Asusun Tallafa wa Noma na kasa da kasa, wato IFAD, ya nuna bacin ransa a cikin sabon rahotonsa na dala biliyan 10 a matsayin asusu na shekara-shekara ga kananan manoma daga rabin dalar Amurka tiriliyan a karon farko daga shekarar 2017 zuwa shwkarar 2018.
Dangane da rahoton da IFAD da shirin manufofin sauyin yanayi suka fitar, CPI, kashi 1.7 cikin 100 na kudaden yanayi, kadan daga abin da ake bukata ke zuwa ga kananan manoma a kasashe masu tasowa.
Rahoton ya kuma koka da cewa duk da rashin dacewar kananan manoma ga tasirin tasirin sauyin yanayi, inda rahoton ya karanta a wani bangare, yin nazarin gibin kudldaden da aka kebewa yanayi na kanana manoma, inda rahoton ya kara da cewa, bincike na farko game da kudadwn na yanayi ga kananan manoman, sunyi kadan matuka.
An fito da shi ne a lokacin wani Babban Taro inda wakilan bankunan Bunkasa Jama’a na duniya su 450 ke haduwa a karon farko don tattaunawa kan yadda za a sake juya akalar kudaden don tallafawa yanayin duniya da burin ci gaba.
Shugaban, IFAD, Gilbert Houngbo, ya yi kira da a kara mai da hankali kan kananan manoma masu samar da abincin duniya amma sun fi fuskantar sauyin yanayi, don haka ya kamata su samu damar samun kudaden canjin yanayi.
Houngbo ya ce: “Ba abin yarda ba ne cewa mutanen da ke samar da yawancin abincin duniya, kuma wadanda ke cikin mafi girman jinkai na karuwar yanayin da ba za a iya hangowa ba, sun sami karamin tallafi”.
Ya kara da cewa, kananan manoma da ke zaune a filaye mara iyaka suna kan gaba na canjin yanayi kuma ya kamata su sami damar samun kudin canjin yanayi da suke bukata don daidaita nomansu.
Har ila yau Manajan Darakta na Duniya, CPI, Dokta Barbara Buchner ya ce, “Abubuwan da muka gano sun nuna cewa kananan kaso na kudin da aka saka a cikin aikin sauyin yanayi a duniya ne ke kan hanyarsa ga kananan manoma”.
Ya yi nuni da cewa, “Wannan rashin kudi na iya haifar da mummunan sakamako, saboda kananan manoma cikin gaggawa suna bukatar karin tallafi don ci gaba da rayuwarsu ta fuskar canjin yanayi.”
A cewar sanarwar, kananan manoma a halin yanzu suna samar da kashi 50 cikin 100 na adadin abincin abinci na duniya, inda ya ci gaba da cewa, yanayin zafi mai karfi tare da yawan fari da ambaliyar ruwa suna lalata amfanin gona da dabbobi kuma yana sanya musu wahala ci gaba da ciyar da al’ummominsu da samun abin masarufi.
A cewarsa, “Duk da cewa babu wadatattun alkaluma game da abin da kananan manoma ke biyan kudin sauyin yanayi, kiyasta daban-daban na bukatunsu gaba daya, inda ya kara da cewa, kasance ne a cikin daruruwan biliyoyi duk shekara, wanda hakan ke ba da alamar irin girman saka hannun jarin da ake bukata.”
A shekara mai zuwa za ta kaddamar da wani shirin noma mai suna ASAP +, wanda ya kasance wani tsarin samar da kudi na sauyin yanayi wanda aka yi tunanin zai zama babban asusu wanda aka kebe don tura kudin yanayi ga kananan masana’antun don taimaka musu daidaitawa da canjin yanayi da yaki da yunwa da rashin abinci mai gina jiki.
Har ila yau shirin na ASAP + ya ginu ne akan shirin hukumar ta IFAD kuma babban shirin daidaita yanayin duniya ga kananan manoma, wanda tuni ya bada sama da dala miliyan 300 ga sama da manoma miliyan biiyar a kasashe 41.