Ibrahim Ibrahim" />

Ramadan: Sanata Sani Ya Kyautata Wa Al’ummar Mazabarsa

Sanata mai wakiltar al’ummar Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawa, Sanata (Dr.) Malam Uba Sani, ya raba ma jama’ar yankin mazabarsa tallafin kayan abinci har na motar tirela goma, wanda a ke sa ran a kalla sama da Gidaje miliyan biyu zasu amfana da wannan kayan tallafin na abinci, wanda ya kunshi daukacin kananan hukumomi bakwai da ke yankin mazabar Sanatan kaduna ta tsakiya.

kananan hukumomin sun hada da, karamar hukumar Igabi, Giwa, Birnin Gwari, kaduna ta Arewa, Kaduna ta kudu, Chikun da kuma karamar hukumar Kajuru.
A yayin da yake zantawa da manema labarai a lokacin rabon kayan abincin, wakilin Sanata Dakta Uba Sani, Arch Abubakar Rabiu Abubakar, ya bayyana cewa, “A kokarin mai girma Sanata Uba Sani, na ganin a ko da yaushe yana kan gaba wajen kyautata ma Al’ummar sa, musamman abin da yasa ba gudanarwa a duk shekara idan watan azumin Ramadan ya tsaya, a wannan karo ma, Sanata Uba Sani, ya ninka abin tallafin da yake bayarwa saboda irin halin da aka shiga naradadin talauchi a dalilin wannan cuta na korona wanda ta addabi Al’ummar duniya bakidaya.”
Ya kara da bayyana cewa, “Kamar yadda kuke gani ne a gaban ku, Sanata Uba Sani ya kawo motar tirela goma dauke da kayan masarufi daban daban, wanda suka kunshi gyero, shinkafa, da kuma sukari, domin raba ma a kalla mutane miliyan biyu dake yankin kananan hukumomi bakwai dake karkashin mazabar Sanatan kaduna ta tsakiya, domin rage masu irin halin kuncin rayuwar da suka tsinci kansu a ciki, musamman a wannan wata na Ramadan.”
Arch Abubakar ya ci gaba da bayyana cewa, “Baya ga wannan irin taimako da Sanata Uba Sani ya saba a ko da yaushe, Sanatan da kuma sauran takwarorin sa ‘yan Jihar kaduna da ke majalisar tarayya Abuja, karkashin jagorancin Sanata Uba Sani, sun hada kudi har naira miliyan goma 14, domin tallafa ma Gidauniyar yaki da cutar korona karkashin Gwamnatin Jihar Kaduna.
“Sannan a bangare daya kuma, Sanatan da sauran ‘yan uwansa Sanatoci dake majalisa, sun zaftare kasafin rabin albashin su domin bayar da gudunmuwar su ga kwamitin yaki da cutar korona wanda Gwamnatin tarayya ta kafa.”
A yayin da ya ke nasa godiyar a madadin Al’ummar karamar hukumar Giwa, wanda kuma shi ne Shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Giwa, Shehu Gambo Giwa, ya bayyana matukar farin cikin sa da godiyar sa ga Sanata Uba Sani, a bisa wannan tallafin kayan azumi da ya basu.
A cewarsa, wannan ba karamin Namijin kakori ba ne Sanatan ya yi, “Ina mai tabbatar maku cewa, kaf a fadin Jihar kaduna, ba bu wani dan siyasa dake da taimakon Sanata Uba Sani, domin a bayyane take, shi ne kadai mutumin da yau zai taimakeka, gobe ya taimakeka, jibi ya taimakeka batare da ya nuna gajiyawar sa ba, domin shi a bangaren taimako bai san wani abu wai shi gajiyawa ba, domin a kullum bai da wani burin da ya wuce taimakon jama’ar sa.
Shehu Gambo Giwa, a madadin sauran Al’ummar kaduna ta tsakiya ya mika godiyar sa ga Sanata Malam Uba Sani, a bisa kayan tallafin abinci da ya ba su na tirela goma, domin suyi hidimar azumi, su da sauran iyalan su baki daya. Kuma ya tabbatar da cewa damn izinin Allah, za suyi bakin kokarin su na ganin wannan tallafi yaje ga hannun kowa, kamar yadda aka damka masu wannan amana, a cewarsa.

Exit mobile version