Rahoton Karya Da Adrian Zenz Ya Watsa Ya Tona Asirin Amurka
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rahoton Karya Da Adrian Zenz Ya Watsa Ya Tona Asirin Amurka

byCMG Hausa
3 years ago
Zenz

Wata doka mai suna wai hana tilastawa ‘yan Uygur aiki ta Amurka za ta fara aiki nan bada jimawa ba.

Kwanan nan, Adrian Zenz, wanda ya sha kitsa karairayi ya sake fitar da wani rahoton dake nuna cewa, wai kasar Sin na kara tilastawa mutane aiki. Irin wannan doka tana cike da karairayi, wadda ta tona asirin kasar Amurka, na kawar da Xinjiang daga cikin yankuna masu samar da kayayyaki ga duniya.

Hakika, kafofin watsa labarai sun ruwaito maganganun tsoffin ‘yan diflomasiyyar Amurka a kasar Sin dake cewa, babu wata matsala a Xinjiang, dukkanmu mun sani, amma yin amfani da jihar Xinjiang don rura wutar rikici kan batutuwan da suka shafi tilasta yin aiki, da kisan kare-dangi, da kuma keta hakkin dan Adam, dabara ce ta tsunduma gwamnatin kasar Sin cikin mummunan mawuyacin hali.

Rahoton karya da Adrian Zenz ya fitar a wannan karo, yana cewa, wai duk da cewa shaidun da za’a iya amfani ba su da yawa, amma sabon ci gaban da ake samu, ya sa ake kara tilastawa mutane aiki, har zuwa wasu sana’o’in fasahohin zamani. Amma rahoton bai fayyace wane sabon ci gaba ba ne, kana bai bayyana shaidu da wasu alkaluma ba, illa karya ce zalla kawai.

A karshen bara, gwamnatin Amurka ta sa hannu kan wani shirin doka mai suna wai “hana tilastawa ‘yan Uygur aiki”, wanda za’a fara amfani da ita tun daga ranar 21 ga watan Yunin bana. Dokar za ta hana Amurka shigo da hajojin Xinjiang. Wato ta hanyar fakewa da batun hakkin dan Adam, wannan doka za ta hana ci gaban Xinjiang, da kwace damar samun bunkasuwa na mazauna yankin, kuma wannan take keta hakkin dan Adam ne a Xinjiang.

Kusan makwanni biyu da suka wuce, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yi jawabi kan manufofin gwamnatin Amurka game da kasar Sin, inda ya ambaci wasu muhimman kalmomi uku da suka hada da, zuba jari, kulla kawance, da yin takara.

Bisa fahimtar Amurka, yin takara shi ne matsa lamba ga abokan takara ta hanyar shafa musu bakin fenti, da kuma keta ka’idojin kasuwancin kasa da kasa, to, abin da mutum ya shuka, shi zai girba. (Murtala Zhang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?
Daga Birnin Sin

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
Next Post
Sin Ta Sake Neman Amurka Da Ta Bayyana Yadda Take Girmama Yarjejeniyar Haramta Makamai Masu Guba

Sin Ta Sake Neman Amurka Da Ta Bayyana Yadda Take Girmama Yarjejeniyar Haramta Makamai Masu Guba

LABARAI MASU NASABA

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version