Raino Da Tarbiyya: Hakkin Maza A Kan Rainon ‘Ya’yansu?

08094233473 rakiyabamalli@gmail.com

Babu shakka maza na da hakki a kan raino da tarbiyar ‘ya’yansu, kai har ma da kula da matansu tun daga lokacin da ta dauki ciki har zuwa haihuwa ta hanyoyi da dama misali:

Abinci

Asibiti

Ayyukan gida da sauran su (kafin haihuwa).

Bari mu dan yi tsokaci a kan wadannan abubuwa kamar haka: Hakkin maigida ne ya tabbatar cewa, da zarar mata ta samu juna biyu, to dole fa abincin da za ta ci ya canza, domin a wannan lokaci tana bukatar abinci ne wanda zai kara mata lafiya ya kuma kare ta daga wasu cututtuka, ba wai kuma an ce dole ne sai maigida ya kashe wasu kudade masu yawa don ganin ta samu irin wannan abinci ba, a’a idan ya kawo kadan ma ya wadatar.

Maigida ya tabbatar da cewa, uwargida ko mai dauke da juna biyu tana samu tana cin kwai ko da kuwa sau daya ne a sati. Haka nan lemon zaki, shi ma na da matukar amfani ga mai ciki, shi ma tana iya sha  ko da sau daya ne a sati. Sannan ta rika cin ganye kamar, alayyahu, zogale, ugu da kuma shuwaka a kai-kai, domin yin hakan zai kara mata lafiya da samun isasshen jini a jiki. Kazalika jariri ko jaririyar za ta samu cikakkiyar lafiya a jikinta ko jikinsa.

Haka zalika, a bangaren asibiti, wannan ma al’amari ne mai matukar muhimmanci a wajen mace mai dauke da juna biyu, wadanda maigida ya kamata ya tabbatar an je an yi ragista a asibiti da wuri, domin kuwa yin hakan zai taimaka wajen sanin lafiyarta da na abinda take dauke da shi ta yadda za ta rika kula da kanta har zuwa lokacin da za ta haihu da kuma sanin yadda za ta rika kula da cikin nata.

Sauran hidimoni da suka shafi kula da gida kuma, wannan ma wasu abubuwa ne wadanda maigida ya kamata ya sanya idonu a kai sosai har ma da hannu, wato kada ya sakar wa uwargida ita kadai. Maigida na iya taimakawa uwargida da wanke kayanta, shara da wanke-wanke da sauran abubuwan da suka dace mussaman a inda babu mai taimaka mata. Yin hakan zai kara shakuwa da kauna da kuma dankon soyayya a tsakanin maigida da uwargida.

A fitowa ta gaba za mu duba abubuwan da maigida ya kamata ya taimakawa uwargida da su bayan Allah Ya sauke ta lafiya, don haka sai a biyo mu a mako na gaba. Da fatan maza ko masu gida za su ci gaba da ba mu hadin kai don samun kyakkyawar tarbiyya a gidajenmu da kuma ‘ya’yanmu a duk inda suka samu kansu.

Exit mobile version