Idris Umar" />

Rahoton Musamman: Wa Ya Kashe Aisha Sunusi? 

A cikin satin da ya gabace mu ne wasu, wadanda ba a san su ba, su ka kashe wata matar aure ’yar shekara 18, kisan gilla, a wata anguwa da a ke kira Sabon Garin Bomo da ke kasar Bomo a karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna.

Wakiln LEADERSHIP A YAU ya binciki yadda lamarin ya faru, kamar yadda mijin marigayiyar ya shaida ma sa a yayin da ya ke gudanar da binciken kwakwaf kan lamarin.

Danjuma Mai Kayan Miya shi ne mijin matar da a ka yi wa kisan gillar; ya ce, a ranar Juma’a da safe  ne bayan ya fita zuwa kasuwa wajen da ya ke gudanar da sana’arsa ta sayar da kayan miya, sai matar tasa, Aisha, ta kira shi a waya cewa, ta na son ta sha garin rogo, sai ya ce, to zai sayo ma ta.

Danjuma ya ce, “kafin komawata na tsaya na yi aski, kafin na kai ma ta abinda ta bukata.” Ya cigaba da cewa, ya na Isa kofar gidan sai ya ga kofar a bude, ba kamar yadda ya saba bari ba.

Danjuma ya ce, ganin haka ne ya sa ya dan ji wani abu a zuciyarsa, amma sai ya yi ma ta sallama, kamar yadda ya saba duk lokacin da ya dawo, amma ya ji shiru.

Ya ce, “Ina shiga falo, sai ban gan ta ba, amma sai na ji ta yi nishi mai karfin gaske a cikin uwar dakinmu. Hakan ya sa na yi sauri na shiga cikin dakin.”

Danjuma ya ce, ya na shiga, sai ya ga matar tasa a kwance cikin jini, ga raunuka a kanta munana. Hakan ya sa shi fita da gudu, don neman gudunmawar jama’a.

Nan take ya samo jama’a su ka zo cikin gidan su ka ga matar rai ga hannun Allah. Hakan ya sa a ka yi gaggawar kai ta asibiti, don ceto ranta. Bayan kai Aisha asibiti ne ba jimawa, sai rai ya yi halinsa.

Binciken da LEADERSHP A YAU ta gudanar ya nuna cewa, wadanda su ka aikata wannan ta’addancin sun yi abinsu ne da rana-tsaka misalin karfe 2-3 na rana, yayin da jama’ar unguwar kowa ya tafi masallaci sallar Juma’a.

Malam Yusuf Adam, wanda shi ne mai iunguwar da lamarin ya faru, ya tabbatarwa da wakilinmu faruwar lamarin, kuma ya ce, “gaskiya ba mu ji dadin faruwar wannan lamari ba, don wacce a ka kashe da mijinta mu na zaune lafiya da su; babu wata matsala tsakaninsu da jama’ar gari. Don haka ne ma a halin yanzu an dukufa da addu’o’i da nufin Allah ya gaggauta tona asirin wadanda su ka yi wannan ta’addancin. Kuma ya yi fatan Allah ya jikan ta da gafara kuma Allah ya bayar da kariya ga sauran matan da ke gidajensu.

LEADERSHIP A YAU ta nemi jin ta bakin ofishin ‘yan sandan shiyyar da lamarin ya faru, inda su ka tabbatar da faruwar lamarin, amma su ka ce ba za su ce komai ba, saboda ka’idar aikinsu, amma su na cigaba da bincike a kan lamarin.

Aisha Zailani makociyar Marigayiya Aisha Sunusi ce. Ita ce ta tabbatar da jin ihun wacce a ka kashen din, kuma har ta  kawo dauki, amma sai ta ji kofar gidansu a kulle. Don haka sai ta koma da nufin cewa ba wata matsala ba ce.

Sai bayan wasu lokuta ta ji a na cewa, ga abinda ya faru ga makociyarta Aisha. Ita ma ta yi kuka tare da nemawa kawar tata rahama.

Bincike ya kara tabbatar  da cewa, wacce a ka kashen din ba ta jima da auren Danjuma ba. Yanzu watansu takwas zuwa tara kenan da yin auren, kuma ma a na zaton marigayiyar ta na dauke da juna-biyu kafin a yi ma ta kisan gillar.

Shi Danjuma mazaunin unguwar Mangorori Hayin Dogo Samaru a karamar hukumar Sabon Gari jihar Kaduna ne. Ita kuma matar tasa, wacce a ka kashe ‘yar asalin garin Zariya ce cikin birni unguwar Limamcin Kona a jihar ta Kaduna.

Zuwa hada wannan labarin jama’a ne ke yin dafifi a gidan iyayen Aisha Sanusi da ke Zariya da gidan mijin nata, don yin ta’aziyya tare da addu’ar Allah ya tona asirin wanda ya yi ko ya sa a ka yi wannan ta’addanci.

Abin tausayi da jimami ga wannan lamari shi ne, a ranar da za a kawo marigayiyar dakin mijinta a matsayin amarya, mahaifinta ne ya sanya ta a motarsa ya kawo ta dakin mijinta da kanda, inda sai daga bisani kawaye da dangi su ka biyo baya.

Haka nan kuma a wannan lokacin da Matashiya Aisha Sanusi ta rasu mahaifinta ne ya kara dora ta a motar da ya kawo ta dakin mijin nata zuwa kabarinta, saboda gayar kauna da ke tsakaninsu, wanda hakan ya tayarwa da jama’a hankali a yayin da su ka fahimci hakan.

Exit mobile version