Rahoton Karya Da Kasar Amurka Ta Tsara

Daga CRI Hausa,

A ranar 27 ga watan da muke ciki, ofishin darekta mai kula da aikin leken asiri na kasar Amurka ya gabatar da wani rahoto dangane da aikin binciken gano asalin cutar COVID-19.

Cikin wannan rahoton da hukumar leken asiri ta kasar Amurka ta gabatar, ba a samu gabatar da shaida ko da guda daya ba, wadda za ta nuna asalin cutar COVID-19.

A cikin wannan rahoto, an fi yin amfani da kalmomi irinsu “mai yiwuwa”, da “watakila”. A cewar wasu ‘yan Amurka masu yin amfani da yanar gizo ta Internet, rohoton nan ba kome ba ne, illa ma dai takardu shara masu kunshe da maganar banza.

Kafin kasar Amurka ta kaddamar da aikin binciken gano asalin cutar COVID-19 a wannan karo, fadar White House ta kasar Amurka ta taba bayyana cewa, samun cutar COVID-19 daga muhallin halittu, ko kuma samun ta daga cikin dakunan gwajin halittu, ba a tabbatar da cewa wanne ne ya fi yiwuwa ba.

Amma bayan wasu watanni 3, kasar na ci gaba da daukar wannan ra’ayi ba tare da samun wani ci gaba ba.

An ce kasar Amurka ta yi kokarin yayata ra’ayin “samun bullar cutar COVID-19 daga dakin gwajin halittu dake birnin Wuhan na kasar Sin” ne domin karkatar da hankalin mutanen duniya, ta yadda ba za su lura da tarihin samun matsalar bullar cuta a dakunan gwajin halittu na kasar Amurka ba. Kana an samu shaida a cikin rahoton da hukumar leken asiri ta kasar Amurka ta gabatar, da za ta tabbatar da gaskiyar ikirarin.

Ko da ya ke rahoton cike yake da kalmomin rashin tabbas, amma an tabbatar da batu guda daya, wato kwayar cutar COVID-19 ba wani makami na halittu da aka tsara ba ne, kana kusan ba zai yiwu ba a samu kwayar cutar ta hanyar jirgita kwayoyin halittu.

Sai dai me ya sa kasar Amurka ta iya tabbatar da batun?

Idan mun yi la’akari da yadda ake karin tuhumar kasar Amurka a fannin fara samun bullar cutar COVID-19, za mu fahimci niyyar hukumar leken asiri ta Amurka.

Yanzu fiye da mutane miliyan 25 na kasashe daban daban sun yi kira da a gudanar da bincike kan cibiyar nazarin fasahohin halittu ta Fort Detrick ta kasar Amurka, kana dakin gwajin halittu na Ralph Baric na kasar shi ma ya janyo tuhuma sosai.

A nata bangaren, kasar Amurka na son wanke kanta daga tuhumar da aka yi mata, ta hanyar gabatar da wannan rahoto dangane da binciken gano asalin cutar COVID-19, maimakon ba da damar gudanar da wani cikakken bincike a wadannan wuraren da aka ambata, ta yadda za a bayyanawa mutanen duniya ainihin abun da ya faru.

Har ila yau, Amurka na ci gaba da kokarin shafa wa kasar Sin kashin kaza, inda ta ce wai kasar Sin na son boye wasu bayanai, abin da ya sa ba ta samu wani sakamako mai gamsawa a aikin binciken asalin cutar COVID-19 ba.

Amma hakika kwararrun hukumar lafiya ta duniya WHO sun riga sun gudanar da cikakken bincike a birnin Wuhan na kasar Sin, inda suka samu hira da mutanen da suke son gani, da binciken dukkan bayanan da suke son dubawa.

Yanzu ya kamata kasar Amurka ita ma ta ba da dama domin a yi bincike a gidanta, ta yadda za a kawar da tuhuma daga zukatan mutanen duniya. (Bello Wang)

Exit mobile version