Abba Ibrahim Wada" />

Ramos Ya Mayar Da Martani Ga Masu Sukarsa

Mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Sergio Ramos, ya mayarwa da masu sukarsa martini akan abinda yafaru tsakaninsa da dan wasa Muhammad Salah da kuma Lucas Karius.

A wasan karshen da Real Madrid da Liberpool suka fafata na cin kofin zakarun turai a ranar 26 ga watan daya gabata ne dai dan wasa Muhammad Salah yaji ciwo a kafadarsa bayan sunyi wata haduwa da Sergio Ramos.

Haduwar ce kuma tasa dan wasa Salah ya fita daga wasan wanda kuma yakawo nakasu ga yan wasan Liberpool wadanda sukayi rashin nasara daci 3-1 a wasan da aka fafata a kasar Ukraine.

Ramos yace, “Gaskiya mutane basa yi min adalci, sabida yadda ake zuzuta abin bai kai haka ba kuma bai kamata ba saboda duka gaba dayanmu neman kwallo mukaje yi”

Yaci gaba da cewa” mai tsaron ragar Liberpool ma ya bugu a kansa kuma ance laifinane saboda naje mun hadu kuma neman kwallo naje yi”

Ya kara da cewa” yanzu abinda ya rage shine kawai dan wasa Roberto Firmino ya fito yace naji masa ciwo tunda shima munyi wata haduwa dashi kuma yaje kasa tunda mutane basa son gaskiya

 

Exit mobile version