Daga Na’ima Abubakar, Kano
An bayyana shirin rundunar ‘yan sandan Jihar Kano na ‘Operation Dan Halak ka fasa’ da cewar abin a yaba ne.Wasu fitattun al’ummar garin Shekar Barde dake Karamar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano ne suka yi wannan yabo a lokacin gudanar da addu’o’in godiya ga Allah bisa samun nasarar da jami’an rundunar ‘yan sandan Jihar Kano masu kula da ofishin rundunar dake garin Sheka, karkashin babban Jami’i mai kula da wannan ofishin.
Al’ummar sun godewa jami’in ‘yan sanda mai kula da yankin, Alhaji Nasir Haruna Gusau, wanda ake ganin shi ne mafi karancin shekaru cikin sa’aninsa wadanda ke rike da irin wannan mukami.Haka kuma an jijinawa kokarinsa bisa jajircewa na ganin bata garin dake neman zamewa al’ummar wannan yanki kadangaren bakin tulu sun zama tarihi.
Al’ummar Sheka na fama da matsalar ‘yan kwanta-kwanta, shaye-shaye da kuma matsalar Daba,amma zuwan wannan jami’i ‘yan sanda tare da hadin gwiwar iyayen kasa cikin kankanen lokaci jama’ar wannan unguwa sun koma barci har da saleba. Saboda haka jama’ar wannan gari suka bayyana gamsuwa tare da rokon Allah ya ci gaba da taimakon rundunar ‘yan sandan Jihar Kano.
Da wakiliyarmu ta bukaci jin ta bakin baturen ‘yan sanda, sai yace ba abinda zai ce, domin yin hakan na cikin umarnin mai girma Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano, saboda haka a ganinsa wannan wani aiki ne da ya wajaba akansa kawai yake yi.