Raino Da Tarbiyya: Masomin Gini Daga Tushe

SADIYA GARBA YAKASAI 08023622757 E-mail: sadiyagarbayks@gmail.com

Assalamu alaikum jama`a, kamar yadda aka sani akwai mai gabatar da wannan shafi Malama Rakiya Bamalli wacce ta yi kokari wurin dora arsashin fadakarwa a kan raino da tarbiyyar ‘ya’yanmu, amma a halin yanzu na sha damarar karbar ta saboda wasu uzurori da suka yi mata yawa. Sai dai duk da haka, lokaci zuwa lokaci za ta rika shigowa filin domin cigaba da ba da gudunmawa.

Idan ba a manta ba, mun kirkiri wannan fili domin mu dada fadakar da iyaye musamman iyaye mata domin su saka ido akan tarbiyyar yaran su yadda tarbiyya yanzu ta tabarbare, tilas sai iyaye sun saka idanu akan rayuwar yaransu. Iyaye mata yanzu tarbiyya ta koma hannun mu mata saboda, namiji shi ba mazauni ba ne dole, uwa ita ce za ta ja ragamar rayuwar ‘ya’yanta.

A yadda zamani yanzu ya juya, dole sai da kwaba ya kamata a ce uwa ta san irin rayuwar da yaranta suke yi, saboda a yanzu babu yaro, duk abin da uwa ta dora danta da shi zai tashi. Ya kamata ta san da irin yaran da ‘ya’yanta suke mu’amala, walau namiji ko mace. Dole sai tana bincikar abin da suke a gida ko a waje, da kuma makaranata. Saboda yanzu rayuwar yara ta tabarbare idan namiji ne uwa ta saka ido irin abokan da yake mu’amala da su gudun fadawa tarkon shaye-shaye da ya zama annoba yanzu ga matasa mata da maza.

Yanayin rayuwar yanzu ya zama iyaye ke shakkar ‘ya’yansu ba ‘ya’ya ke shakkar iyaye ba. Duba da yadda karancin tarbiyya ya zama, yawanci ana samun matsalar tarbiyya daga iyaye, dalili iyaye kuwa sun saka san ‘ya’ya a zuciyarsu har ba sa gano irin halin rayuwar da ‘ya’yansu suke ciki ko da a ce wani a waje ya gano wani hali mara kyau da da ke yi, idan ya fada wa iyaye ko yai wa dan fada, maimakon uwa ta gode sai ta nuna bacin ranta cewa an tsangwami danta. Duk yanayin da iyaye suka dora dansu me kyau ko mara kyau to fa dashi zai tashi, saboda haka yana da kyau tun ice yana danyen sa ake tankwasa shi.

Tarbiyya ba abace ta wasa ba, dole sai iyaye sun dage sun sa ido su kuma yarda cewa duniya tana san danka kai kana kinsa. Ita ce damar da za ka gane cewa danka nagari ne ko kuma lalatacce.

Yana da kyau a ce uwa ba ta dora danta a turba mara kyau ba; duba da yanayin rayuwa, duk yadda uwa za ta yi ta nuna wa danta hali na wwarai.

A nan zan dakata zuwa sati nagaba inda zan zaiyyano Raino kansa kafin Tarbiyya. Da fatan za ku ci gaba da bibiyarmu kamar yadda kuka saba. Allah ya kai mu mako mai zuwa da rai da lafiya, amin.

 

Exit mobile version