Connect with us

LABARAI

Ramadan: Talban Katagum Ya Tallafa Wa Nakasassu 1,342 Da Alarammomi 800

Published

on

Talban Katagum, Dakta Musa Babayo, ya kaddamar da rabon kudi Naira dubu biyar-biyar ga nakasassu sama da dubu 1,342 da kuma tallafa wa alarammomi sama da 800 da kudi da kayan abinci a shiyyar Bauchi ta Arewa, domin sauwaka musu wahalhalun rayuwa lokacin gudanar da azumin watan Ramadana.
Malam Bakari Uba, Sakataren Gudanarwa na ‘Gidauniyar Dakta Musa Babayo Foundation’, shi ne ya shaida wa LEADERSHIP A YAU hakan, inda ya kara da cewa, dukkanin tallafin sun yi ne domin neman yardar Allah tare da sanyaya aminci da kauna a zukutan nakasassun da suke cikin al’umma.
Wadanda su ka ci gajiyar tallafin kudin sun kunshi Guragu, kurame, makafi, kutare da kuma alarammomi da su ka fito daga shiyyar Bauchi ta Arewa (Katagum).
Malam Bakari Uba ya ce, Talban Katagum ya saba duk shekara ya kan tallafa wa masu bukata ta musamman a cikin al’umma.
“Ya saba duk shekara ya kan tallafa wa nakasassu tun daga kan  guragu, kurame, makafi, kutare da kuma alarammomi. Duk shekara a irin wannan lokacin daf shiga watan Ramadana ya kan yi hakan don taimaka wa jama’a.
“Dukkanin wadannan rukunin mutane da su ke fama da nakasa su na da kungiyoyinsu da jerin sunayensu wadanda muka bi su daya-bayan-daya muka basu tallafin nan. Makafin da suka samu tallafin nan a wannan shekarar su 520, Guragu mutum 512, Kurame sama da dari 200, sai kuma Kutare mutum 101ne suka samu tallafin,” a cewarshi.
Ya ci gaba da cewa; “Kowa sai da ya samu naira dubu biyar-biyar kash, kuma gaskiya a nazarinmu tallafin na taimaka musu matuka suna jin dadin hakan. Don da yawansu sun nuna cewa babu mai musu irin wannan gabatar sai shi.”
Bakari Uba ya kuma kara da cewa, baya ga mutane masu bukata ta musamman, Dakta Musa Babayo ya kuma rabar da tallafin kudade da kayyakin abinci ga Alarammomi sama da dari takwas 800 da suke shiyyar Katagum domin su ci gaba da cibiyar da almajiran da suke karkashinsu, inda yake mai cewa sun yi rabiyar ne daidai yawan almajiran mutum daidai yawan abin da zai samu na daga tallafin.
Da ya ke ganawa da wakilinmu ta hanyar rubutun wasika, daya daga cikin Kuramen da suka ci gajiyar tallafin Dayyabu Tanimu Azare, ya nuna gayar godiyarsu da farin ciki a bisa wannan tallafin da suka samu.
“Ina daga cikin kuramen da suka ci gajiyar wannan tallafi mai gayar alfanu a garemu. Na amshi kyautar naira dubu 5,000 daga gidauniyar Dakta Musa Babayo haka sauran ‘yan uwana masu fama da irin wannan lalura suka amsa. Muna amfani da wannan damar wajen gode masa da addu’ar Allah yawaita mana irinsu a cikin al’umma.
“Wannan tallafin watan Ramadan din da ya bamu muna fatan Allah ya biya shi. Ina kuma amfani da wannan damar wajen kira ga masu hannu da shuni da su tallafa wa mabukata a irin wannan lokacin na watan Ramadana. Muna addu’ar Allah kawo mana karshen cutar Korona da ta addabi duniya,” A sakon da Dayyabu Tanimu mai fama da lalurar kurmanci da ya aiko ma na.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: