Rahoton Kai Hari A Jami’ar Abuja Zuki-tamalle Ce, In Ji ‘Yan Sanda  

Kai Hari

Daga Idris Aliyu Daudawa,

Rundunar ‘yan sanda ta Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT)ta bayyana cewa rahoton da ake ta yayatawa wai ‘yan ta’adda sun kai hari a Jami’ar Abuja ba komai ba ne illa zuki-tamalle.

Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan ta babban birnin tarayya, ASP Mariam Yusuf  wadda ta bayyana hakan a cikin wata sanarwar da ta fitar ta ce shi wannan bayanin ya biyo bayan wasu rahotanni da aka buga ta wasu sassan kafofin sadarwa na sada zumunta ne cewa ‘yan bindiga sun kai wa jami’ar hari.

Sanarwar ta kara da bayanin, “Rundunar tana kira ga al’umma cewa su yi watsi da sakon da ake yadawa a wasu sassan kafafen sada zumunta na zamani da ke ikirarin cewa‘yan bindiga sun kai wa ‘Jami’ar Abuja hari.”

Ta ci gaba da bayanin cewa“Muna so mu bayyana karara cewa babu wani al’amarin kai hari wanda ya faru ranar Talata a Jami’ar ta Abuja.

 

“Don haka ana shawartar jama’a da su yi watsi da sakon wanda ba kawai batanci ba ne, abu ne da yake nufin haifar da tashin hankali a tsakanin mazauna babban birnin tarayya,” kamar yadda ta ce.

Haka nan Mariam ta ce kwamishinan ‘yan sanda (CP) mai kula da babban birnin tarayya, Mista Bala Ciroma ya ba da umarnin yin sintiri ba tare dawani bata lokaci ba, na kewaya makarantun da suke yankin.

 

Mariam ta yi kira ga mazauna birnin su kasance masu bin doka, su kuma kwantar da hankulansu, da kuma bin diddikin duk wani labarin da suka ji, kada a samu rudani da tashin hankali tsakanin al’umma.

Ta  kara jaddada cewa ita rundunar koda wanne lokaci a shirye take wajen kare rayukan mutane da dukiyoyinsu.

Tayi kira da mazauna babban birnin duk wanda ya ga wani abinda yake jin zai iya samar da matsala yana iya sanar da rundunar ta wadannan nambobin wayar kamar haka08032003913, 08061581938, 07057337653, da kuma 08028940883.

Exit mobile version