RAHOTO: Rikicin Makarantar Kangere: Ba Mu Yarda Da Kalaman Kakakin ‘Yan Sanda Ba —NANS

Daga Khalid I. Ibrahim, Bauchi

Kungiyar dalibai ta kasa ta bayyana cewa mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, SP Haruna Muhammad ya sharara karya kan rikicin da ya auku a tsakanin sojoji da kuma daliban Kwalejin koyon aikin Malanta ta Kangere da ke Bauchi a ranar 24 ga watan Mayun 2017 da ta gabata.

Kungiyar ta bayyana cewar sam akwai kura-kurai a cikin rahoton da sojoji da kuma ‘yan sanda suka fitar kan rikicin, Mataimakin Shugaban kungiyar daliban na kasa (National Association of Nigerian Students), Kwaramared Shattima Umar ne ya bayyana hakan a ganawarsa da ‘yan jarida a Sakatariyar NUJ ta Bauchi a makon jiya.

Kwamared Shattima ya bayyana yadda lamarin ya samo asali, “mun je makarantar da nufin za a yi zabe, zuwanmu ke da wuya na yi mamaki da na ga sojoji a wajen, da ni da mutanena sai muka ce kila domin su bayar da tsaro ne kawai.

Da muka tambayi shugaban makarantar, sai ya ce za a daga zabe, muka shaida masa cewar eh mun amince, amma ta wacce hanya ne za a bayyana wa daliban cewar an daga wannan. Tun kafin a sanar kawai sai ma’aikata suka je suka daga akwatin zaben, su kuma dalibai suka ce ba su yarda ba, nan take sai sojoji suka zo suka yi harbi har sau biyar a sama, sai dalibai suka ce su sam ba su yarda ba. Suka je kan hanya suka tare, nan sai ga motocin sojoji, suka yi harbi suka harbi dalibai tara 9 a gabanmu. Akwai wanda suka harba a ido, wani a kirji da sauran wurare.”

Shugaban daliban ya ci gaba da bayyana cewa abin takaici kuma sai ga shi jami’an tsaron sun fitar da wasu rahotonni akasin abin da ya wakana, “muka zo da safe sai muka ga sanarwar Kakakin ‘yan sanda, SP Haruna Muhammad ya fitar da sanarwa yana cewa kawai ta’addanci “CRIMINAL CONSPIRACY”da tada hankalin jama’a daga daliban, kuma ya boye wa jama’a cewa yaran nan harbinsu aka yi, sai ya nuna sun ji ciwo ne. Da muka ji haka sai muka tashi mu je wajen Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda muka yi masa bayanin ga fa abin da wannan ya fada, me ke faruwa?”

Ya ci gaba da cewa, “sai Mataimakin Kwamishinan ya ce mana shi a takaice ma bai san ma ya yi ba; muka duba location dinsa a facebook sai muka samu yana ma Lagos a wannan lokacin da ya rubuta wannan abin”.

Daliban sun kuma kara da cewa, su ma sojoji sai ga shi sun sharara tasu, “washe gari kuma sai muka sake ganin Darakta na hulda da jama’a na sojoji ya yi nasa rubutun, shi ma yana cewa ba a yi ma harbi a cikin makarantar ba. Wai yara ne suka je suka yi rigimarsu kawai suka ji ciwo. Tabbas mun ga lokacin soja daya ya ji ciwo, amma ba mu san ina ya je ya ji ciwonsa ba. Sannan kuma muka sake ganin sojojin sun sanya a fejinsu na Twitter wai kafin su zo dalibai sun ji wa kansu ciwo.”

Shattima Umar ya bayyana cewar ba su san a wane dalili ne ake boye gaskiyar lamarin abin da ya faru a makarantar Kangere ba. Ya ce, da bukatar a yi bayanin gaskiyar abin da ya faru.

Da yake magana kan daliban da sojojin suka kama suka mika ga ‘yan sanda a yayin artabun kuwa, Shugaban ya bayyana cewa shi da kansa ya je ya yi belin daliban, yanzu haka babu wasu dalibai a hannun jami’an tsaro. “Dalibai ne wadanda suka fita neman ‘yancinsu a lokacin da ake abin, su 32 mun kuma je da ni da sauran muka yi belinsu,” in ji shi.

 

Exit mobile version