Connect with us

NAZARI

Ramadan: Illolin Ruwan Sanyi Guda Takwas

Published

on

Wakilinmu na sashin kiwon lafiya ya zakulo mana wasu daga cikn illolin dake tattare da shan ruwan, ya kamata mutane su fahinta musamman a wannnan lokaci na azumin watan Ramadan da mutane ke gaggawar kwankwadar ruwan sanyi da zaran an yi budi.
1. Tsaida Bugun Zuciya:- bugun zuciya shike gyara dumin jiki da daidaita numfashi to ruwan sanyi yana sa bugun zuciya ya rika raguwa har takai ga tsayawa. Ko kunsan yawancin yan film na kasar indiya da yan ball da boding da wrestling tsayawar bugun zuciya ke ajalinsu kuma bincike ya nuna yawancin shan ruwa mai sanyi yayin da suke aikine yake jawo musu.
2. Lalata Tsarin Kayan Ciki :- shan ruwa mai sanyi yana tattare hanji guri daya sai ya sanya abinci yaki narkewa da wuri hakan kan jawo matsalar hanji, ulcer kenan ko kuma tashin zuciya. Yawancin masu shan ruwan sanyi suna yawan zubda yawu ko tashin zuciya ko saurin kullewar ciki.
3. dauke karfin Jiki :- Duk da cewa shan ruwan sanyi kan sa mutum yaji dadi amma a hankali yana dauke masa darfin jiki sakamakon cewa yayin da ruwan mai sanyi ya shiga jikinsa dole sai naurorin jikin sunyi kokarinsu na ganin sun maida wannan ruwan ya daidaita da dumin jikin hakan yana sa suyi rauni sakamakon kokarin da suke yana wuce haddi. Ko kun lura duk sanda kuka sha ruwan sanyi sai kunji duk jikinku sanyin ya ratsa kaman farkon zazzabi a hankali kuma sai kuji ya daina.
4. Ciwon Makogwaro Da Dakushewar Murya:- Yawan amfani da ruwan sanyi yana lalata jijiyoyin makogwaro har sukai ga basa amfaninsu mai kyau a mai sha yakai shekaru arbain sai ya fara fama da ciwon makogwaro da dakushewar murya ko muryar ta fashe kwatankwacin mashayin taba.
5. Ciwon Hanta Da koda:- dukansu suna bukatar wadataccen ruwa a jikinsu don haka yayin da bawa ya zama yana amfani da ruwa mai sanyi zai zamo su kuma suna cutuwa ta yanda aikinsu zai fara kasa in haka ta samu mutum ya shiga matsala.
6. Busar Da Ruwan Jiki :- Akwai naurori a jikin dan Adam da aikinsu shi ne sadar da ruwa ko ina a jikin mutum ta yadda ko ina na jikinsa zai samu damar motsawa cikin nishadi. To wadannan naurorin sukan yi sanyi sakamakon ruwan sanyi sai su yi rauni gaba daya.
7. Matsalar Ma’aurata :- Wannan abune tabbatacce harga likitocin zamani cewa shan ruwan sanyi yana raunata mazakutar namiji yana kuma busar da mace in mahaifarta nada rauni yana iya hana haihuwa. Yana tsinka maniyyin namiji ya zama yana saurin inzali ko kuma ya rage masa kuzari. Yana dauke ni’imar jiki su zamo basa gamsuwa da juna.
8. Basir Da Ciwon Kai Na Gefe ‘Migraine’:- Shan ruwan sanyi yadda nace muku yana tattare hanji hakan yana kawo mutum ya kasa bayan gida sai ya hadu da basir. Sannan yana kawo ciwon barin kai wanda ake cewa migraine. Shi kuma migraine yana kashe jijiyoyin ido a daina gani sosai in ya yi nisa har hauka yana sawa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: