RAHOTO: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Horas Da Jami’anta Kan Sanin Makama Aiki A Bauchi

Daga Khalid I. Ibrahim, Bauchi

 

A ranar Litinin da ta gabata ne Shalkwatan Rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta shirya wani taron bita da koyar da jami’anta dabarun dakile aiyukan assha da kuma basu horo kan ilimin gudanar da aiki da hanyoyin shawo kan matsalolin da suke fuskanta.

Taron horaswar a kuma kunshi taya shugaban rundunar ‘yan sanda na kasar, Babban Sufeta Idris murnar cikarsa shekara daya bisa jagorancin hukumar ‘yan sandan Nijeriya inda aka yi bayanin wasu daga cikin nasarorin da ya iya cimmawa kawo yau.

Bangarorin tsaro na soja, hukumar kula da shige da fice, ma’aikatan kula da gidajen yari da dai sauran bangarori na tsaro dukkaninsu sun samu halartar wannan taron na wuni guda.

Jimkadan bayan kammala taron, Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Bauchi Garba Baba Umar ya yi wa manema labaru karin haske kan wannan taron inda ya ce sun shirya taron ne domin taya shugabnsu murnar cika shekara guda a bisa shugabancin rundunar, a bisa haka suka kuma zabi maudu’in domin baiwa jami’ansu horo kan tafiyar da aiki daidai da zamani da kuma dabaru na asali.

“Duniya a yanzu aikin dan sanda ya canza, ba a yin aikin dan sanda ba tare da al’ummomi ba. Jawo al’ummomi a jiki shi ne zai ba ka dama ka yi aikinka na dan sanda yanda ya kamata. Sannan akwai wasu dokoki da hakkokin jama’a da ya kamata a ce ‘yan sanda sun sani suna kuma yin aiki da shi. A bisa haka muka shirya wannan taron domin bayar da horo ga jami’anmu”.

Ya kara da cewa tabbas wannan taron zai bada natija sosai wajen cigabantar da aiyukansu yanda ya dace, “Yaranmu za su gane cewar idan an kawo kara wajen ‘yan sanda da basu iya bincike ba, za a kai kotu sai ka ji wai kotu kuma ta watsar da kara. A bisa irin wannan mun nuna wa jami’anmu hanyoyi da dabarun da ya kamata su rika bi, domin su ma akwai kurakuran da suke yi. Sai muka nuna musu ga yanda za su yi kaza da kaza ga abubuwan da za su gyara da sauransu. Ga abun da za ka yi ga hujjojinka a bisa haka ne za ka samu nasara a kan kes dinka”. In ji kwamishinan.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Bauchi ya bayyana cewar babbar nasarar da shi ya iya cimmawa a Jihar Bauchi ya iya kokari wajen magance aiyukan ‘yan ta’adda da suka hada da ‘yan sara-suka, da kuma ‘yan kungiyar asiri, da uwa uba ‘yan siyasa masu daure musu wajen yin aiyuknsu na ta’addanci.

Shi kuwa mataimakin shugaban kwamitin kulla alaka tsakanin ‘yan sanda da al’umma na yankin Arewa Sanusi Maijama’a Ajiya ya bayyana wa ‘yan jarida cewa “Duk mai kishin kasa da son kasa ta ci gaba to wajibi ne ya baiwa ‘yan sanda hadin kai. Domin ba karamin sadaukarwa ba ne yau a ce ka samu kanka kana aikin dan sanda”.

Ya bayyana cewar koya wa jama’a yanda ya kamata su yi wajen taimaka wa ‘yan sanda da kuma su yanda ‘yan sandan za su yi wajen taimaka wa jama’a abun ne mai matukar muhimmanci a irin wannan lokacin.

“Kwamitinmu ta yi matukar nasara sosai, duk wani ka ji an kama dan ta’adda mu ne muke ba da labarin inda suke da abun da suke, muna taimakawa wajen nemo inda suke da kuma ba da bayanin inda suke”. In ji sa

Dallatun Bauchi ya bayyana cewar kalubalen da suke fuskanta a halin yanzu shi ne na rashin ba da bayani da kuma tsoron da jama’a ke yi wajen bada rahoto wa ‘yan sanda a cewarsa hakan bai dace ba, “Muna ba wa jama’a horo domin shawo kan wannan matsalar, dole ne mu baiwa ‘yan sanda hadin kai babu wanda za yi dan sanda ya yi maka aiki bai sanka ba”.

LEADERSHIP Hausa ta rawaito cewar sama da ‘yan sanda dari biyar ne suka samu wannan horon daga ofishoshin ‘yan sanda daban-daban na cikin garin Bauchi. An kuma gabatar da laccoci da makaloli a wajen taron.

Exit mobile version