Daga Muhammad Shafi’u Saleh, Yola
Kimanin magidanta 41,000 aka bayyana cewa za su amfana da tallafin irin shuka a yankin kananan hukumomi tara da matsalar boko haram ta shafa a Adamawa.
Shugaban wata kungiyar habaka harkokin noma da abinci ta kasa (FAO) Ahmadou Diop, ya bayyana haka a yayin kaddamar da rabon irin shukan a garin Fufore, inda ya ce shirin wani mataki ne shawokan matsalolin yunwa da karancin abinci a yankin kananan hukumomin bakwai.
Ya ce kungiyar da hadin gwiwar ma’aikatar noma ta tarayya sun gabatar da wani shirin tantance mutane kimanin miliyan biyar da suka fi fuskantar matsalar yunwa a jihohin Borno, Yobe da Adamawa.
“Gabadaya shirin na shawokan matsalar karancin abinci da abinci mai gina jiki ga al’ummar da abun ya shafa ne, a arewa maso gabas domin bunkasa harkokin noma. Kananan hukumomin da za su amfana sun hada da Fufore, Girei, Gombi, Hong, Madagali, Michika, Mubi ta kudu, Mubi ta arewa da Yola ta kudu”.
Da yake Magana a taron, kwamishinan ma’aikatar noma ta jihar, Ahmad Waziri ya shawarci mutanen da za su amfana da tallafin da suyi amfani da irin hatsin shukin ta yadda ya dace.
Kwamishinan ya bayyana cewa an zabi kaddamar da shirin a garin Fufore ne bisa la’akari da yawan ‘yan gudun hijira da ke zaune a Unguwanni a jihar.
Da yake Magana a madadin mutanen da suka amfana Malam Idris Adamu, ya godewa kungiyar bisa tallafin irin shukin da ta basu, ya kuma yi alkarin za su yi amfani da shi ta yadda ya dace.