Yau a kofar gidan Alhajin Allah zai kwankwasa kofa da doka sallama tare da fatan an shiga watan azumin Ramadan lafiya cike da koshin lafiya. Har wala yau a matsayin ka na mutum kuma musulmi wanda ya san muhimmancin tausayi ga masu karamin karfi, kiyaye hakkokin yan uwansa musulmi da yan uwansa na hallita tare da makobtaka.
Na tabbata cewa Alhaji bai manta da hikimar Allah ba wajen yin wasu masu shi wasu kuma maras shi, kana kuma a cikin kowane lokaci da yanayi al’amurra suna gudana cikin yanayin cudanni in cudeka, saboda a yanayin hallitar dan Adam babu mutumin da ya wadatu da kansa, face yana da bukata da aiki wajen sauke nauyin da ya hau kansa wanda ta haka ne zamantakewa mai ma’ana zai gudana.
Watan Ramadan, wata ne mai dimbin alhairai tare da darussa masu yawan gaske wadanda zasu koyar da dan Adam hakikanin rayuwa, kokarin daidaita wasu bambance-bambancen da ke tsakanin mai shi da maras shi; a wannan tsakani na awanni, an zama daya wajen nisantar ci da sha da sauran wasu shagulgula tare da karkatar da ibada ga Allah Madaukakin Sarki. Tare da yin tarayya a abubuwa da dama wadanda suka kebanci ibada da neman kusanci da yardar mahaliccin kowa.
Ayoyi daban-daban a cikin Alkur’anil Kareem Allah ya ambaci falala da albarkokin da wannan watan ya kunsa, ciki har da yi wa al’ummar musulmi alfarmar Lailatul Kadry, daren da dacewa a cikinsa tafi ta wata duba a wajen Allah. Uwa uba kuma, Allah ya bayyana cewa shima Al’kur’ani Maigirma an saukar dashi a wannan wata na Ramadan- Tirkashi, Alhajin Allah ai wannan babbar garabasa ce!
Bugu da kari, azumin Ramadan yana daga cikin manyan shika-shikai a addinin musulumci, wadanda sai sun cika mutum zai samu cikakken lasisin kasancewa musulmi, bari wannan zance, sauran addinan samaniya suma ba a barsu a baya ba dangane da sha’anin watan Ramadan, sannan masana a fannoni da dama sun bayyana muhimancin watan, ballantana kuma duk musulmi kwarai ba zai kasa tabuka abin azo a gani ba tare da aiki tukuru don samun babban rabo a wannan lokaci kwaya daya a shekara.
Ko shakka babu, Alhajin Allah ba zai yi wasa da wannan muhimmiyar dama ba, saboda na tabbata zai yi iya kokari wajen ganin ya ribaci watan Ramadan wajen sadaukarwa, ciyarwa, ibada da sauran su ba. Alhaji, na tabbata kowace rana a shirye kake wajen ganin ka kula da halin da makobta, yan uwa da sauran mabukata suke ciki a wannan lokaci wanda Allah yake ribanya ladar kowane aiki nagari.
Malamai sun koyar da cewa daga cikin ayyukan ibada mafi soyuwa a gurin Allah babu kamar taimaka wa mabukaci, wannan kuma komai kankantar abinda aka taimaka don Allah, bilhasali lokacin Ramadan, saboda haka, a madadin masu karamin karfi- Alhajin Allah a taimaki yan uwa, makobta, da duk wani maras galihu. Sannan ta la’akari da halin da ake ciki na matsin rayuwa ga talaka, ya dace masu hannu da shuni suna waiwayar mabukata tare da tallafa musu da abinda ya sawwaka.
A hannu guda, akwai fargaba dangane da abubuwan da ke gudana, sabanin shekarun baya, wanda za ka tarar da attajirai da masu abin hannu suna kai komo wajen tanadar abincin buba-baki ga talakawa, a kofar gidajensu ko a bakin masallatanmu da sauran cibiyoyin da jama’a ke taruwa don samun saukin rayuwa, amma halin da ake ciki yanzu abin yana ja baya: ko me ya kawo hakan?
Alhajin Allah, ko a yan shekarun da suka gabata nan baya kadan, an wayi gari suma yan siyasa sun fara kwaikwayon ayyukanku na taimaka wa maras galihu, ta hanyar raba wa talakawa sikari, shinkafa da sauran kayan abinci a lokacin Ramadan, amma kuma abin ya fara ja da baya- yana da kyau a kara zuba wa motar nan taku gas don aci gaba da gashi.
Anya dai Alhaji, jiya kaima na je masallacin da kake sallah, na zauna har bayan Isah’i ban ga motsinka ba, ban hango abin buda bakin da ka tanada wa masallatan da suka saba suna jiranka ba- ko kayi tafiya ne? Ko dai Alhaji an samu canjin yanayi ne, amma kuma idan an daure komai zai wuce, saboda hannu bai bayarwa baya rasa wa.
Bugu da kari kuma, ciyarwa a kowane lokaci abu ne mai kyau kuma aiki ne na jajirtattun mutane masu yantaccen tunani kuma na musamman a cikin kowace al’umma, sannan kuma zababbu ne wadanda basu gajiyawa ko kosawa a fagen bayarwa. Irin wadannan mutane suna da cikakkiyar masaniya tare da imani da cewa Allah ba zai tabar dasu ba, sannan kuma sun san kowane lokaci zasu ci gajiyar abinda suka kyautar.
Arziki da mutane suka mallaka a hannun su, tamkar ajiya ce kuma gwaji ne kan ko zasu iya rike amanar mutanen da suke tare dasu ko yaya. A hannu guda kuma, kyauata da ciyarwa ce fayyace ci gaban dukiya da halascinta tare da samun tabbacin cewa ta Allah ce, akasin hakan kuma Malam ka kirata da kowane suna kuma ka iya dorata a kan kowane ma’auni.
Batu na daban kuma, da ace Alhajin Allah kun dukufa wajen ci gaba da sauke nauyin da ya rataya a bisa wuyanku, da yanzu mun samu sa’ida a wasu matsalolin da muke fuskanta, saboda malamai sun bayyana yadda musifu kan auku ta dalilin rashin fitar da zakka da kyuatata wa mabukata, kana kuma, Allah yana yaye musifu da matsaloli matukar ana yawaita yin sadaka da kyautata wa ga mabukata.
Ramadan Kareem Alhajin Allah!