Connect with us

LABARAI

Ranar Arfat: Ganduje Ya Shirya Gagarumin Taro Domin Waraka Daga Annobar Korona

Published

on

Domin koyi da kyakkyawar Tarbiyyar ma’aiki Kan bayanin da ya Yi ta yadda

Allah ya you alkawarin amsa addu’o’i da aka gudanar aranar araft. Gwamnan
Jihar Kano Dakta Abdullah Umar Ganduje ya shirya addu’ a ta musamman inda
aka Tara malamai, limamai da sauran muhimman mutane 360 a fadar Gwamnatin
Kano a ranar Alhamis aka gudanar da addu’o’i ga Jihar Kano da kasa baki
daya domin fatan Allah ya kawo karshen Annobar Korona.

Ya bayyana cewa, “Mun hadu a wannan wuri nee Kan muhimman abubuwa guda
biyu. Dukkanm muna sane da cewa Annobar Korona jarrabawa ce daga Allah.
Munga yadda kasashen da yawa a duniya ke fama da Wannan annoba. Bayanban
kokarin da muke ya zama wajibi mu kara himmatuwa wajen yin addu’o’i domin
neman Allah ya kawar Mana da Wannan annoba.

Hakan zai mataimaka Mana samun taimakon Allah tare da jinkansa domin Kawo
karshen Annobar. Dalilin haduwar anan na biyu shi ne sakamakon matsalar
tsaro da ya addabi makwabtanmu da sauran bangarorin kasarnan, alokacin guda
Kuma ya mu ci gaba da addu’ar fatan Allah ya bi gaba tsare dukkanin
kasarnan daga matsalolin tsaro daya ya addabe su’

Gwamnan ya kuma yi addu’ar fatan Allah magance matsalolin da suka addabi
kudancin Kaduna, Katsina, Zamfara, Sokoto da Jihar Niger da ga matsalar
rashin tsaron da jihohin ke fuskanta.  Tare da rokon Allah ya ci gaba tsare
jihohin mu da kasa baki daya.

Gwamna Ganduje ya bukaci limamai da su ci gaba da jajircewa wajen gudanar
da addu’o’i ga Jihar Kano da kasa Baki daya alokacin sallar idi day kuma
sallar Juma’a.

Ya kara da cewa, yin addu’o’i ya Zama wajibi alokacin da ake kokarin kiyaye
ka’idojin da matakan da jami’an lafiya suka gindaya.

A karshe Gwamna Ganduje ya bukaci jama’a Sue kara lura da matakan kariya
Kamar yadda jami’an lafiya suka tsara.
Advertisement

labarai