Ramadan: Shakikan Buhari Sun Bada Tallafin Tirelan Shinkafa 36 A Bauchi

Daga Khalid Idris Doya,

A kokarinsu na kyautata wa al’umma musamman marasa galihu da suke cikin al’umma a cikin wannan watan mai alfarma na Ramadan, hadakar abokan shugaban kasa Muhammadu Buhari sun rabar da tallafin shinkafa wanda yawansu ya kai cikin Tirelolin mota 36 da aka rabar wa al’umma a Jihar Bauchi.

Shinkafar da suka kunshi buhu mai nauyin 25kg da kuma masu 50kg da yawansu ya kai manyan motoci shake guda 36 ne aka rabar wa al’umma a Bauchi ta cikin shirin kungiyar Baba-Na-Kowa wato ‘Baba For All Initiative’.

Tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Hon. Yakubu Dogara wanda ya kasance mai jan gaba wajen nemo wannan tallafin shi ne ya shaida adadin kayan da aka ware wa Jihar Bauchi lokacin da ke kaddamar da fara rabar da tallafin buhunan shinkafar ga mabukata wanda ya gudana a dakin taro na ‘Double 4 Hall’ da ke Bauchi.

Dogara wanda ya samu wakilcin mambar da ke wakitar mazabar Bauchi a majalisar wakilai ta tarayya, Yakubu Abdullahi, ya ce tallafin an yi ne da zimmar faranta ran al’umman Jihar da kuma taimaka musu a irin wannan yanayin na bukatar hakan da suke ciki musamman idan aka yi la’akari da watan Ramadana da al’ummar Musulmi ke ciki.

Kungiyar ta abokai da makusantan shugaban kasa sun kunshi manoma, ‘yan kasuwa, ‘yan siyasa wadanda suka kasance masu tsananin kauna ga shugaban kasa Buhari da jam’iyyarsa ta APC, sune suka hada tallafin da zimmar rabawa a wasu jihohin kasar nan da Jihar Bauchi ta samu cin gajiyar tirelolin mota 36 daga ciki.

Dogara ya kuma bayyana cewar tallafin na cikin sa’ayinsu na hidimta wa al’umma da tallafa wa marasa shi a cikin al’umma a wannan watan na Ramadan.

Yana mai cewa sun so a ce kowani mai Azumi ya samu abun buda baki da na yin suhur wadatacce, don haka ne suka duba hanyoyin da za su taimaka wa al’umma musamman talaka.

A cewar Dogara, Jihar Bauchi ta kasance jihar Buhari ta biyu bayan Katsina da aka haifesa a ciki wanda ke bata fifiko da muhimmanci a fannoni daban-daban lura da irin soyayya da kauna da jama’an jihar suke wa Buhari tun lokacin da ya shiga siyasa har zuwa yanzu.

“Wadannan tallafin kayan abincin tsohon Kakakin Majalisar tarayya, Yakubu Dogara ne ya yi sa’ayi da kokarin samar wa Jihar Bauchi, kuma ya wakiltani ni da wasu mutum uku a matsayin mambobin kwamtin rabawa ga jama’an da aka yi don su,” Inji Abdullahi Shehu.

Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa, jagoran rabon kuma shugaban dakin da aka ajiye kayan wato Double 4, Hon. Salisu Zakari Ningi, wanda ya ce tabbas wannan shinkafar za ta yi matukar taimaka wa al’ummar Bauchi kuma za a raba ne bisa dacewa ga dukkanin runfunan zaben da suke Bauchi inda za a shiga lunguna da sakuna ana rabarwa ga mabukata.

Ya ce sun yi tsarin da lallai kayan abincin za su shiga hannun wadanda aka bada tallafin domin su, tare da sanya ido wajen rabon.

Ya kuma ce a karin farko za a yi la’akari da masu fama da bukata na musamman (Nakasassu) wajen fara raba musu daga bisani a je zuwa sauran rukinin jama’a.

Daga nan sai ya jinjina wa Dogara bisa jajircewa wajen samu wannan tallafin, ya horesa da ya ci gaba da irin wannan himma da kwazon domin cigaban jiharsa ta haihuwa.

Ya gode wa gidauniyar abokan Buhari a bisa wannan tallafin da suka yi wa jihar Bauchi, ya kuma basu tabbacin yin adalci wajen wannan rabon.

Exit mobile version