Mataimakin Shugaban Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya shaida wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, cewa, mafi yawan ’yan Nijeriya sun amshi tallafin da Gwamnatin Tarayya ke bayarwa, don rage radadin da annobar Cutar Korona ya haifar a kasar.
A ranar Talata ne, Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya amshi sabon rahoton farfado da tattalin arziki, wanda mataimakin Kasa Yemi Osinbajo yake jagoranta a fadarsa da ke Abuja.
A cikin kalaman mashawarcin Osinbajo, Laolu Akande, ya bayyana cewa, wannan shi ne farkon taron a hukumance da kwamitin ya gudanar a wannan shekara.
A shekarar 2020, Buhari ya aiwatar da kwamitin farfado da tattalin arziki wanda ya nada Osinbajo a matsayin wanda zai jagoranci kwamitin, an dai aiwatar da wannan kwamitin ne domin ceto da tattalin arziki wanda cutar Korona ta durkusar.
“A karkashin shirin kananan kasuwanci, mutane 277,628 suka ci moriyar shirin, inda aka farfado da kananan kasuwanci guda 56,575 wajen samar musu da jari.
“Wadannan yawan mutane sun hada da zangon farko na mutum 20,614 sun sami kudaden tallafi a watan Oktoba, yayin da zango na biyu suka sami kudaden tallafin a tsakanin watan Nuwamba da Disamba.
“Bayanin shirin ya nuna cewa, wadanda suka ci moriyar shirin mutum 257,014, kowannan su ya sami naira 30,000 daga cikin zango na farko, yayin da zango na biyu wadanda suka samu kudaden a tsakanin watan Nuwaamba zuwa Disamba daga cikin mutum 222,466 wadanda suka amfana da shirin, kowannan su ya sami naira 50,000 tare da mutum 34,548 wanda ake biyan albashi a tsakanin watan Nuwamba da Disamba.
“Kashi uku daga cikin yawan mutanen da suka amfana da shirin suna da bukatoci na musammam, yayin da kashi 43 na wadanda suka ci moriyar shirin dukkan su mata ne,” in ji shi.
Mataimakin shugaban kasa ya bayyana cewa, har yanzu ana samun karuwar wadanda suka amfana da shiri a bangaren sufuri wanda aka kaddamar da watan Disamba. Ya kara da cewa, mutum 333,000 masu gudanar da kananan kasuwanci suka amfana da naira 30,000 ga kowanninsu wanda yanzu haka suna ci gaba da gudanar da harkokin kasuwancinsu cikin kwanciyar hankali. Osinbajo ya bayyana jihohin da suka cin gajiyar shirin kamar haka, Babban Birnin Tarayya da Legas da Ondo da Kaduna da Borno da Kano da Anambra da Abiya da Bauchi da Filato, wadannan su suka fara cin moriyar shirin a zango na farko. Sauran sun hada da Taraba da Bayelsa da Edo da Ogun da Kwara da Inugu da Ebonyi da Adamawa da Ekiti da Katsina da Kebbi da kuma Kogi, wadannan su suka ci moriyar shirin a zango na biyu. Haka kuma, Akwa-Ibom da Yobe da Sokoto da Nasarawa da Naje da Imo da Oyo da Osun da Jigawa da Kroos Ribas da Zamfara da Benuwe da kuma Gombe, wadannan su shuka zo a zango na uku.
A cewar Osinbajo, shirin samar da wutar lantarki ta hasken rana zai samar wa gidage miliyan biyar wutar lantarki a yankunan karkara ya fara aiki.
“A halin yanzu dai, an kashe naira biliyan 140 a bangaren shirin samar da wutar lantarki daga hasken rana da zai haskaka gidaje miliyan biyar, a cikin wadanda za su amfana sun hada da mutanen yankunan karkara da mutanen burane, wanda tuni wadanda suka fara gudanar da harkokin masana’antu da wannan wutar lantarki da aka samu daga hesken rana karkashin shirin farfado da tattalin arziki,” in ji shi.