RAHOTON MUSAMMAN: Machina: Masarautar Da Ta Hada Zumunta Tsakanin Mutane Da Macizai

Daga Muhammad Maitela, Damaturu

Machina, gari ne mai muhimman dadaddun wuraren tarihi wanda masana suka ce an kafa masarautar yankin a wuraren shekarar 980 ta miladiyya.

Tarihi ya nuna cewa wani mafarauci mai suna Bolo Kandira ne ya assasa shi. Haka kuma duk da kasancewar Machina a tsakiyar sahara bai hana Turawa ‘yan mulkin mallaka baje kolinsu a garin ba.

Machina ita ce cibiyar Karamar Hukumar Machina da ke Jihar Yobe, gari ne wanda tazarar nisan sa ta doshi kilo mita 300, a kusurwar arewa maso-yamma daga Damaturu, babban birnin Jihar Yobe, kana wadda ke kan iyaka da jamhuriyar Nijer.

Masarautar Machina ce kadai za ka samu a cikin ‘’ya’yanta harda maciji wanda tarihi ya tabbatar da cewa sun fito ciki guda (‘yan-biyu) da sarki Mai Idrissa a can baya. Gari mai ango da amaryar da suka koma manyan duwatsu, gari a tsakiyar sahara kuma zagaye da duwatsu, shimfide a kan falalen dutsin da ya sa daukacin garin babu rijiyar kankare ko burtsatse; har sai bayan ka yi tafiya mai tazarar kusan kilo mita bakwai. Gari ne wanda ya shahara da fararen dawakai 12 na musamman a fagen hawan-daba.

A cikin wata ziyarar musamman da wakilinmu na Jihar Yobe ya kai a masarautar, ya tattauna da Sarkin Machina, Mai Alhaji Bashir Al-Bishir Bukar (OON). Sarkin ya yi cikakken bayani kan alakar masarautar da maciji tare da sauran batutuwa masu ban ta’ajibi inda ya fara da cewan “Abu na farko dai shi ne ba a kashe maciji a Machina saboda maciji dan uwan haihuwar mu ne na jini, maciji dan sarkin Machina ne. Bisa ga wannan, duk wanda ya kashe maciji a wannan garin to ya tabbatar dan sarki kuma dan uwamu ya kashe”. In ji Mai Machina

Ya kara da cewa “bisa ga yadda yake a tarihin wannan masarautar shi ne, akawai lokaci wanda matar Mai Machina na wancan lokacin ta haifi ‘yan-biyu; daya mutum (Mai Idrissa) dayan kuma maciji. Yayin da bayan macijin ya dauki kwanuka tare da mahaifiyar su sai ya mazaya zuwa cikin duwatsun da ke kusa da gidan sarki. Bisa wannan dalilin, yadda mutum yake hayayyafar ‘’ya’ya da jikoki, haka shi ma wannan maciji dan sarki ya haifi ‘’ya’ya da jikoki, kuma ‘ya’yan sa da jikokin sa ‘yan’uwanmu ne. Sannan kuma ba su cutar da kowa a wannan garin kuma matukar ka ga maciji ya cutar da mutum a Machina, to shi mutum din ne ya yi kokarin cutar da shi. Saboda haka maciji dan uwan mu ne na jini wanda muka fito ciki guda “.

A wani batu na daban kuma, Mai Machina ya nusar da cewa haka wannan alaka da zamuntar  ta kasance tare da gudana a tsakanin ‘ya’yan dan sarki maciji da bangaren su a cikin kowanne irin lamarin rayuwar yau da kullum. Yayin da ya ce lokacin da wani abin farin ciki ko na bikin ciki ya samu masarautar ko na damuwa, za ka tarar da macizan manyansu da kananansu suna ta kai kawo a cikin fada. Tare da karin haske da cewa wani sa’in macizan kan hau har bisa karagar sa lokacin da ake zaman fada, “babu mamaki kafin ka bar nan ka ga sun zo nan har a kan wannan karagar da nake zaune ko su rinka zagayawa sannan daga bisani su tafi abin su”. Ya bayyana.

Sarkin Machina ya sake bayyana cewa, “kafin wannan lokaci na yaduwar ilimin addinin musulunci tare da sabbin al’amurran ci gaba na zamani wadanda suka yi yawa, wannan ya jawo abubuwa sun dan ci baya Idan an kwatanta da can baya da muke ware wasu muhimman raneku domin bukukuwan kulawa da su ta hanyar gudanar da yanke-yanke da abinci (gumba) da nonon shanu mu kai mu aje inda suke. To amma duk da wannan, bai hana mu ci gaba da basu kulawa ta musamman ba, a can inda suke zaune ko idan sun shigo nan fada”. Mai Machina.

