Daga Muhammad Awwal Umar, Minna
Mai martaba Sarkin Kagara, Alhaji Salihu Tanko ya nemi ‘yan siyasa da su daina amfani da matasa wajen tada zaune tsaye a kasar nan, domin matasan su ne shugabannin gobe.
Sarkin ya yi wannan kiran ne a fadarsa bayan saukowa daga sallar Idi karama ranar Lahadin makon jiya. Alhaji Salihu Tanko ya ce zaman lafiya shi ne babban jigon cigaba a kasa, saboda kasa ba ta taba samun ci gaba sai kowane bangare na al’umma sun yarda su zauna lafiya da juna.
Da ya juya kan manoma da makiyaya kuwa mai martaba sarkin wanda ya kwashe shekaru talatin da biyar kan karagar mulki a masarautar ya ce, “kasar Kagara kasa ce wadda Allah Ya azurta ta a kan noma da kiwo, don haka ya zama wajibi makiyaya da manoma su fahimci anfanin zaman tare da juna su nemi kowace irin hanya ce da za ta iya samar da zaman lafiya a tsakaninsu, dan haka manoma da makiyayi ‘yan uwan juna ne bai kyautu a bari ana samun ‘yan kananan soki-burutsu na tasowa a tsakaninsu ba, dole su kauda bambance-bambancen da ke tsakaninsu wajen samar da zaman lafiya a tsakaninsu ta haka ne kawai za su iya anfana da muradun gwamnati na dawo da martabar noma da kiwo a kasar nan”.
A wani bangaren kuma, shugaban Karamar Hukumar Rafi kuma shugaban majalisar shugabannin kananan hukumomin Jihar Neja (ALGON), Hon. Muhammad Gambo Bojo a wata ziyara da dagattan kasar Kagara suka kai masa, ya jawo hankalinsu da cewar su Iyayen kasa ne kuma Iyayen al’umma ne ya zama wajibi su tashi tsaye wajen fadawa shugabanni ‘yan siyasa gaskiya a duk lokacin da suka ga ana kokarin kaucewa hanya.
Hon. Bojo ya ce su daina tunanin cewar dokar kasa ta baiwa shugaban karamar hukuma karfi a kansu wajibinsu ne su fito su rika ba da shawarwari ga shugabanni, “da haka ne gwamnati za ta iya samun nasarar isar da muradunta ga al’ummar kasa. Yanzu babban aikin da ke gaban karamar hukuma shi ne kirkiro kasuwanni a inda ake bukatar hakan dan samun hanyoyin karin samun kudin shiga kamar a garin Maikujeri da sauran sassan da suka kamata, saukar da wutan lantarki wanda hakan ne zai iya ba da damar bunkasa kananan kasuwanci a yankunan karkara”.
Ya kuma ce “dangane da tsaro, gwamnatin Jihar Neja ta taka rawar gani kwarai musamman wajen inganta tsaro a yankin, domin ta inganta jami’an tsaro da kayan aiki, kan haka ita kanta karamar hukuma ba ta yi kasa a gwiwa ba ta kara kaimi wajen hada kai da jami’an tsaron soja, ‘yan sanda da ‘yan banga wajen zakolu bata-gari da masu fakewa a cikin al’umma da munanan manufa”. Haka bai samun nasara sai an samar wa al’umma walwala da jin dadi dan karamar hukuma ta kara kaimi wajen samar da abubuwan more rayuwa ga al’ummar yankin wanda hakan zai baiwa kowa damar cin moriyar gwamnati na inganta rayuwar ‘yan kasa na gari.
Dan haka Hon. Gambo Bojo ya jawo hankalin matasa da su daina barin ana anfani da su wajen ruguza rayuwarsu, “duk wanda ya baka makami da nufin yaki da wani lallai ba masoyin ka ba ne, ya zama wajibi matasa su yiwa kansu karatun ta natsu, su dawo da martabarsu ta yadda za su iya zama masu dogaro da kansu wajen kirkiro abubuwan da za su iya moriyarsa da kuma kasa, wanda hakan zai iya zama silar karyewar duk wani mai tunanin bullo da abubuwa da yake tunanin zai iya ruguza su”.
A na shi bangare, Hakimin Kusharki kuma Katukan Kagara, Alhaji Aliyu Muhammad Kusharki ya yabawa gwamnatin Alhaji Abubakar Sadik Sani Bello wajen ceto rayuwar al’umma daga hannu bata gari, Hakimin ya ce yanzu a gundumarsa kawai abin da gwamnatin Neja ta yi abin a yaba ne, “samar da jami’an soja wajen fatattakar bata gari a duk cikin sako da lungu na yankunan karkara abin a yaba ne. Kuma yanzu haka ayyukan raya kasa da gwamnatin Neja ta yi a masarautar Kagara idan ba ta zama ta daya a cikin masarautun Neja to lallai tana kan gaba sosai”. Sai ya nemi duk wani mai rike da sarautar gargajiya da siyasa da su yi mai yiwuwa tare da sanya kishi wajen hada hannu dan kawo abubuwan ci gaba a masarautar Kagara. Inda ya kara da cewa “Lallai samun dattijo mai tsoron Allah a matsayin sarki abin a yaba ne, dan wannan shi ne alamar samun nasara a wannan masarauta”. In ji shi.