Daga Idris Aliyu Daudawa
Ko wacce shekara kananan yara da yawa ne suke mutuwa a sanadiyar cutar ciwon hakarari. Wannan cuta na cikin manyan cututtuka wadanda suke kashe yara yan kasa da shekara biyar a duk fadin duniya. Ranar wannan cutar ta duniya (11/12), masanan lafiya suka ce ko yake hanyoyin kare wannan ba su da yawa, amma akwai ingantattun hanyoyi kadan da zasu taimaka wajen kiyaye irin wannan mutuwar. Taken wannan shekara na ranar cutar ciwon hakarkari shi ne “Sabuwar al’ada ta kawar da cutar hakarkari ta kananan yara.”
Ciwon hakarkari wata cuta ce wadda ta shafi sashen huhu don haka iskar da mutum yake shaka, bata iya shiga cikin hanyar jini. Don haka ne ma shi numfashi yake zamar wa yaro da matukar wuya, wannan shi kai yaro har ga wani yanayi na kamuwa da ita cutar. Irin cutar hakarkarin da take kashewa ita ce wadda ta samu tawurin kwayar bakteriya, koda yake dai da akwai na irin kwayoyin cuta birus.
A duniya gaba daya, fiye da yara miliyan daya wadanda basu kai shekara biyar ba ne, suke mutuwa a ko wacce shekara. Ainihin yawan yaran da suke kamuwa da cutar sun ninka wadanda suke mutuwar, har wajen sau goma. Don haka ne yara wajen biliyan daya ne suke kamuwa da ciwon hakarkari, amma wakansu suna samun magungunan da suke bukata.
Babban masanin lafiya a asusun tallafawa yara, Dokta Mark Young, ya bayyana cewar za’a iya kiyaye yawancin mutuwar yara daga ciwon hakarkari. Yace akan matsayin kariya, idan yaro ya sami abinci mai nagarta wanda ya kunshi dukkan abubuwan da ake bukata na gina jikin yara, ya sha nono kawai, idan suka sami ruwan sha mai kyau da kuma tsabta da kuma kula dfa wanke hannuwa, – irin wadannan abubuwan suna kare yara daga kamuwa da cutar a mataki na farko. Hakanan kuma za’a iya yin amfani da allurar rigakafi mai inganci domin samun kariya daga kamuwa daga ita cutar.
Kuma idan yaro ya kamu da kwayar cutar ciwon hakarkari. Dr, Young ya bayyana cewar, ana iya maganinsa ne da wuri. Akwai magunguna masu inganci wadanda kuma suke da saukin sha ga yara kamar su amodicillin, wadanda suke aiki sosai a cikin yara. Wani abu mai wuya kuma shine gane cutar daga iyaye da wuri. Za su gane ta wurin ganin yaro mai tari ko wahalar uin numfashi. Iyali na bukatar gane wannan kamin daukar mataki na yin magani.
Kasashe da yawa suna inganta samun maganin ciwon hakarkari, da kuma wadansu cututtuka kamar su gudawa, wata cutar da ta ke yawan kashe kananan yara.
Haka nan kuma kungiyar GABI, dake taimako wajen kara allurar rigakafi, tace tana taimakon fiye da kasashe 50 domin samun allurar rigakafin cutar hakarkari ya zuwa 2015.