Connect with us

WASANNI

Ramos Ya Kafa Mummunan Tarihi A Gasar Zakarun Turai

Published

on

Dan wasan baya na kungiyar Real Madrid, Sergio Ramos, ya kafa tarihin dan wasan da ya fi kowanne dan wasa karbar katin gargadi (yellow card) a tarihin gasar zakarun turai, bayan da aka bashi katin gargadi a wasan da kungiyarsa ta buga da Roma a ranar Laraba.

Duk da cewa Ramos yana daya daga cikin ‘yan wasan da suka ji dadin gasar zakarun turai a cikin shekaru biyar din da suka gabata, bayan ya taimaka wa Real Madrid ta lashe kofin sau hudu cikin shekaru biyar.

Sannan kuma dan wasan yana daya daga cikin ‘yan wasan da kungiyar take ji da su sosai sakamakon hakanne yasa yanzu shine kyaftin din kungiyar sakamakon dadewa da yayi a kungiyar.

Tun bayan komawarsa Real Madrid daga kungiyar Sebilla, Sergio Ramos ya zama wani jigo a kungiyar, kuma ya lashe kofuna daban-daban a rayuwarsa ciki har da gasar cin kofin duniya da kasar Sipaniya.

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Paul Scholes shi ne wanda yake da katin gargadi (Yellow Card) guda 36 sai Sergio Ramos wanda ya kamo shi a kakar wasan da ta gabata, amma kuma yanzu a wasan da suka buga da Roma, Ramos yanzu yana da guda 37.

Har ila yau Ramos yana da katin gargadin guda 165 a gasar laliga wanda hakan ya sa yanzu shi ma ya fi kowanne dan wasa yawan katin gargadi a gasar ta laliga da a yanzu ake bugawa.

Kocin Real Madrid ya bayyana cewa yana fatan katin ba zai zama barazana ga Ramos ba a kokarin da kungiyar take yi na sake lashe kofin a karo na hudu a jere bayan ta lashe sau uku a jere a lokacin tsohon kocin kungiyar, Zinedine Zidane

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: