah”, in ji shi.
Shaikh Yakubu Yahaya ya kuma ce su Almajiran Sheikh Ibrahim zakzaky ba a raine su a kan zagin Sahabbai ba, kana ya kara da cewa “‘yan Shi’a masu zagin Sahabbai kamar ‘yan hakika ne a cikin Tijaniyya, don haka ba ma tare da su domin zagi ba ibada ba ne kuma ba zai taba zama ibada ba har abada. Kuma Sahabbai muna son su muna bin koyarwar su, don haka ba wani abu da za ka ce zagi shi ne ibada, domin idan ma wani abu aka yi na ba daidai ba, to ai ya wuce, saboda haka ma ba za ka iya gyarawa ba. Don haka abu ne kowa ya yi kokari ya kwaci kansa shi ne kawai magana. Mu ba ma kan wannan layi na zagin wadanda suka taimaki manzon Allah (SAW)”.
Malamin ya ba da misali da Ikiramata dan Abu Jahil lokacin da zai Musulunta, “Manzon rahama ya ce kada wanda ya zagi ubansa Abu Jahil duk da kasancewa Abu Jahil shi ne babban makiyin Manzon Allah. Amma yanzu haka akwai gidan talabijin da mikiya Allah da manzonsa suka kafa a daya daga cikin kasashen turai da ake kira Fadak TB na yan Shi’a da wani Yasir Habib na fadak TB da suka sai da lahirar su a duniya suna magana cewa su Shi’a ne suna zagin manya-manyan Sahabbai don biyan bukatar makiya Musulunci na cikin mu da na waje wanda kuma masarautar kasar ce take daukar nauyi a kokarinsu na hada fada a tsakanin Shi’a da sunnah a duniya baki daya.
Har ila yau, ya ce “wani abun takaici kuma shi ne akwai wata kasa ta musulmi da ta ware Dala biliyan 20 dan kafa gidajen talabijin da rediyo da biyan malamai da aka dasa da sunan malamai da za su taimaka wajen cimma wannan burin a hada fada a tsakanin musulmi da kuma cusa miyagun maganganu da za su haddasa kyamar juna, don haka kowa ya sani duk abin da ya yi shi zai gani a ranar lahira”.
A karshe Sheikh Yakubu Yahaya ya ce dangane da rigimar Biyafara, ba sa goyon bayan raba Nijeriya, abun da Shaikh Zakzaky ya dora su a kai shi ne in son samu ne Nijeriya ta hade da Nijar da Chadi da Kamaru, ya zama kamar kasar Chana.
“Mu yi girma domin kasar mu da arzikin mu su zama muna da karfi a duniya amma idan rabuwar ta kama a ra’ayin mu shi ne ba bukatar tashin hankali ko fadace fadace, ba ma bukatar a harba harsashi ko daya ko wani ya rasa ransa a rabu kamar yadda Cassalabakiya ta yi a 1991, da yadda kasar Rasha ita ma ta rabu ta hanyar jefa kuri’a”, kamar yadda ya bayyana.