Connect with us

LABARAI

Rahoton Jaridar Ingila: ISIS Na Shigo Da ’Yan Ta’adda Nijeriya Daga Siriya

Published

on

Shugabannin kungiyar ‘yan ta’adda na “Islamic State”, suna shigo da mayaka masu tsatsauran ra’ayi daga kasar Siriya zuwa Nijeriya domin shirin kaiwa kasar Birtaniya hari, wata jaridar kasar Birtaniya mai suna “The Sun” ce ta ruwaito wannan labarin ranar Litnin.
A na tura masu tsatsauran ra’ayi da ‘yan Boko Haram zuwa yankin Gabas ta Tsakiya don a horas dasu a wani shiri na musayar fasaha, inji Jaridar.
Jaridar ta ruwaito cewa, ana matukar tsoron cewa, alakar dake a tsakanin kasar Nijeriya dana Birtaniya zai sa lamarin ya yi matukar sauki ga kungiyar ISIS ta samu tura makasa zuwa kasar Birtaniya domin aikata ta’asar data shirya gabatarwa na kisa da ta’addanci.
Jaridar ta kuma lura da cewa, fiye da sojojin kasar Birtaniya 150 ke cikin shirin hadaka da yakwarorinsu na Nijeriya domin shirya yadda zasu katse hanzarin wadannan masu mugun nufin, da kikarin hana kugiya IS kafa sansani mai karfi a yankin Afirika ta yamma.
A wani wajen horarwa a garin Kaduna na Arewacin Nijeriya, wani babban soja mayakan sama, ya bayyana cewa, masu tsatsaura ra’ayi na daukan darussa daga kungiyar IS bayan sun mika musu bai’a, musamman ba’iar da suke mikawa ga bakar tutar nan na kungiyar IS.
Group Captain Isaac Subi, dan shekara 46, ya dade yana yaki da ta’addanci a fadin yankin Afirika tun daga shekarar 1991, ya ce, “Suna shigowa kasar nan don horas da mayakansu a nan haka kuma ‘ya ta’adda daga cikin Nijeriya na samun daman shiga kasar Yemen da Syria kara samun kwarewa daga bisani sais u dawo su ci gaba koyar da juna, suna da wannan shirin ga mayakansu na dukkan bangaren.” Rahoton ya kuma kara da cewa, alakar ‘yan ta’addan ya kai ga wasu mummunar hare hare da aka kai a kasar Birtaniya a lokuttan baya, ya kuma bayar da misali da, daba wa jama’a wuka da akan titin Landa da wani mai suna Fusilier Lee Rigby a shekarar 2013, da kuma hare haren ta’addanci da Michael Adebolajo da Michael Adebowale dukkansu ‘yan asalin Nijeriya suka kai birnin Landa a lokutta daban daban.
Ana da fargabar cewa, kungiyar ta Is yata yi amfani da zirga zirgan jirgin sama tsakanin Legas da Landan wajen safarar ‘yan ta’adda zuwa Birtaniya domin aikata mugun shirin nasu. Subi ya kuma kara bayyanawa Jaridar Sun, cewa, rashin ingantaccen tsaro a iyakokin kasashe a yankin Afirika ya sanya ana samun sauki wajennyada harkar zubar da jinni da ta’addanci a yankin na Afirika, harkokin ta’addancin na kuma kawo tashin hankali da asarar rayukan jama’a.”
A cikin shekara 4 da suka wuce an kashe fiye da mutum 20,000 a yankin Arewa ,maso Gabas, an kuma kiyasta cewa, a kwai ‘yan ta’adda fiye da 3,000 a yankin gaba daya.
Wasu jama’a fiye da Miliyan 2 sun tsere daga zubar da jinin dake aukuwa a yankin na Gabas ta Tsakiya, wasu kuma da aka kama ana matsa musu yi wa ‘yan ta’addan yaki, matan kuma da aka kama ana tilasta musu zama matan ‘yan ta’addan.
Mai ba kasar Birtaniya shawarar a kan harkar tsaro a Abuja, Brig. Charles Calder, ya ce, kungiyar IS babbar barazana ce ga kaddarori da harkokin kasar Birtaniya a duk inda suke a duniya.
“Idan ba a yi maganin matsalar ‘yan ta’addan ba, a dan lokaci mai zuwa zasu zama babbar barazana da kaddarori da harkokin kasar Birtaniya a dukkan fadin duniya.”
Calder ya kara da cewa, aika sakonni da tsinto kwararrun daga cikin sojoji da horas dasu ne hanya mafi inganci na kare Nijeriya daga wargajewa, ya kuma kara da cewa, a halin yanzu sojojin kasar Birtaniya sun horas da sojojin Nijeriya fiye da 35,000, ya ce, a halin yanzu kuma an fahimci sojojin Nijeriya na aiki tare da bajinta a sassa daba daban na duniya.
Kokarin jin ta bakin jami’in watsa labarai na rundunar tsaron Nijeriya, Brig. Gen. John Agim, ya ci tira, anan son a ji ra’ayinsa ne a kan barazanar da kungiyar IS keyi wa kasar Birtaniya.
Amma a wata tattaunawa da Mista Agim, ya yi da wakilinmu ranar Laraba data gabata,ya amince da bayanin cewa, rundunar sojoji na sane cewa, wasu hare haren da ake kai wa a kasar nan ‘yan kasashen waje ke kai wa saboda rashin kyakyawar tsaroa iyakokinmu.”
“Muna sane da cewa, wasu masu kai hare haren a yankin Arewa maso gabas ba ‘yan Nijeriya bane, ana shigo dasu ne saboda tunanin zasu samu kudi.”
“Wadanda ake shigo dasu, ana shigo dasu domin samun kudade ne. watakila ka faifan bidion dake nuna wasu ‘yan ta’adda daga kasashen Nijar da Chadi suna rokon a daukesu aikin zuwa Nijeriya yin ta’addancin, abinn lura shi ne wasu mutane dake neman aikin yi a shirye suke su zama makamin duk wanda ya shirya amfani dasu.
“babban matsalar ita ce, wasu mutanen da basu da aikin yi na a shirye ga duk mai son amfani dasu a kann dukmaikin da yake son yin amfani dasu, abin takaicin kuma shi ne iyakokinmu a bude suke,” inji Agim.
Da aka tambaye shi abin da hukumar shige da fice “Nigeria Immigration Serbice” take yi don inganta tsaro a iyakokin kasar nan, jami’in watsa labaran hukumar Mista Sunday James, ya ce, an inganta tsaro a iyakokin kasar nan saboda tabbatar da cewa, “babu wani dabn kasan waje da aka bari ya shigo kasar nan ta kowanne hanya, ta kasa ne ko ta sama ko ta ruwa ba tare da an tantance shi ba.”
Ya kuma kara da cewa, jami’an hukumar na kara himma wajen sauknauyin aikinsu, “Ana iya ganin haka ne ta yawan mutanen da hukumar tamu suka kama a ‘yan tsakanin nan, rundunar mu ta “Special Border Patrol Corps” sun samu horo na musamman domin gudanar da aiyyukansu.” James ya shawarci ‘yan Nijeriya su kai rahoton duk wani ko wata kungiyar da basu gane take takensu don a dauki matakin daya dace.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: