Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano
An bayyana ciyarwa a azumin da Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ke yi da cewa abin a yaba ne kwarai da gaske.
Wannan jawabi ya fito daga bakin shugaban Majalisar Mahaddata Alkur’ani reshen Jihar Kano, Gwani Sunusi Abubakar a lokacin da tawagar manema labarai ta ziyarci tsangayarsa wadda ke cikin cibiyoyin da Gwamnatin Ganduje ke samar da abincin buda baki ga al’umma.
Gwani Sunusi Abubakar ya ci gaba da cewa “mu majalisar Mahaddata Alkur’ani reshen Jihar Kano muna godiya kwarai bisa samar da irin wadanan cibiyoyi da ake samar da abinci domin amfanin masu bukata. Halin da ake ciki ya tsananta kwarai, domin magidanta da yawa ne ke zuwa domin karbar nasu abinci, haka kuma muna aikawa ga tsangayu da kuma masallatai da wuraren zaman jama’a domin sa albarka ga wannan aikin alhairi da Gwamna Ganduje ke aiwatarwa”.
Saboda haka ya bukaci Alarammomi a Jihar Kano da su ci gaba da sa wannan gwamnati cikin addu’o’in a wannan wata mai albarka.
Jama’ar da wakilinu ya samu zantawa da su sun bayyana godiya tare da yabawa da irin abincin da ake dafawa a wannan cibiya, inda suka ce ko shakka babu abincin ya kai duk yadda ake bukata “muna yiwa Gwamna Ganduje addu’ar fatan dorewa da wannan aikin alhairi”.