Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home RAHOTANNI

RAHOTO: Makomar Alkalai A Turkiyya Bayan Yunkurin Juyin Mulki

by Tayo Adelaja
June 21, 2017
in RAHOTANNI
3 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Jibril Abdullahi Zaria

Tare da fatan edita yana lafiya, ina son ya taimaka ya dan ba ni dama a wannan jaridar mai farin jini don na yi tsokaci a kan al’amuran da ke faruwa a kasar Turkiya jim kadan bayan juyin mulkin da wasu sojoji suka kuduri aniyar yi a bara. Na sha karanta ra’ayoyin jama’a da dama a wannan kafa, hakan ce ta sanya ni ma na nemi a ba ni na dan tofa nawa albarkacin bakin.

Kamar yadda na yi nazari, na fahimci cewa a ci gaba da fafatawa tsakanin mahukuntan kasar Trukiyya da magoya bayan Malamin addinin Musuluncin nan da ke a yanzu yake zaman gudun hijira a kasar Amurka, wato Fethullah Gulen, sakamako ya nuna cewa hukumomin kasar a wannan makon, wato ranar Talatar nan ta kara sallamar Alkalai da ma’aikatan Shari’ah da dama bisa zarginsu da hannu dumu-dumu a yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a ranar 15 ga Yulin bara.

Kafafen yada labarai da dama tun daga na kasar, har ma da na kasashen waje, suna ci gaba da dora alaun tambaya kan yadda ake kokarin sa idanu a kan ‘yan jarida da kuma wasu jami’ai.  Amma manazarta na ci gaba da dora manyan tambayoyi da har yanzu aka kasa fahimta, mene ne dalilin da ya sanya ake yakar bangare daya kawai? Me ya sa hukumomin kasar ta Turkiyya suka dora karar-tsana a kan fitaccen Malamin kasar, Fethullah Gulen? Wasu daga cikin rahotannin na cikin gida sun tabbatar da cewa rikicin tsakanin Shugaba Erdogan da Sheikh Gulen ba ya rasa nasaba da siyasa. A cewar rahotannin, Gulen yana daga cikin fitattun mutanen da suka taka muhimmiyar rawa wajen ba wa Shugaba Erdogan goyon bayan samun shiga gidan sarautar kasar, amma daga bisani, wasu ‘yan ba-ni-na-iya suka shiga tsakani, wanda hakan ta tilasta wa Sheikh Fethullah barin kasar tasa ta gado, ya koma cikin kasar Amurka, inda a yanzu yake zaman gudun hijira.

Fethullah dai, kamar yadda rahotanni daga kafafen yada labarai na duniya suke nuni fitaccen malami ne da ya shafi shekaru da dama yana yin kira ga al’ummar Musulmi da su rika yin koyi da tafarkin rayuwar fiyayyen halittu Annabi Muhammad (SAW). Muhimmin sakonnin yake aikawa a ko’ina a duniya shi ne, Musulmi shi ne kadai tsayayyen mutumin da zai iya tabbatar da zaman lafiya a doron kasa, ta hanyar ayyuka nagari, yin riko da sunnonin Manzo (SAW). A mafi yawan rubuce-rubucensa, Sheikh Gulen ya fi mayar da hankali kan yadda ake bata sunan addinin Musulunci musamman a yanzu da duniya ke kokarin danganta wasu gungiyoyin ta’addanci da Islam. A mafi yawan ra’ayoyin malamin, yana koyar da tsantsan zama a matsayin masu neman ilmi da aiki da shi.

An dai ce malamin kusan ya fi kowa magoya baya daga ‘yan kasarsa, a ciki da wajen kasar ta Turkiyya, wanda a halin yanzu ya bude cibiyoyin koyar da ilmin addinin Islama a Nahiyoyi da dama, ciki, har da Afrika da mafi yawan kasashen na kasashen na Afrika, har ma da Nijeriya a ciki. Baya ga wannan ya kasance a kan gaba wajen yada manufar addini ta hanyar rubuce-rubucen littattafan da a yau ake fassara su zuwa yaruka sama da 60 na Afrika.

Faruwar yunkurin juyin mulkin nan, Sheikh Gulen yana da cikin sahun gaba na wadanda suka fito suka soki lamirin yunkurin da sojoji suka nemi a Turkiyya. Kana kuma ya yi kira da babbar murya ga hukumomin kasar tasa da su gaggauta gudanar da binciken gano wadanda suke hannu a cikin a bin da ya fassara da bakar aniyarsu. Ya kara da cewa a daidai lokacin da duniya ke ci gaba da kurbar madarar dimokuradiyya, bai ga amfanin sojoji marasa kishin kasa ba, da har za su fito suna kokarin maida kasar baya ba.

Jim kadan bayan dukkanin sakonnin nan da Sheikh Gulen yake aikewa zuwa ga mahukunta kasar tasa ta Turkiyya, sai ga shi a rana tsaka kallo ya nemi komawa sama, a lokacin da Shugaban Kasar Recep Erdogan ya bayyana Sheikh Gulen da cibiyarsa  ta ‘Hizmet’ a matsayin daya daga cikin wadanda suka shirya yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba. Jin haka, kamar yadda na karanta a wasu daga cikin manyan jaridun kasashen Turai da Amurka, Sheikh Gulen ya fito ya karyata zancen na Shugaba Erdogan. Kana kuma ya kara jaddada manufarsa, sannan ya nesanta kansa da cibiyarsa ta Hizmet daga abin da shugaban na Turkiyya ya bayyana.

Irin haka na ci gaba da faruwa a kasar, wanda a yanzu dukkanin kungiyoyin da ke cikin kasar da ma na kasar waje suna ta kiraye-kiraye ga gwamnatin kasar da ta sassauta wa wadanda ba su ji ba, ba su kuma gani ba.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Kasashen Waje: Sallah: Al’ummar Nijar Sun Koka Da Tsadar Kayayyaki

Next Post

Kungiyoyi Da Kulob-Kulob: Bunkasa Kasuwanci: ‘Yan Kasuwar ‘SCC Jere Junction’ Sun Bayyana Kudurinsu

RelatedPosts

Kayan Marmari

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Yi Gyara A Kan Tsarin Makarantun Islamiyya

by Sulaiman Ibrahim
1 day ago
0

Daga Sagir Abubakar Katsina Majalissar zartarwa ta Jihar Katsina ta...

Korar Ma’aikata A Kaduna Ta Kara Jefa Jama’a Mawuyacin Hali – Isah Ashiru

Korar Ma’aikata A Kaduna Ta Kara Jefa Jama’a Mawuyacin Hali – Isah Ashiru

by Sulaiman Ibrahim
1 day ago
0

Daga Abubakar Abba, Kaduna Dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna karkashin...

Babandede Ya Yi Gargadi A Kan Daukan Aiki Na Bogi Da Sunan NIS

Sauye-sauye Masu Ma’ana A Sashen Fasfo Na Hukumar Shige Da Ficen Nijeriya

by Yahuzajere
3 days ago
0

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya (NIS), karkashin...

Next Post

Kungiyoyi Da Kulob-Kulob: Bunkasa Kasuwanci: ‘Yan Kasuwar ‘SCC Jere Junction’ Sun Bayyana Kudurinsu

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version