Daga Rabiu Ali Indabawa,
Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta ce fargabar katse layin wayoyin tarho kan rajistar Lambobin Shaida na Kasa (NIN) ba shi da tushe.
Hkumar ta umarci masu amfani wayoyi da su da su daina fargaba ko jin tsoro game da batun katse masu layi, tana mai cewa wannan batu ne da bashi da tushe.
Daraktan Hulda da Jama’a na NCC, Dakta Ikechukwu Adinde, ya ce bayanin ya zama dole, saboda yawancin masu amfani da layin sun zama cikin rudanin cewa za a’ yanke layinsu saboda rashin rajistar NIN. Ya shawarci jama’a da su yi biris da jita-jitar da ake yadawa a wasu bangarorin kafofin yada labarai, cewa idan mutum bai da rajistar za a rufe layinsa.
A cikin wata sanarwa jiya a Abuja, Adinde ya bayyana cewa dole ne hukumar ta “fitar da wannan bayani domin kawar da tsoron masu yin rajistar da sauran jama’a”. Ya ce yawancin wallafe-wallafen “an gina su ne a kan kuskuren zaton cewa ga kowace hanyar sadarwa ko hanyar hadin SIM, akwai mai rijistar dan’Adam guda daya