Daga Muhammad Awwal Umar, Minna
Sama da cibiyoyi tamanin da biyar ne Gwamnati Neja ta ware dan ciyar da almajirai da marasa karfi a Azumin watan Ramadan na bana.
Babban darakta mai kula da harkokin addinai da jinkan marasa karfi, Dakta Umar Faruk Abdullahi ne ya bayyana hakan bayan kammala shan ruwa da ya shiryawa manema labarai a jihar.
“Bayan lura da wasu halaye da suka sabawa ka’idodin hukumar mun gaggauta rufe wasu cibiyoyin a garin Minna. Aikin ciyarwar wanda mun gada ne daga Gwamnatin da ta shude kuma aikin ya zagaye dukkanin masarautu takwas da ke jihar nan, kamar a masarautar Kagara da Suleja masu martaba ne suka kafa kwamitin kula da ayyukan a karkashin hukumarmu.
“Dangane da tallafin sallah ga marayu, yanzu haka muna shirye-shirye dan mika bukatar hakan ga maigirma Gwamna, wanda ina kyautata zaton zai yi na’am da shawarwarin”.
Dakta ya ce hannu daya baya daukar jinka, dan haka ya jawo hankalin masu hannu da shuni da kungiyoyi masu zaman Kansu da su cigaba da kokarinsu na tallafawa masu rauni, wanda hakan zai taimaka wajen yaye damuwa ga wanda aka barwa kewar rashi ko kasawa ta rayuwa.