Mai Martaba Mai Machina ya sake bayyana cewa kowanne lokaci su kan yiwa jama’ar da suka bakunci garin gargadin kada wanda yayi kokarin cutar da maciji, gudun abin da zai zo ya komo.

Mai Bashir Al-Bashir Bukar ya sake bayyana cewa, wani muhimmin abu wanda garin ya kara fito da sunan Machina shi ne yadda ta shahara wajen raya al’adun gargajiya a ciki da wajen kasar nan. Masarautar kan shirya kasaitaccen bikin daba ko shiga gasa, yayin da kuma masarautar ce ke zuwa matsayi na daya. Inda ya ce a bikin nuna al’adun gargajiya wanda ya gudana a bana, su ne suka zo na farko a wannan shekara.

“Sannan kamar yadda kowa ya sani ne, muna da fararen dawakai 12 wadanda kowanne lokaci da su muke hawan-daba. Duk inda muka je ko wani ya wakilci Machina a hawan-daba; karamar daba ce ko babba. Akwai bambanci tsakanin hawan-daba babba da karama-karamar akalla tana da dawakai 24, yayin da babbar tana da adadin dawakai 90 zuwa 100, to amma dai ko wacce ce, za ka tarar muna da fararen dawakai 12, sannan kuma wannan shi ne alamar da za ka gane cewa Machina tana wajen”.

Mai Machina, Alhaji Bashir Al-Bashir ya bayyana yadda masarautar Machina take da kyakkawar alakar zamantakewa da sauran masarautu a Jihar Yobe dama makwabtan ta da jamhuriyar Nijar wadda ke makwabtaka da su. Inda ya kada baki ya cen “gaskiya ko yaushe kokarin mu shi ne kyakkawar alakar mu da sauran masarautu da muke wuri guda sannan sai wadanda muke makwabtaka da su na sauran jihohi kana da makwabtan mu na Nijar, yanayin da har ya zama kamar ‘yan’uwa na jini, kuma ya jawo duk wani biki ko zaruffan yau da kullum su kan gayyace mu muma mu gayyace su, sannan da huldar kasuwanci mai karfi tsakanin mu”.

Alhaji Mai Bashir al-Bishir ya jadadda cewa, a matsayin sa na kwararre a fannin halayyar dan adam, kwararren malamin makaranta wanda ya samu horon malanta tun daga matakin farko zuwa digirin-digirgir, “wannan ya taimaka min wajen sanin yadda ya kamata in jagoranci al’ummar wannan masarauta cikin nasara. Alhamdulillah muna bin kowacce hanya wajen tabbatar dorewar zaman lafiya a tsakanin al’ummar wannan masarauta tare da jin koke-koken jama’a cikin kowanne lokaci, ina gida ko na fita waje, ba na sakewa wajen sauraren shawarwari da koke-koken jama’ar da nake jagoranta, kowanne lokaci kofa ta a bube take ga kowa”.

Mai Martaba Mai Machina ya sake bayyana matukar jindadin sa dangane da kokarin Gwamnatin Jihar Yobe wajen gina hanyar garin daga Nguru zuwa Machina, sannan da shirin gina sabuwar hanyar bunkasa yankunan sahara wadda ta taso tun daga Gaidam zuwa garin. Inda ya ce, “al’ummar wannan yanki namu cike suke da murna da farin cikin shimfida wadannan hanyoyin da suke kunshe da alhairai, sabanin can baya da muke jin kamar an manta da wannan yanki namu, yanzu an sada mu da manyan birane masu ci gaba”. In ji shi.

“A can baya, kafin Gwamnatin Jihar Yobe a karkashin wannan mulki na Alhaji Ibrahim Gaidam, ba kowanne ma’aikaci ne ke murna idan an tura shi Machina aiki, da dama sun dauki garin kamar kurkuku da har sai wanda yayi babban laifi ake turo muna! Saboda yadda hanyar ba tada kyau wanda sai an sha wahalar gaske. Amma yanzu wannan ya kau, mun kasance kamar kowanne gari ko birni”.

Asali da kuma tarihin da garin yake da shi musamman kan alakar dan sarki maciji da mutane abubuwa ne da idan aka mayar da hankali wajen watsa su a duniya ta kafafen yada labarai za su janyo hankulan masu yawon bude ido daga sassa daban-daban na duniya.

 

 

Exit mobile version