Kafatin din kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Sergio Ramos zai kauracewa fagen wasa na kusan kwanaki 10 bayan rauni da ya samu a gwuiwar sa a yayin fafatawa tsakanin tawagar kasar Spain da Jamus a gasar cin kofin Nahiyoyi ranar talata da ta gabata.
Kauracewar dan wasa Ramos daga bugawa kungiyar wasa tamkar babban rashi ne ga kungiyar Real Madrid bayan da a wasanta da kungiyar kwallon kafa ta Billareal a ranar asabar a gasar La liga suka tashi 1-1, bayan haka Real Madrid za ta kuma kece raini da kungiyar Inter Milan ranar 25 ga wannan watan da muke cikin sa a gasar cin kofin zakarun turai.
Rashin dan wasa Sergio Ramos a kungiyar yana zama babban gibi saboda tasirinsa a kungiyar ba iya kawai a buga wasa a baya ba, har ma da shugabantar kungiyar da kuma uwa-uba zura kwallo a baya duk da cewa dan wasan baya ne.
Kociyan kungiyar Zidane ya bayyana cewa duk da rashin dan wasan za suyi kokarin ganin sun samu nasara a wasan nasu da Inter Milan kuma akwai ‘yan wasan baya wadanda zasu buga wasa tunda babu Ramos din.